Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 48 of 125
"Bana son gulma, ki tashi daga saman kaina"
Turo baki tayi
"Ba aljanu ne da kai ba balle kace na tsaya a kanka zasu ta shi"
Ganin ya motsa yasa ta yin tsalle daya tana matsawa, dariya takeyi ganin yanda yake kallon ta, ta san da lafiyarta kalau saiya masgeta. Shisa ta rufa ma kanta asiri ta koma ta kwanta
"Meye kake zanawa Hamma?"
Ta tambaya, banza yayi ya kyaleta. Kawai dan ta dame shi ne yasa ta dinga mishi tambayoyi, towel din da yake kan kofa na Bilal ya janyo ya ajiye a gefen shi, surutunta har tsakiyar kwakwalwar shi yake ji
"Kaji Hamma..."
Layla ta fadi, ko kadan bata ga dago towel din ba sai da ya shauda mata shi
"Mayya ce ke?"
Towel din ta janye tana ajiyewa gefe, juya kwanciya tayi. Ya furta kalmar daya san zata bakanta mata rai hankalin shi ya kwanta. Zanen shi yaci gaba dayi har sai da yaji shirunta yayi mishi yawa, dubawa yayi yaga tana bacci. Net din da tunda Bilal ya daura musu shi suke fada a kai ya saki yana gyara mata sosai. Kuma kawai dan ya cakar da Bilal din ne yasa shi fadin
"Ni fa ba zan shiga net kamar kifi ba..."
Dan murmushi ne ya kwace mishi yanzun daya tuna mitar da Bilal yai tayi har washegari. Yakan yi tunanin ko bakin Bilal na mishi ciwo wani lokacin saboda mitar tsiya. A haka su Ayya suke cewa Bilal salihi, Bilal baya magana. Bayan har tsegumi yakeyi, shi kadai kuma yake yiwa, baisan ko Aisha naganin wannan bangaren na Bilal ba. Komawa yayi ya zauna, haka kawai wannan karin saiya kasa samun natsuwa, lokaci zuwa lokaci yake tsintar kan shi da kallon Layla da take bacci. Mikewa yayi ya karasa wajen kofa yana kama labulen dakin ya daga shi sama. Fankar dakin ya kurewa gudu duk da an dan fara alamar sanyi. Ya karasa ya bude net din Layla yana rufa mata bargo.
Duk da haka ya kasa samun sukuni, bai daina jin zufar rashin dalili ba duk kuwa da fankar dakin daya kure
"Me yake damuna ne haka?"
Ya furta a hankali. Kwayoyin shi ya tashi ya dauko ya sha yana mayar dasu ya adana. Amman har wajen awa biyu tsakani bai samu natsuwar da yake nema ba. Wata takardar ya dauka ya dora akan ta zanen da yakeyi yana rufa babban towel din daya siya domin hakan kawai ya dora kan shi akan tebir yana kwanciya. Kallon Layla yake da take bacci hankalinta a kwance, ba zai ce ga asalin abinda yake tunani ba, amman rabon da bacci ya dauke shi sha biyu saura ko da taimakon kwayoyi an dade, yau bacci mai nauyine ya dauke shi.
Karfe wajen biyu da rabi hankalin Bilal ya kasa kwanciya, duk yanda yaso yayi bacci saiya kasa, kalaman Abbu na danne shi. Yana jin kamar ya kamata ace ya fadawa Rayyan bai kamata su kwana daki daya da Layla ba, amman sai yayi shiru ya bar shi. Abin kuma ya dame shi sosai da sosai. Tashi yayi ya fita. Hango fitilar dakin su yayi a kunne, kwanakin nan da wuta suke kwana. Yana mamakin yanda labulen dakin yake a dage. Yasan Rayyan, ko shara Bilal din zaiyi ya daga labule sai yaita masifa, quda zai shigo musu daki.
Ya rasa hadin Rayyan da qudaje, ko kwara daya yaga gaccin shi a daki sai ya fitar dashi, ko ya kashe shi hankalin shi yake kwanciya. Balle kuma sauraye, ko jiya dariya Bilal yayi kamar zai shaqe jin Rayyan din na ma sauro masifa
"Dan ubanka idan sha zakayi ba zaka sha ka wuce ba, sai kana mun ihu a kunne"
Yanzun ma dariya ya tsinci kan shi dayi. Yana karasawa dakin. Bacci Rayyan yakeyi akan tebir, ko tunanin ciwon wuya bayayi. Cikin dakin sosai ya shiga, ya dauki maganin sauro na fesawa yana dan fesa musu saboda Rayyan din. Hannu ya saka cikin net din yana janyo dayan pillow din, ya mayar ya gyara. Dan bubbuga Rayyan din yayi daya bude idanuwan shi da suke cike da bacci
"Ka sa pillow hamma, wuyanka zaiyi ciwo"
Karbar pillow din Rayyan yayi yana ajiyewa ya mayar da kan shi ya dora, idanuwan shi ya lumshe saboda baccin da yake cikin su, sai yakejin kamar yayi kwanaki baiyi bacci ba. Wani irin numfashi Bilal ya sauke yana jinjina al'amarin su. Kafin ya fice, dan shima hamma yakeyi, idanuwan shi cike suke da bacci, hankalin shine ba'a kwance ba sai yanzun.
*
Zai iya cewa tunda safe yake tashi yayi wanka, wajen karfe hudu na safe wasu lokuttan. Yau ma da kan shi ya dora ruwa a kettle yaje ya sirka ya tashi Layla da ta dinga turo mishi baki kamar zatayi kuka. Duk da yasan babu mai fitowa sai da ya tsaya ta wajen hanyar bandakin har tayi wanka ta fito. Lokacin na shi ruwan yayi zafi, da duka kayan shi har wanda zai sake ya shiga bandakin. Yana fitowa ya tsoma wanda ya cire a wani bokitin yana zuwa ya wanke su. Alwala ya daura, saida ya kwankwasa dakin ganin Layla ta saki labulen, muryarta da alamar bacci ta amsa shi.
Hakan yasa shi ya shiga, ya sake komawa ta kudundune cikin bargo. Kai kawai Rayyan ya girgiza. Bayason jikin shi ya bushe shisa ya shafa mai, turaruka ya fesa, yana jin shi a dai-dai. Har wani shiru yake ji cikin kan shi babu wata hayaniya saboda baccin daya dan samu. Share dakin ya karayi yaji kamar ya taka kasa. Zuwa lokacin har anyi kiran sallar farko, masallaci ya fita, kafin a tashi sallah zai samu yayi raka'a biyun da yake sunna mai karfi kafin asuba. Ko da aka idar da sallar asuba ya dade a zaune cikin masallacin, ba lazumi yakeyi ba ko wani abu, kawai lokutta da dama yakan samu natsuwa a cikin masallaci.
Wani lokacin kuma kamar ana mintsinin shi haka yake so ya idar da sallah ya fita, shisa baya wasa da ranaku irin na yau. Sai da ya gaji da zaman sannan ya tashi ya fita. Dakin su ya koma, karfe takwas da rabi yake da darasi, yana nan zaune yana dan dudduba wasu abubuwan da bai fahimta ba har takwas saura, yana da biskit, da shayi ya hada yana cikin shane Hindu ta bude ido, tafi mintina biyar kafin tace
"Hamma...ina kwana"
Sai da ya ajiye kofin da yake hannun shi sannan ya amsa da
"Ya jikin ki?"
Taji sauki sosai, daman kwana biyun farko sunfi wahalar da ita
"Naji sauki..."
Ta furta a hankali, cigaba da shan shayin shi yayi harya gama
"Ina da lecture da safen nan"
Tashi zaune Layla tayi
"Nima haka... Karfe tara, sai mu wuce tare"
Kai Rayyan ya jinjina
"Zaki iya zuwa?"
Nade net din tayi tana sauko da kafafuwanta daga kan katifar
"Eh mana..."
Bai mata maganar taci wani abu ba, tunda yasan daga ita har Bilal basa iya cin abinci da safe haka. Shikam ko da asuba ne zaici, sai dai in bayajin yunwa. Iya abinda zai tafi dashi na ranar ya harhada ya dauko jakar shi yana kara shiryata ya saka a ciki. Ta riga da ta sake kayanta sanda ta fito, ta mayar da wancen cikin ledar da tazo da ita. Mayafin da ta ajiye akan gado ta janyo, doguwar rigace ta atamfa, mikewa Layla tayi tana duba ledar ta dauko dankwalin rigar ta ajiye. Ta karasa ta dauki ledar ruwa, fuskarta da bakinta take son daurayewa. Anan bakin kofa ta tsaya, tana jin idanuwan wani da batasan waye ba a cikin gidan yana kallonta, ko daga kai batayi ba harta karasa ta koma dakin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.