Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 53 of 125

Watakila taji tsoro ne batayi amfani da maganij ba, duk kudin da ta kashe a kai. Tunda kwanaki ma da taje gidan ta ga Haris din ya shigo har bangaren Ayya yana gaishe da ita, harma da yar hira sukayi yana shiga Kitchen ya zuba tuwo da tayi, ba zata manta cewa Ayya

"Haris dinne nan?"

Saboda ita bata ga alamar lalacewa a tare da shi ko daya ba, mikewa Ayya tayi yana amsa ta da

"Shine, bari in dauko miki leshin da nake magana"

Murmushi kawai Hajiya Dije tayi, tasan dan karta tayar mata da zancen Haris ne. Wannan kuma duk matsalar Ayya dinne a ganinta. Yanzun dai a sama ta sami saniyar tatse. Danma kudin a wajen bin 'yan tsubbu suke tafiya itama. Duk kan mijinta da take tunanin an janye hankalin shi daga kaine. Ayya kuwa ranar wata zuciya aka kawo mata an yayyanka turbude da magani akace ta wanke ta zuba ruwan a bakin kofar dakin su Rayyan, sai ta ajiye zuciyar tayi mishi girki da ita duk idan yazo, daga shi har Bilal din a tabbata sun ci, to zai zama kamar ta kwato musu tasu zuciyar ce da Layla ta lashe.

Karba Ayya tayi, da fari maganin yayi mata kama da ararrabi saboda kalar shi, kamar ta dandana da ta wanke, sai tayi saurin kauda tunanin daga ranta. Duk irin wannan was-wasin kan bata aiki wani lokacin. Yanda akace tayi haka tayi, zuciyar ta kulle a leda ta saka a fridge, take ta ajiyarta tunda su Rayyan din sunki zuwa, sai a satin da tayi waya da Bilal ya tsayar mata ranar zuwan nasu. Cous-cous ta dafa musu da ya sha hanta da zuciyar da kuma kayan hadi. Aikam ranar tas suka cinye shi da Bilal, danma Bilal ya tsaya taince albasar da take ciki.

Duk da haka taki samun natsuwa, rabin rayuwar ta tun zuwan su jikin window take yinta, ko baccin rana ta daina samu tana runtsawa, dan ko ta kwanta sai taji kamar an gitta, da sauri take dirkowa daga kujera ta leqa ta ga ko Layla ce. Ga Rayyan din da ta dan fara gane kan shi kafin ya tafi ya kara hargitse mata. Ko sau daya bai tako dakin ba, itama da taje ta same su a bangaren su kan shi a kasa suka gaisa, surutun duniya da tayi baice mata uffan ba. Haka ta fita cikin kunar rai, Bilal ne ma yabi bayanta yana lallashinta

"Ayya kinsan halin shi ai, kuma baya ma jin dadi kwana biyu tunda muka dawo, nima shiru-shirun ake tayi mun"

Ya karashe da murmushi, ranta na suya tace

"Dan uban shi dan bayajin dadi sai inta magana yanaji na yaki dagowa balle inyi tunanin zai tanka? Har yaushe zai san ina da muhimmanci mai girma a rayuwar shi Bilal? Ace yafi karfin ya taso yazo ya gaishe dani ko da sau dayane a rana? Shikenan..."

Ta karashe muryarta na karyewa cikin yanayin da yasa Bilal fadin

"Dan Allah kiyi hakuri....zai gyara ai..."

Kai ta jinjina, dakyar ta iya cewa

"Hmm...Allah ya shirya"

Nan Bilal ya zauna yana ta mata labari har saida ya ga ta warware tukunna ya tafi. Shisa tayi kewar shi matuqa a watannin nan da baizo ba. Duk wata hanya da zaibi ya rage mata damuwa ya sani. Yafi kowa fahimtarta, akwai halayenta da ko Abbu baisan yanda zaiyi da su ba amman Bilal ya sani. Zata iya cewa idan da na zama amini to Bilal ne amininta, duk wata damuwarta ko ta waya idan ta kira shi ta kai karar Abbu da Mami sai ya lallaba ya bata hakuri, saiya nuna mata yanda yake goyon bayanta, cikin dabarar shi. Neman Malamanta ne kawai abu daya da Bilal bai sani ba, abu daya da ba zata iya rabawa da shi ba saboda bata so yayi mata wani kallo na daban.

Mami kuwa tun da suka dawo sai ta tsinci kanta da bin Layla da ido a duk al'amurranta, tun kafin tafiyar su wayewar da yarinyar tayi ya wuce shekarunta, amman yanzun sai take ganin wata irin wayewa ta ban mamaki ta kara shigarta, kamar idanuwanta sun kara budewa. Bakinta bai daina bin Layla da addu'a ba ko a zaune take. Musamman da take makaranta, sai taita yawan tsintar kanta da faduwar gaba na rashin dalili, kuma tasan duk akan damuwar Layla ne da ta saka a ranta. Sai ta kirata sau nawa a rana, a duk karshen wayar tana jaddada mata

"Dan Allah ki kula Layla, ke mace ce. Kiyi kokarin kare martabar ki a dukkan al'lamurran ki. Ba lallai sai a shigar ki ba, martabar ki na tare da abinda harshen ki zai furta, tana kuma tare da mu'amallar ki da mutane, musamman maza... Ki kula, ki rufamun asiri ki rufawa kanki asiri"

Ta kan amsa da

"In shaa Allah"

Wani lokacin kuma ta kanyi shirun da yake karawa Mami damuwa, sai taji kamar ko Layla nayin wani abu da bai kamata ba shisa tayi shiru tana jinjina kalamanta na ranar, a lokutta irin wannan da ta sauke wayar take fadin

"Allah ka taimakeni, Allah ka bani ikon sauke amanar da na dauka"

Amman zuciyarta na rawa sosai. Jiya cikin dare ta farka, sabonta ne duk idan ta farka taji ba kishi bane ko wani matsi na fitsari da makamancin shi ya tasheta to fa sai tayi kokarin yin sallah ko da raka'a biyu ce tayi addu'a. Ta kanji kamar akwai dalilin da yasa Allah ya dawo mata da ruhinta a dai-dai lokacin. Watakila wani abune zai sameta, ko ahalinta shisa Allah ya bata damar sake kaddarar ta hanyar addu'a. Jiyan harta ninke dardumarta sai taji son ta duba Layla, wajen karfe biyu da rabi, tana kama kofarta da take kullewa a kwanakin nan sai tayi nasarar jinta a bude, turawa tayi taga Layla ta kife wayarta da saurin gaske.

Kwan fitilar dakin ta kunna, haske na gaurayewa da yake akwai wutar lantarki

"Layla?"

Ta kira tana karewa Layla da take zare mata idanuwanta da ta ga sun sake launi da alamar baccin da yake cikin su da kuma wani abu daban da ba zata ce ko menene ba

"Karfe nawa yanzun? Baki yi sallah ba bakiyi komai ba dan ubanki kin zauna danna waya?"

Mami ta karashe a fadace, wayar nan tana ci mata tuwo a kwarya, daman da rana sanda zasu ci abinci duk sai da ta amshe a hannunta da na Jabir tukunna suka maida hankali suna cinye abinci suka sake daukar wayoyin. Yau dai a tsorace Layla take kallonta, ko kadan bata san cewa bata kulle dakin ba. Kamar sanda ta dauko ruwane wajen karfe sha biyu, hankalinta nakan labarin da take karantawa, shaf ta manta da ta kulle dakin. Hankalinta a tashe yake da yanayin labarin, ta fita daga group din. Idan an aiko wani mai zafine sai Nanaa ta mata copy ta tura mata.

Makoshinta da kamar an zuba kasa saboda yanda take fitar da numfashi yasa ta tashi ta dauko ruwan, ashe bata kulle kofa ba, har zazzabi take ji na rashin dalili kafin Mami ta shigo mata daki babu tsammani, zuciyarta har cikin bakinta taji saboda yanda ta tsorata, idan Mami taga abinda take karantawa kashinta ya bushe, ita da waya har abada, a jikinta take jin haka

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.