Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 62 of 125
"Ina son ka Hamma na"
Wasu lokuttan Bilal kan amsa da
"Fada mun me kike so kawai Ruky"
Amman ko da tana son wani abu ne da gaske take nufin kalamanta. Yaune karo na farko da yaji an ambaci "So" kuma an hada da sunan shi a ciki, sai yaji ya natsar da wani abu a cikin kirjin shi, har haske yaji a tarin duhun da yake cikin kan shi
"Nagode... Nagode Layla"
Ya furta a hanyar shi, har yaje gida yana jin shi sama-sama. Bilal yayi bacci sanda ya karasa, shi sai da ya watsa ruwa tukunna ya fito robar ruwan da Bilal ya shigo da ita, ko fasawa baiyi ba, shi ya fasa ya sha rabi ya qulle ya ajiye, dauka yayi, kwayoyin shi ya dibo, ya ga alama idan ya zuba su a lemo ko ruwa sunfi saka hayaniyar da yake ji yin shiru. Ya jefa a ciki ya mayar yana kullewa. Da yake ba wani sake dandanon ruwan sukeyi ba, da wahala kaji su akan harshen ka, da robar a hannun shi ya karasa ya daga net ya shiga. Ajiyeta yayi a kasa ya gyara net din yana kwanciya. Babu abinda yake dawo mishi banda kalaman Layla, baima sha ba bacci mai nauyin gaske yana dauke shi, baccin daya manta rabon da ya same shi ta dadin rai.
Yayi wanka kafin su tafi masallaci daman, sanda suka dawo yawanci duk an tashi ana ta hada-hadar shirin tafiya makaranta, masu lakcar safe da masu shirin wani dan test da za'ayi, ko suna son shiga makaranta da wuri dan su kwafi assignment duk anata sauri. Bilal bai samu yayi wanka da wuri ba
"Da na sauke ka tasha sai in dawo"
Bilal din ya fadi ganin kamar yana batawa Rayyan din lokaci shi da yake da tafiya a ranar. Shikuma yafi son Bilal din ya shirya gabaki daya, idan ya sauke shi tasha daga can makaranta zai koma kai tsaye ba saiya wani dawo gida ya fara wani shirin ba, idan shine ba zai iya wannan ba. Wani irin sama-sama yake jin shi, ko dan hutun daya samu ne daga bacci, yana bude ido kalaman Layla ne suka dawo mishi suna saka zuciyar shi cigaba da dokawa, har zuwa yanzun kamar ana kara mata gudu, yanayine da bai taba jin irin shi ba, har sai da yai tunanin anya lafiya, kamar bugun da zuciyar shi takeyi ya wuce iya kalaman Layla, kamar tana son sanar da shi wani abu mai girma da yake shirin faruwa da shi. Lokaci zuwa lokaci yakan sauke ajiyar zuciya a hankali.
Aikam sanda Bilal din ya gama shiryawa har karfe bakwai da kusan kwata. Rigace fara ya saka sai wandon jeans bula, hutun da aka dawo na karshen nan ya tara kasumba irin ta Rayyan, kalar gyaran fuskar shi da askin yayi, ya rage sumar shi kasa sosai sosai shima. Ranar da ya shiga dakin Ayya kuwa sai da tace
"Oh Allah na Bilal"
Dariya yayi sosai
"Kema karkice kin dauka Hamma ne, yanzun Huda tace mun a waje, wai dana wuce ta dauka shine ya dawo"
Murmushi Ayya tayi, to a cikin gidan nasu ma mutane da yawa sun mishi magana, daga nesa za'a dauka Rayyan ne, saiya matso kusa yanayin haske da Rayyan ya fishi da tsayi kan banbanta su, sannan shi Bilal yana fara'a. Amman tabbas idan ba farin sani kayi musu ba, ka kuma jima baka ga daya daga cikin su ba, da wahala kagane. Baiji wani iri ba sai da suka hadu da Layla, yanda ta dafe kirji tana wani irin mayar da numfashi kafin dissapointment ya lullube fuskarta ya taba zuciyar shi
"Me yasa kayi irin askin Hamma?"
Ta bukata tana dorawa da
"Na dauka shine, wallahi na dauka shine"
Ko amsar shi bata jira ba ta wuce. Zai karya idan yace abin bai mishi ciwo ba, shisa ya yanke hukunci ba zai kara tara suma ba, irin yanda Rayyan din yakeyi zaici gaba, gashi a fuska damun shi yake shisa baya ajiyewa daman, yanzun kam harya fara sabawa, yana kuma kallon yanda Layla ta kan bishi da ido kamar yayi wani abu da bai kamata ba.
"Ka gama? Mu tafi?"
Cewar Bilal yana daukar wayar shi ya saka a aljihu. Mikewa Rayyan yayi yana daukar jakar shi suka fice, kofar kawai Bilal yaja bai damu daya kulle ba. Mota suka shiga, ko yar jakar shi Rayyan bai saka a baya ba, anan kan cinyar shi ya ajiyeta, ya juya motar suka fice daga layin.
Da mashin Layla ta hawo da ta ga motar su, amman napep ta samu, dan harta fara takowa da kafarta tunda skirt dinta ba zai hau mashin bama. Sai ga nepep ta samu, kuma kanta na kan wayar da take dannawa. Da mafarkin Rayyan ta kwana, mafarkai cikin yanayin da take fatan yin tsayin rai dan ta gani.
Ji tayi tana son ganin shi kafin ya tafi, tana sauka daga cikin napep din zuciyarta tai wata irin dokawa da sai da ta lumshe idanuwanta tana budewa. Dari biyu ce ta baiwa mai napep din tana furta
"Ka je kawai"
Ko godiyar da yake mata bata amsa ba, zuciyarta ke bugawa kamar zata fito waje. A irin yanayin daya kamata ace tayi addu'a, harshen ta ne yayi nauyi na gaske. Wata murya ke bata shawarar ta juya, amman ta kasa, kamar wadda akewa dole haka ta taka tana shiga cikin gidan. Makoshinta harya bushe saboda bugun da zuciyarta takeyi, dakin su Rayyan ta wuce kanta tsaye tana turawa ta shiga hadi da sake tura kyauren duk da bai rufe duka ba, dakin ya mata duhu da yake kwan a kashe yake, idan akwai wutar lantarki bata kula ba, balle tayi tunanin kunna kwan. Da fitilar wayarta ta haska, robar ruwa ta gani a kasa ta karasa ta dauka ta kwance, ta sha fiye da rabi tana dorawa kan tebir din Rayyan.
Gefen gadon ta zauna tana maida numfashi
"Hamma tafiya kayi"
Ta furta da wani yanayi a muryarta, watakila Rayyan din daya tafine yasa zuciyarta bugawa haka. Sosai ta so ganin shi, gashi tasan magana da sassafe wahala takeyi mishi fiye da kowanne lokaci, idan ta kirama ba dauka zaiyi ba shisa bata kwatanta ba. Haka kawai sai taji kanta ya fara mata nauyi, kamar wadda rashin lafiya ke son kamawa, takalmanta da ta shiga dasu cikin dakin sosai ta cire tana turawa gefe wajen tebir din. Kwanciya tayi sosai, a hankali ta zame dan mayafinta ta ajiye a gefenta. Wani irin yanayine daya hade mata da wanda ta shigo da shi da karatun wani labari a group ya taso mata da shi harya darsa mata son ko da ganin Rayyan ne.
Tunda take a duniya bata taba jinta a irin yanayin nan ba, kamar wadda take yawo a wata duniya ta daban, kamar tana cikin mafarkin da idanuwanta suke a bude haka take ji, shisa ta lumshe idanuwanta tana tunanin yanda akayi su Bilal din suka saka gado a maimakon katifa kawai a dakin nasu. Tana kuma tunanin yanda suka kyauta saboda taji dadin kwanciyar sosai. Kamar a cikin mafarki haka taji shigowar Bilal da harya kusa makaranta aka kira shi aka fada mishi Malamin ba zai sami damar zuwa ba, yaji dadin hakan saboda bashi da natsuwar daukar darasin ko da anyi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.