Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 46 of 125
Wajen mintina sha biyar tsakani, batare daya kalli Bilal ba yace
"Ka ga Layla?"
Kai Bilal din ya jinjina mishi, kullum sai yaga Layla, in ya fita kafin ya wuce aji saiya biya ya kirata ta sauko yaga ya ta kwana, ko tana da wata matsala sannan ya wuce, amanar ta Abbu ya bashi, babu yanda za'ayi ba zai dubata a duk rana ba.
"Ni ban ganta ba"
Cewar Rayyan da wani yanayi a muryar shi da yasa Bilal dagowa
"Ba tazo aji ba, bata jin dadine tun jiya da dare"
Mikewa tsaye Rayyan yayi zuciyar shi na wata irin dokawa
"Me yasa baka fada mun ba?"
Kallon shi Bilal yayi yanda ya hargitse lokaci daya kamar yace mishi wani babban abune ya samu Layla, shi yasan lokacin al'adarta ne, badan ta gaya mishi ba, sai dan ya kula da duk wata haka take fama. Wancen watan da ciwon da komai ta zo wajen Rayyan, yana ganin yanda har fuskarta Rayyan din ya taba ko zaiji zazzabi bayan ya tambayeta me ya sameta tace mishi bakomai. Bai fada mishi ba saboda yasan idan akan Layla ne Rayyan zai dauki abin ya saka a ran shi. Amman can kasan zuciyar shi yana jin kamar akwai wani dalili bayan nan, dalilin da bayaso yasan shi saboda yana da yakinin zai saka shi yaji kamar bai kyauta ba.
Jacket din shi da take can gefen gado Rayyan ya dauka yana sakawa akan kayan jikin shi da riga da wando ne, ya dauki wayar shi yana kama hanyar kofa
"Ina zaka je? Takwas da rabi fa"
Ko amsa bai samu ba, numfashi kawai ya iya saukewa yana bin Rayyan din da kallo harya fice daga dakin. Wani irin sauri yake ya karasa titi ya samu machine zuwa gate din makaranta, kawai so yake ya fara hango hostel din su Layla, bai daina gwada kiran lambarta ba, har lokacin bai samu ba, ya kusan mintina goma a tsaye bakin kofar hostel din kafin yayi nasarar samun wayarta
"Ki daga dan Allah"
Ya furta a hankali, ya kasa tsaida bugun zuciyar shi waje daya. Yankewa tayi, ya sake kira, sai gashi ta daga, muryata can kasa tace
"Hamma?"
Kamar tana son tabbatar da cewa shi dinne ya kirata
"Layla me ya sameki? Me yasa baki fadamun baki da lafiya ba? Ina wajen hostel dinku, ki sauko in ganki"
Ya karasa yana kokarin tuna ranar karshe da yayi magana cikin sauri kuma da yawa a lokaci daya irin haka.
"Ni ba zan iya fitowa ba"
Layla ta fadi daga dayan bangaren, tana saka zuciyar shi kara dokawa, shi fa sam bayason yaji bata da lafiya. Kuma gashi tana fada mishi ba zata iya fitowa ba, wacce irin rashin lafiya ce haka?
"Ki fito ba wasa nake ba, Allah ina jira"
Ya karasa yana kashe wayar, duk wata addu'a da tazo bakin shi ita yake karantawa, ya kafa idanuwan shi a kofar hostel din, har ya hango ta, dakyar take tafiya yana gani, yana kuma ji har cikin ran shi. Ta tsaya yafi sau biyar kafin ta iso inda yake tana tsugunnawa da alamar ciwon da take ji. Ta kwana biyu batayi ciwon mara irin na yau ba. Sunje clinic da Anisa an kuma bata magani, ta sha, sai taji kamar ya kara mata ciwon da take jine. Dakyar ta sauko yanzun ma
"Layla"
Rayyan ya kira yana tsugunnawa shima, idanuwanta da suka sauya kala zuwa wani launi da baisan ya zai fassara ba ta dago tana saukewa cikin nashi da dole ya rissina su saboda yanda ta kara ma bugun zuciyar shi gudu
"Ta shi muje asibiti..."
Ya furta a hankali, kai ta girgiza mishi
"Munje tun jiya, na sha magani"
Shima kan yake girgiza mata
"Baki da lafiya har yanzun"
Dakyar ta iya fadin
"Zai tafi nan da kwana hudu"
Da rashin fahimta yake kallon ta
"Ya akayi kika sani?"
Kwanciya kawai Layla take son yi saboda cikinta kamar ana shara a ciki. Kilan Allah ya taimaketa tayi bacci
"Hamma..."
Ta fadi a gajiye, ganin kallon da yake mata ya sata cewa
"Period ne..."
A hankali tana mayar da kanta ta saddar, ya dauki wasu dakika kafin ya fahimci ma'anar kalamanta. Tsintar kan shi yayi da mikewa yana kama hannunta ya taimaka mata ta mike, jin shi yayi da dumi fiye da kowanne lokaci, hakan ya saka shi taba fuskarta, zazzabine ruf a jikinta. Idan yace ya tafi gida hankalin shi ba zai taba kwanciya ba, bayan yasan babu wanda zai kula da ita idan yabarta nan hostel din
"Muje gida, in kinji sauki sai ki dawo"
Yanda yai maganar babu wajen gardama, kallon shi Layla takeyi, bama zata iya gardama ba a halin da take ciki, kwanciya kawai take son yi
"Zan dauko abu, kuma idan na koma ba zan iya sake saukowa ba Allah... Hamma kabarni anan, zuwa gobe ma zai fara sauki in shaa Allah"
Kai yake girgizawa tunda ta fara magana, sai yanzun ya kula duk tayi zuru-zuru. Idan dawowar ne gobe ta dawo, amman yau kam ba zai iya barinta ba, tunani zai mishi yawa
"Layla tare zamu tafi, karki mun gardama"
Yanda ya karasa maganar da wani irin sanyin murya da bata taba jiba yasa ta cewa
"Ka aramun wayarka in kira Anisa to"
Mika mata wayar yayi, sai da ta dan matsa sannan tayi kiran, kallonta yake duk da baya iya jin me take fadi harta gama ta dawo tana sake tsugunnawa, sun kai mintina goma da wani abu kafin Anisa ta sauko, da fara'a take kallon Rayyan
"Ina wuni..."
Yanayin yanda ta rage muryarta yasa Layla mikewa tsaye tana mata wani kallo
"Sannun ki"
Shine amsar da ta samu daga wajen Rayyan din, kyau yake yi mata tun ranar farko data fara ganin shi, amman tambayar duniya da tayiwa Layla akan shi sai ta hade rai
"Bana so Anisa, bana so Allah"
Takan fadi cike da kishin daya tabbatarwa da Anisa ba ciki daya Layla suka fito da Rayyan ba. Hakan dai bai hana yaci gaba da burgeta ba. Ledar da take hannun Anisa ta karba tana fadin
"Nagode..."
Kafin ta kalli Rayyan da alamar su tafi, ledar hannunta shikuma ya karba, yana kama hannun nata suka wuce cikin yanayin da ya burge Anisa matuqa. Ita daman saboda Anisa ne ta mike, saboda bataso ma Rayyan ya kalleta, ciwo bai hana wani irin kishi rufe ta ba. Yanda ta damqi hannun Rayyan yasan ciwo take ji, ba zaice ga yanda ciwon da take ji yake ba, amman ya san shi a karance. Shisa yanzun yaji har kasan ran shi, tsayawa yayi yana kallon yanda take runtsa idanuwanta
"Sannu..."
Ya furta yanajin kamar ya dauke mata ciwon da take ji, amman babu halin hakan, ganin tana shirin tsugunnawa yasa shi kama hannunta yana hanata. Juyawa yayi ya dan tsugunna, cikin tashin hankali Layla tace
"Hamma..."
Saboda taga yawancin mutane sun fara kallon su
"Zaki hau ko saina watsa miki mari?"
Rayyan ya furta, gara ya dauketa zuwa gate, watakila su sami abin hawa, tunda yaga tafiyar wahala takeyi mata. Bata taba hango kwatankwacin abinda yake faruwa yanzun ba. Rayyan ne, tana hango abubuwa da yawa da zasuyi tare, fiye da rabin abubuwan da tasan a tunaninta kawai zasu tsaya saboda shine, amman abinda yake shirin faruwa yanzun abune da bata taba hangowa ba ko a tunanin nata. Dogon wandone a jikinta da riga, da zata fito sai ta dauki hijabin da Mami ta dinka mata, dogone kusan har kasa, sallah take yi da shi. Yanzun ma shi hannunta ya fara tabawa bayan ya kirata, shisa ta saka.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.