Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 73 of 125
Wayar Bilal ya tashi ya saka a caji dan yaganta a kashe, aikam cajin ne babu. Sai da yaga ta dauka sannan ya dawo ya zauna. Gwada lambar Layla yayi inda yai nasara ta shiga, har ta kusa yankewa sannan aka daga, wani irin numfashi ya sauke
"Layla..."
Ya kira daga lungun zuciyar shi, yanajin kamar yabi ta cikin wayar ya leqa inda take yaga lafiyar ta.
"Layla..."
Ya sake kira, muryarta can kasa ta amsa
"Hamma"
Lumshe idanuwan shi yayi yanajin yanda zuciyar shi ke rawa, nutsuwar da ta kwace mishi yake nema koya take, iya wadda zai samu karfin yi mata magana yaji inda ta shiga haka. Amman ya kasa samu
"Hamma ban da lafiya"
Layla ta fadi ta dayan bangaren, cikin wani mawuyacin yanayi da ya saka Rayyan din mikewa, sai dai ya kasa kara yin motsi saboda Bilal da yake gani a kwance shima, tunani yake ko akwai hanyar da zaibi ya raba kan shi gida biyu yabar daya anan asibitin dayan kuma yaje wajen Layla, dan sai yake jin kamar kuka take kokarin dannewa, zuciyar shi ciwo takeyi, ciwon daya kama ta nan take, dakyar ya iya cewa
"Kina ina? Me ya same ki? Waye a wajen ki?"
Ya kusa dakika biyar kafin ta amsa shi
"Bani da lafiya Hamma..."
Ta sake maimaitawa kamar bataji tambayoyin da yayi mata ba, wannan karin yaji sautin kukanta da ya kara mishi ciwon da zuciyar shi takeyi, dan baisan yanda zaiyi ba, baisan wa zai kira ya taimaka mishi ba. Ya bude baki zai sake yin magana ta riga shi da fadin
"Anisa...muna asibiti tun da safe. Hamma kana ina?"
Numfashi Rayyan ya sauke, a muryarta yake jin yanda take bukatar shi
"Ina asibiti, Bilal ba shi da lafiya. Me yasa zaku min haka Layla? Ya kuke so inyi? Ya zakuyi rashin lafiya lokaci daya?"
Ya karasa maganar yana bi da rokon yafiyar Allah dan yaji kamar yayi sabo, kamar yana kokarin dora ayar tambaya akan abinda basu da zabi a kai. Amman da gaske baisan yanda zaiyi ba
"Ki ba Anisa waya..."
Ya fadi muryar shi na fitowa da gajiyar da yake ji har cikin zuciyar shi
"Hello..."
Yaji muryar Anisa cikin kunnen shi
"Anisa ya jikin nata? Me suka ce yana damun ta?"
A nutse Anisa ta ce
"Zazzabi ne mai zafi, sai sunce tana bukatar samun hutu saboda jininta ya hau, sun mata allurar baccine tun da safe, sai yanzun ba dadewa ta tashi, gashi na hada mata shayi zata sha, likita yace za'a karayin wata allurar dan ta kara samun bacci... Da sauki ba kamar yanda muka zo ba"
Tunda ta fara magana yake saurarenta da dukkan nutsuwar shi, amman ya kasa gane yanda za ayi ace yarinya karama kamar Layla da yanzun ne zata cika shekara ashirin a duniya tana da hawan jini, ina ta samo shi? Tunanin me takeyi? Ko yace tunanin me sukeyi daga ita har Bilal da za ace suna da hawan jini haka. Lafiya kalau ya tafi yabar su duka, amman yanzun ya dawo lokaci daya duk sun kwanta. Gara Layla yaji muryarta, ta tashi, amman Bilal har yanzun ko motsi baiyi ba. A ina zasu sami hawan jini?
"Nagode Anisa.. Dan Allah ki zauna da ita kafin gobe, ina asibiti wajen Bilal, shima bashi da lafiya"
Ya karasa yana jin kirjin shi na zafi
"In shaa Allah...Allah ya basu lafiya"
Amsawa yayi da
"Amin"
Kafin ta mikawa Layla wayar
"Hamma..."
Ta kira shi tana saka shi jin kamar yayi fuka fuki zuwa inda take
"Kiyi hakuri Layla, Bilal ko motsi baiyi ba har yanzun... Ba zan iya barin shi ba, ba zan iya barin shi inzo wajen ki ba, dan Allah ki kula da kanki, ki sha tea din idan Anisa ta hada, ki kwanta ki huta kinji"
Muryarta da yake ji can kasa na kara taba shi, kamar bataji duk abinda ya fada ba, dan ta zabi amsa shine da
"Ina son ka, wallahi ina son ka da yawa. Dan Allah karka barni, Hamma ina son ka"
Ta karasa da kukan da ya saka shi fadin
"Ina zanje Layla?"
Dan tun daga dan yatsan kafar shi yake jin babu inda zashi yabarta. Baima san itace mutum na biyu mai matuqar muhimmanci a rayuwar shi ba sai yau, Bilal ne na farko, yau yasan matsayin Bilal ba zai taba haduwa dana kowa ba. Yana jin yanda zuciyar shi take zafi da rashin ganin Layla, amman awannin da suka wuce Bilal ya danneta a zuciyar shi da kan shi gabaki daya.
"Ina son ka"
Ta sake fadi, muryarta na isowa kunnen shi cike da firgici, baisan tsoron da take ji ba, amman ya taba zuciyar shi
"Ina son ki Layla, watakila yaune rana ta farko kuma ta karshe da zan fada miki, saboda nayi magana mai yawa yau, ina tayi har yanzun. Amman ina son ki, ko da bazan fada ba, zan nuna miki, ina nuna miki, ke ce bakya gani"
Ajiyar zuciyar da tayi na nutsar da wani abu a cikin kan shi
"Mafarki nakeyi ko Hamma? Daya daga cikin mafarkina ne yau ma"
Kai Rayyan ya girgiza mata, baisan soyayyarta na da yawa a tare da shi ba sai yanzun da yake jin kamar zata danne shi
"Zan sake fadi a karo na biyu, sai ina ganin ki, kafin lokacin ki kula mun da kanki"
Jin tayi shiru ya sa shi dorawa da
"Zan iya yarda dake? Zan iya yarda zaki kula mun da kanki?"
Shirun ta sakeyi sai sautin numfashin ta da yake tabbatar mishi da kuka take
"Kasheni kike son yi Layla? Idan banji zaki kula da kanki ba abin zai mun yawa, dan Allah kiyi mun magana"
Ya karasa yana kai hannu ya murza kirjin shi, inda zuciyar shi ke ciwo har kaikayi takeyi, amman murzawar baisa yaji kamar ya sosata ba
"Eh"
Ta fadi, kai ya jinjina ba sai ta tsawaita maganar ta ba
"Idan kin kasa bacci sai ki kirani muyi labari, ki sha tea din yanzun kinji ko?"
Bata amsa ba, amman yasan kai ta daga mishi, dakyar ya raba wayar da kunnen shi yana sauke ajiyar zuciya. Inda wayar Bilal take ya karasa ya kunna, yasan password din shi dan haka ya shigar, ya jira wayar ta gama kawowa, saboda Aisha ta fado mishi a rai. Yasan hankalinta ba'a kwance yake ba, kuma ba zata taba iya tako kafafuwanta gidan su ba, in dai yanda Bilal yake labarinta ne, yana da wannan tabbacin. Missed calls ya gani har guda sittin da bakwai, baibi ta kan su ba, lambar Aisha ya dubo, yana tura mata text
"Rayyan ne, muna asibiti da Bilal bashi da lafiya. Amman da sauki. Idan ya tashi zai kira ki"
Karantawa yayi yaga ko yayi sannan ya tura mata, kamar tana jira dan yana shiga tana dawo da amsa
"Subhanallah, Allah ya bashi lafiya. Dan Allah daya tashi ya kirani, da safe zan kira sai in zo in gan shi"
Har zai ajiye wayar saiya kula da tarin sakonnin da ta turo babu amsa, guda daya ya karanta
"Dan girman Allah Nawan ka rufa mun asiri, dan Allah be ok be fine, dan girman Allah"
Sai ta bashi tausayi, saboda yasan yanda firgicin nan yake
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.