Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 33 of 125
Harta fara kewar Bilal tun ba'a kwana ba, tasan shine kawai baya iya daukar awanni bai ganta ba, ko leka kaine sai yayi
"Ayya nace tun dazun banganki bane fa... Kina lafiya dai ko?"
Ba zai taba gane yanda kulawar shi take kara mata son shi ba.
"Subhanallah, Maimuna... Lafiya? Me ya faru?"
Ahmadi ya fadi yana karasawa cikin dakin sosai, kamar haka take jira ta sake fashewa da wani kukan
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ahmadi ya furta cikin bayanannen tashin hankali
"Duk ina yaran? Suna lafiya? Dan Allah kiyimun magana"
Dan harya fara zufa saboda tashin hankali, muryar Ayya na shakewa saboda kuka ta soma fadin
"Tunda kake, Ahmadi tunda Rayyan ya mallaki hankalin shi ka taba ganin ya tayani aiki? Ko da shara ce?"
Cike da mamaki Ahmadi yake kallonta, ya dauka sun gama yanke hukunci addu'a ita ce kawai abinda zasu dinga bin Rayyan din da ita, ba zasu kara bata ransu akan shi ba. Idan ma sun bata ran nasu zasu yafe mishi da sun huce ko Allah zai sanyaya zuciyar shi. Tunda fushin su zai kara jefa shi cikin wani yanayin ne, kuma idan bai manta ba yau Bilal yace zasu tafi makaranta, hatta kudin Rayyan din ya hada yaba Bilal, to me zaiyi wa Ayyar haka da take wannan kukan.
"Idan nace maka Rayyan na linkewa wasu can daban kayan da suke sakawa abin ba zai baka mamaki ba?"
Bata ma rufe bakinta ba take ganin wani sabon mamakin karara a fuskar Ahmadi, hannu takai tana share kwallarta, wasu sabbi na samun damar zubowa, kada kai tayi cikin kunar zuciya
"Yanzun zaka yarda dani ko? Yau zaka yarda matarka na bibiyata, zaka yarda yarana take so ta rabani da su. Ahmadi na kauda kai iya yanda zan iya... Da Allah nake rokon ka kayi mata magana ta kyalemun yaro, ta kyalemun yarona"
Ta karasa tana sakin wani gunjin kuka. Tabbas zancenta ya daure mishi kai matuqa. Yasan Rayyan, a cikin yaran shi yanzun babu wanda yake kula da takun shi kamar Rayyan. Idan da gaske Ayya takeyi yana linkewa su Mami kaya to tabbas zargin da takeyi na da tushe, duk da a kasan ranshi yasan Mami ba zata tabayin abinda zai cutar da wanin shi ba.
"Kiyi hakuri, zan mata magana. In shaa Allah babu abinda zai faru. Dan Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan..."
Ahmadi yake fadi, dan kukan nata ya kara daga mishi hankali, bai fita daga dakin ba har saida ya tabbatar ta daina kukan, da kan shi ya zubo mata abinci ya kawo mata ruwa. Sannan ya nufi bangaren Mami. Duba jikin Layla yayi ya shiga yi, ya samu tana bacci, daga nan ya wuce bangaren shi, bai yiwa Mami zancen ba sai bayan sunci abincin dare harma sun kwanta sannan yace
"Maryama me yake faruwa ne?"
Numfashi ta sauke
"Me kake so ince maka? Na dauka ta gaya maka abinda ya faru"
Kai ya jinjina
"Baya nufin bana son ji daga bakin ki"
Murmushin takaici mai sauti Mami tayi, kafin ta labarta mishi iya abinda tasan ya faru tana dorawa da
"Rayyan bai tana shigowa bangarena ba, idan ya taba lokacin yarinta na manta... Amman yau ya shigo saboda Layla... Ina tsoro, har raina ina tsoron wannan kaddarar ko wacce iri ce, saboda ina hango tarin tashin hankalin da yake cikinta"
Wannan karin Ahmadi ne ya sauke numfashi, gabaki daya abin ya saka jikin shi yayi sanyi, idan da gaske saboda Layla ne Rayyan din ya shigo ba Mami bace kawai a tsorace, shi kanshi zuciyar shi yaji tana rawa.
"Allah karka doramun kaddarar da bazan iya dauka ba, Allah ka dubeni da Rahmar ka ka saukakama yarana kaddarar su..."
Daren kusan Ahmadi, Mami da Ayya kanta kwana sukayi suna juyi. Ayya na jinjina aikin bokan Maryama da yanda ya zame mata dole ta kira Hajiya Dije su tattauna wannan al'amarin. Mami na tunani amanar Layla da take hannunta, tana kuma tsoron abinda zuciyarta take sanar da ita yana faruwa tsakanin Layla da Rayyan din da bata jin sun sani. Ahmadi kuwa gabaki daya lamarin ne yake sanyaya jikin shi, yaran nashine yake ganin kamar sunyi kankanta, kamar ma basu da hankalin hango kaddarar da take bibiyar su.
Rayyan ne kaddarar su
Rayyan ne suke tunanin zai zama tushen komai.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Nov 22, 2020
10
BAYAN SHEKARA UKU
Ita kadai tasan cikin kalar fargaba da tashin hankalin da take a shekarun nan. Yanda duk taso ta nisanta kanta da Hajiya Dije ko dan gudun suje inda za'a binciko mata abinda zai daga mata hankali sai ta kasa, Rayyan na bata tsoro, yanda yake manne da Layla duk idan ya dawo makaranta yana karya mata zuciya. Musamman yanzun da take ganin suna kara girma, yaranta na wani irin girma da har mamakin shi takeyi. Ita ce harta aurar da Khalifa da Zubaida. Kuma duk lokacin da zata sami Ahmadi da maganar takan ga gajiyawa a fuskar shi, kamar ya gaji da yanda ta kasa daukar ido ta saka akan Rayyan din da Layla kamar yanda yayi
"Ya kike so inyi? Ko akan dukan da yakeyi mata nayi magana tsini ne kawai bakina baiyi ba. Kinsan halin Rayyan, abinda ya ga dama shi yakeyi"
Ahmadin yace mata wani lokacin, ita ko dukan bata so, batason wani abu na hada danta da Layla. Batason ganin shi a bangaren Mami sam-sam. Rayyan din ya kara mata tsanar matar kamar zata hadiyi zuciya haka takeji duk idan taga giccinta. Yau da kanta ta shiga kitchen, har Rukayya na mata tsegumi
"Ayya saboda su Hamma zasu dawo shisa kika ce ke zakiyi girki..."
Dariya kawai tayi, wannan karin sun dade, watansu na hudu kenan rabon su da gida. Duk da ta wani fannin dadewar tayi mata dadi bana wasa ba. Hakan na nufin aikin da Malam Ma'azu kwano kamar yanda Hajiya Dije ta kira shi yaci. Daman tace a borno yayo karatun allo, a haka idan ka ganshi zaka raina shi, sai dai aiki yake kamar babu gobe. Tashin farko dubu goma Ayya ta ajiye mishi na bugun kasa, inda yace ta saka tafin hannunta kan wani rairayi da yake cikin falankin katako. Batayi musu ba ta saka, duk da tasan zancen gizo ba zai wuce na koki ba, ba nan bane wajen farko da sukaje da Hajiya Dije, kuma duk maganar shige dayace, Layla na rike da kurwar Rayyan, danma yana da dakakkiyar zuciya da sai abinda tace ne zaiyi.
Wannan ma suna shiga ta fara labarta mishi matsalarta akan Rayyan din, kafin yace yasan kasa zata nuna mishi komai, ta saka hannunta akan yashin, suna zaune suna kallon yanda yake rubutu yana sharewa yana sakeyin wani, kafin yayi numfashi mai nauyi yana dago kai ya kalli Ayya
"Yaron ki zai zama shahararren mai kudi, akwai nasarori da suke biye da shi. Shisa abokiyar zamanki ta kasa zaune da tsaye a kan shi. Saboda taje an duba mata yanda kaf gidan ba za'ayi mai arziqin shi ba. Yarinyar da kike magana da ita aka, idan baki tashi tsaye ba duk abinda zai samo a kansu zai kare, ke kanki ga katanga nan naga ana ginawa tsakanin ku"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.