Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 27 of 125

Gidan nasu daki shidda ne, guda daya Abbu ya biya mishi shi kadai, sanin halin shi. Banda sallama babu wani abu da yake hada shi da wani a cikin gidan, sau dayane da akace wani Emmanuel bashi da lafiya za'aje duba shi ya bisu. Acan ya barosu saboda baisan ya zai zauna ayi hirar da suke tayi da shi ba. Sunayen su ma bai sani ba, Emmanuel din saida yaje asibitin ya gane shi. Lokacin da yaje ya sami da yawansu a gidan, suke fada mishi yanda suke tsara shara da wankin bandaki, idan wannan yayi wannan ma sai yayi.

Sai dai shi baya jira, shiga biyar idan zaiyi a rana, komin wankin da akayiwa bandakin saiya kara wankewa, ya sha jin suna gulmar shi

"Dan sarkin masu tsaftar Rufasi da kewaye"

Daya cikin su ya taba gwada tsokanar shi

"Gaye sarkin tsafta..."

Kallon "Yaushe muka fara wasan nan" Rayyan yayi mishi ya wuce yana barin shi a wajen batare daya samu damar karashe zancen ba, babu wanda ya sake gwada tsokanar shi a cikin su kaf, koya zakayi mishi fara'a fuskar shi bata canzawa, kullum fuskar shi a hade take, ga cikar gashin girar da yake da ita sai yasa ake kara ganin abinda turawa suke kira da "Frown" bayyane a fuskar tashi. Ko a aji an shaida Rayyan, yakan amsa tambaya idan yana cikin yanayin ko kuma wata rana yayiwa Malami. Amman idan ba kai ka fara mishi magana ba, ko kusa da shi ka zauna zaiyi tamkar bai ganka ba.

Na shi miskilancin daban ne, babu wanda zaice ya taba ganin shi yana yawo da wani, shi kadai yake al'amuran shi a cikin makaranta, duk kuwa yanda wasu a aji suke son kulla abota dashi, daga gaisuwa sai kaci sa'a zaka sake fito da magana daga bakin shi. Ko fita zaiyi daga gida wani lokacin a ranshi yake furta

"Allah yasa kar wanda yai mun magana yau. Bansan me yasa mutane basa gajiya da magana ba"

Shisa yau ma yana gama shirin shi tsaf, ya saka wandon jeans, takalmin sneakers ne a kafar shi, sai riga baka da ta amshi farar fatar shi, sai kamshin yakeyi saboda ya yarda da turare, kuma daya fito wanka sai da ya busa sigarin shi. Bilal kance yana warin hayakinta duk idan ya sha, shisa yanzun yafi da ta'ammali da turare, kawai ya tsinci kan shi da kara shinshina jikin shi bayan ya gama shirin, jakar shi daya shirya kaya a ciki ya dauka yana fitowa, mukulli yasa ya kulle dakin, ya saka shi a aljihu kenan kamar daga sama yaji ance

"Rayyan ba dai tafiya ba da sassafen nan, kana kewar gida ne da yawa haka?"

Juyawa yayi yaga wanne mai karfin halinne, ya tsani magana da mutane, yafi tsanar magana da mutanen da baisani ba, idan kana so ka bata mishi rai kayi mishi magana da sassafe haka

"Cikin abubuwan da aka haramta ya kamata ace akwai magana da sassafe"

Ya kan fadima kan shi, kallon gayen yayi, Saminu yaji ana kiran shi, ya rike sunan ne saboda surutun shi, surutun da yasa gayen sam bai mishi ba. Idan yana daki a kwance da daddare muryar shi tafi ta kowa tashi. Lokutta da dama yasha lumshe idanuwan shi ya hasaso ya shiga dakin su Saminu da yake kusa da nashi ya kwada mishi mari.

"Kamar ana korar ka?"

Saminu ya sake fadi yana washe ma Rayyan din hakora kamar ya san shi. Hannu Rayyan ya mika mishi sunayin sallama, yanajin wani yarr a jikin shi saboda hannun Saminun da yake da lema alamun ya taba ruwa, kilan ma baki ya kuskure ya sakada yatsu a ciki yana wankowa. Yatsina fuska Rayyan yayi cike da kyama, yana da bala'in tsantsani, shisa ko a cikin makarantar bako ina yake cin abinci ba, yafi son soyayye kuma, ko ya siyi lemo da biskit yafi mishi natsuwa, akan ya siyi abu yaci zuciyar shi taita tashi a banza da wofi.

Yanzun ma raba Saminu yayi yana ficewa daga gidan. Nufin shi ya fita harya samu acaba da zai kaishi tasha, sai ya tsinci kan shi da takawa yana cigaba da tafiya, kafin wani lokaci ya gan shi kofar gidan su Haris, bayason yaji kamar bai kyauta ba, duk da yanda kasan cuta haka yake avoiding din Haris a cikin makaranta, yana iya hango shi daga nesa ya sake hanya. Duk da Haris din yaki fushi, har aji yakan same shi idan ya kwana biyu bai ganshi ba, wata rana kuma har gidan yakan je da yar kular shi ya kai mishi abinci

"Ni na dafa, duk me zan kawo maka ni na dafa..."

Haris din ya fadi ranar farko daya kawo mishi abinci, baici ba saida ya tafi, ya kuma ji dadin wake da shinkafar da miyar kifi. Dan ya kwana biyu baici abinci ba a lokacin, to kusan saiya zamana idan yaci abinci ba soyayyen abu ba, to Haris ne ya kawo mishi, ko nashi rishon mai amfani da kalanzir dana wuta bai taba kunnawa ba. Ba ruwan zafi yake wanka dashi ba komin sanyin da akeyi kuwa, ba kuma girki ya iya ba balle ya dafa. Jiyan Haris ya same shi har aji yayi mishi fatan nasara da cewa

"Naga yau zaku gama jarabawa... Nikam sai ranar laraba in shaa Allah"

Baisan ya akayi bakin shi yayi nauyin cewa Haris zai tafi gida ba yau, daya huta yanzun. Gashi tsaye a kofar gidan yana tunanin shiga, bama shigar bace ke mishi wahala, abinda zai fada din ne tashin hankalin shi. Yana nan tsaye yayi sa'a Haris ya fito, da mamaki yake kallon Rayyan, dan bai tsammace shi ba, bayan sun gaisa ne yake fadin

"Sai kayi tsaye a bakin kofa? Da ban fito ba fa? Ka shigo"

Kai Rayyan ya girgiza

"Zan tafi gida ne, shine na biyo"

Murmushi Haris yayi, yaji dadin biyowar kuwa. Dan mutane kanyi mamaki idan yace musu Rayyan din kanin shine, duk da akwai yanayi na kamanni da zai nuna cewa akwai alaka ta jini a tsakanin su, amman halayyarsu tayi hannun riga

"Ka kyauta daka biyo, nagode da zumunci. Allah ya tsare hanya. Nima in shaa Allah ranar laraba dana fito daga exam zan taho gida"

Kai kawai Rayyan din ya daga mishi yana juyawa. Jakar shi ya sakewa kafada saboda ta daman ta gaji, anan ya rataya tun fitowar shi. Daga gidan su Haris din kai tsaye titi ya fita yana samun mashin zuwa tasha. Kamar ya runtsa idanuwan shi ya bude su ya ganshi a gida haka yake ji, idan ba kwakwalwar shi ce take mishi karya ba, kamar zumudin zuwa gida yaji yanayi.

*

Sam tunda Rayyan ya dawo hankalin ta yaki kwanciya. Baccin kirki ma bata samu tayi, gashi hutun yayi mata tsayi, daya tafi makaranta sai taji hankalinta ya kwanta sosai. Ko babu wani abu Rayyan din yayi nisa da gidan, yayi nisa da Mami da Layla. BikinĀ  Zubaida ma da za'ayi nan da wata biyu bai tsaya mata a rai kamar yanda take so taga Rayyan ya koma makaranta ba. Gashi yanzun yafi da yin nesa da ita, jiya badon Rukayya ba sai girkin da ta dora ya babbake, yanata qauri, sam a hanci ma bataji ba, tazo jikin window din dakin ta daga ciki ta labe tana leke.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.