Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 9 of 125

Mikewa kawai Ahmadi yayi

"Allah ya shiryeki ya yaye miki abinda ya shiga kanki. Saikin gyara lamurran ki wallahi"

Yake fadi yana ficewa daga dakin, bayason tsayawa yaji maganganunta balle harya biye mata suyi fadan da idan basuyi ba yaga alama batajin dadi. Haka ta kwana ko wadattacen bacci bata samu ba saboda kunar zuci. A haka kuma ta wuni tanajin ta sama-sama. Su Khalifa ma na dawowa gidan daga makaranta, kadasu tayi gidan Yaya Ayuba, har abinci saci acan dan bata samu karfin dora tukunya ba. Bata kara mamaki ba sai da Ahmadi ya shigo gidan ko la'asar batayi ba, tasan ba girkinta bane ba, shisa ta kara mamakin ganin ya fado dakin nata

"Maimuna..."

Ya kira da wani irin yanayi a muryar shi da yasa gabanta yin mummunar faduwa, tana kuma mikewa daga kishingidar da tayi, tunda tasa Rayyan ya kwanta yayi bacci itama take nan gefen shi. Ganin yanda yake kallonta yasa ta mikewa tsaye gabaki daya

"Lafiya? Me ya faru?"

Ta tambaya, so yake ya bude bakin shi ya gaya mata rasuwar dan uwan da yasan duk a cikinĀ  gidan su tafi shakuwa da shi, tsiran su ba wani mai yawa bane ba, duka shekaru biyu ya bata, kuma shi kadai ne take ji har kasan ranta duk a cikin yaran matar Baban nata da taki jinin ta bude idanuwanta tagani. Amman kowa yasan Maimuna yasan Audu, ko kasuwa yaje tsarabarta daban take da ta sauran mutanen gidan. Badume daya koma da zama bayan auren shi bai yanke zumuncin da yake tsakanin su ba, duk juma'ar duniya yana shigowa, kuma kowa yasan dan ita kadai yakanyi hakan, har gida yake zuwa ya dubata ya kai mata yan tsarabun da ya siyo.

Kusancin su mai girmane, shisa aka rasa mai zuwa ya fada mata gobarar da ta afka musu tun a daren jiya, gobarar da tai sanadin rayuwar Audu, matar shi da yaran shi biyu, cikin ikon Allah tana barin Bilal, jaririn da satin shi uku da haihuwa. Lamarin da ya girgiza kauyen Badume da kewayenta, domin Audu mutum ne mai karamci da sanin ya kamata, tun zaman shi babu wanda zaice ga ranar da yaga fuskar shi ba dauke da murmushi ba. Mutum ne da yake samun shaidar arziki ko da baya waje. Ahmadi aka samu har wajen aiki, suna ganin kamar zai fi mata sauki idan taji daga bakin shi, shikuma yana juyayin yanda ba zata taba manta a bakin shi taji wannan lamarin ba.

Da bakin shi ya fada mata zancen auren shi da Maryama, zancen da ya birkita mishi Maimunar shi ta yanda har yanzun bata dawo dai-dai ba, shi din mutum ne mai rauni, sam ba zai iya fada mata wannan zancen ba. Asalima yana ganinta yaji idanuwan shi sun ciko da kwalla, kwallar rashin Audu da ba ita kadai zataji shi ba, kwallar tausayin matar tashi da halin da yasan zata shiga. Bai iya komai ba sai hade dan sauran tazarar dake tsakanin su yana rikota jikin shi, zuwa lokacin harta fara kuka tun kafin ma tasan meya faru, jikinta ya gama bata koma menene ya faru ba abu bane me kyau.

Ko ina jikinta bari yakeyi

"Me ya faru? Ahmadi waya rasu? Ko Baba ne?"

Take tambaya tana dagowa daga jikin shi, kai ya girgiza mata yana kokarin danne kwallar dake son zubo mishi. Dakyar ya iya cewa

"Ki dauko mayafin ki..."

Batayi musu ba, dan ko ina jikinta bari yake, mayafin ta dauko tana rike dashi a hannunta ta fice daga dakin, tama manta da Rayyan da yake kwance a cikin dakin, takalman ma, daya nata, dayan na Ahmadi daya cire a bakin kofar ta saka. Saida ya fito daga dakin ya kalleta cike da tausayawa, nata takalmin ya tsugunna ya dauka yana tura mata, kula tayi ta zare nashi, ta saka nata. Sannan ya dago yana saka takalman a kafar shi. Maryama da ta fito goye da Haris ya kalla, da idanuwan shi yai mata nuni da bangaren Maimunar, ganin har tayi hanyar waje

"Rayyan yana bacci..."

Ya furta a hankali, itama da alama hankalinta a tashe yake

"Me yake faruwa?"

Dan lekawa yayi bai hango alamar Maimuna ba, hakan yasa shi fadin

"Audune Allah yayi mishi rasuwa, sunyi gobara jiya da dare, kamar da iyalin duka..."

Yanda Maryama ta dafe kirji tana sakin wani salati daya fito da kuka yasa Ahmadi wucewa yabi bayan Maimuna, ta yanki hanya kuwa sai sauri takeyi. Kunya ya cire ya ajiye gefe yana karasawa da sauri ya kama hannunta ya rike. Ko da suka isa gidan ma bai saketa ba saida ya karasa da ita har cikin gidan. Inda ta samu tashin hankalin da bata taba tsammani ba, tayi suma ranar yakai hudu tana farfadowa ana gaya mata labari kala daya. Tun da dare data samu natsuwar da zata iya mikewa taje ta karbi Bilal da sai kuka yake a hannun Yayar Audu din wato Talatu.

"Da kin barshi kin ji da kanki kawai Maimuna, ko tsayuwar kirki bakya iyawa..."

Talatu ta karasa cikin kuka. Wata mata da Maimuna ba zatace kowacce ba a lokacin ta karbe zancen da fadin

"Shima yaron zafin maraici ne yake taba shi, duk wanda suke shayarwa an gwada bashi mama fur yaki karba..."

Hannu kawai Maimuna ta saka tana daukar Bilal batare da tace musu komai ba ta fice daga dakin. Waje ta samu a tsakar gidan tana zama da yaron a hannunta, tanajin kamar duk duniya shi kadai ne alakar data rage mata a tsakaninta da Audu, kamar babu jinin shi a jikinta, kallon Bilal take, kaunar yaron na ratsa duk wani sassa na jikinta, tana tuna yanda ko ranar suna shi satika uku da suka wuce harda ita ake tsokanar Audu da yaran sak shiya biyo, duk ya kwace ma Jummai matar shi kamanni da yaran nasu, kunya irin ta Audu murmushi kawai yayi ya fice daga gidan.

Da tasan duk bankwana sukeyi da ta bishi sun dan zanta, da ta bishi ko yan mintina ta kara samu a tare da shi. Amman ina, ko ganin karshe da tayi mishi juma'ar data gabata basu wani dade ba, ruwa kawai yasha

"Nayi yamma Maimuna, idan Allah ya bamu aron rayuwa a gidanki zanci abincin rana juma'a mai zuwa"

Ta tuna kalaman shi, da suka saka hawaye masu zafi zubo mata. Tana kara rike Bilal a jikinta, wani irin zazzabine ya rufeta da tasan kaduwa da firgicine suka saukar mata da shi. Ance an gwada bashi mama yaki karba, ita kam gwadawa tayi yanzun, kamar Bilal yasan kalar kusancin da yake tsakanin ta da Audu ya kuwa karba, kafin wani lokaci yayi luf a jikinta. Aikam hakan ba karamin kara rikita kowa yayi a gidan ba, haka akaita koke-koke ana zantukan zumuncin da yake tsakanin Maimuna da Margayin. Ba ayi bakwai ba kuwa sai da ya zamana babu mai gwada karbar Bilal daga hannun Maimuna, masu tunanin cewa ma zasu rike shi basu furta zancen ba, dan ta nuna abune da ba zai yiwu ba.

Rayyan ma da Maryama ta biyota dashi, kamar yasan wani abu mai girma ya faru, baiko gwada zai sha Mama ba, larabar tazo musu da sauyi mai girma gabaki dayan su. Tayi rashi babba, ta kuma karbi amanar da take tunanin babu wanda ya cancanci a yarda da yai rikonta sai ita, ta karbi Bilal da Ahmadi ya nuna goyon bayan shi dari bisa dari a kai. Ko bai auri Maimuna ba, shi din mai rike jinin Audu ne, akwai wannan kusancin a tsakanin su. Shisa har yanzun da take rike da Bilal, rashin Audu yake kara tabata

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.