Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 118 of 125
"Na san banda wani abu da zan baka Hamma, ba haka na hango yau ta kasance mana ba..."
Layla ta ke fadi wasu hawaye masu zafi na zubo mata. Kai Rayyan yake girgiza mata, sam bayason inda tunaninta yake so ya dauketa
"Bana so, bana son wannan shirmen tunanin naki. Kin zo mun dake, kin zo mun da Nur, kin bani duk abinda nake so harda abinda banyi zato ba, dan Allah ki bari, karki kara mun damuwa da tunanin nan naki... Raina a bace yake, amman bake bace"
Ya karasa maganar yana matsawa sosai ya sumbaci goshin ta, yana sake sumbatar kuncinta kafin ya riko ta jikin shi yana sauke wani irin numfashi, ya manta yanda kusanci da ita haka yake samar mishi natsuwa, ya manta yanda jinta a jikin shi kawai yake kwantar da duk wata murya da take neman daga mishi hankali, sosai ya kara riketa a jikin shi yana sumbatar duk wani waje da labban shi zasu iya sauka kafin ya sake riketa kamar zai koma jikinta
"Nagode Hamma..."
Layla tace tana dorawa da
"Nagode da ka zamar dani matar ka"
Dariya yayi mai sauti yana sake riketa
"Nagode da kika zama matata, nagode Layla. Ba zan miki alkawarin baki farin ciki ko da yaushe ba, amman In shaa Allah zanyi kokarin ganin kinyi farin ciki koyaya ne a duk ranar da zan samu aronta tare dake, Nagode... Nagode"
Yana jin amsarta ta yanda ta kara shigewa a jikin shi, Ayya tace itace mafarin komai, tace laifin duka nata ne, baisan ko Layla da take jikin shi bane ta sauya tunanin shi, bai san ko dan Ayya din daga jikinta ya fita ba, amman ya kasa dora duka laifin a kanta, ya ga fuskarta, ya ga idanuwanta, ba tun yanzun yasan duka rayuwarta ta ta'allaqa ne wajen ganin ta kare su daga duk wani abu da zata iya ba. Idan da ta hango abinda tayi zai iya tabasu ba zatayi ba, yana ganinta ita da Haris, tana kaunar shi kamar daga jikinta ya fito. Kuskure ne tayi, kowa baifi karfin yayi kuskuren ba, ko da akwai son kai a cikin shi, baice ran shi bai sosu ba, baice ba za'a dauki lokaci ba kafin ya daina jin ciwon abin. Amman zasu kai wajen, kamar yanda shi da Layla suka kawo yau.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Jan 30, 2021
33
Fitowa tayi daga wanka, idanuwan ta kan Nur suka fara sauka kafin ta saki salati
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Idanuwan shi Rayyan ya daga ya kalleta a kasalance, kamar bai san dalilin yin salatin nata ba, yana kallo ta karaso ta kama Nur tana karewa gashinta da yake tsaye birci-birci duk ya cakude waje daya kallo wani malolon bakin ciki ya taso ya tokare mata wuya. Ita kadai tasan wahalar da tasha daren jiya tayi mata kitson, da kuka da komai, har dukanta sai da tayi, saboda Rayyan din ya kwana asibiti wajen aiki, Aminu Kano bangaren masu matsalar kwakwalwa. Ta san indai ya dawo ba za'ayi ba tunda Nur ba son kitso takeyi ba, ko kibiya ta gani a hannun Layla sai ta saka kuka.
"Kwance mata kayi?"
Ta tambaya, gira Rayyan ya daga
"Me yasa zakiyi mata kitso? Kin matse mata kai dakyar take motsa wuyanta, har gefen kan ya fara yin alamar kurji"
Sakin Nur tayi kawai, idan tayi magana tsaf hawayen takaici zasu biyo baya. A shekaru uku da aurenta da Rayyan ba zata ce bata cikin kwanciyar hankali ba. Amman tunanin da tayi na cewar auren Rayyan shine zai gyara mata komai, idan tana tare da shi babu wani abu da zai dameta ne ya sha bamban. Mutane ne suka nuna mata damuwar ta babu inda zata je, kamar yanda suka koya mata rayuwa da damuwar a kasan zuciyar ta. Ko biki akeyi ko suna idanuwan mutane akan Nur suke fara sauka, Nur suke fara gani, kamar yanzun rayuwar ta gabaki daya ta tattara ne akan yarinyar
"Ita ce wannan ko? Allah sarki"
Sune kalaman da suka fi tsaya mata a kirji suna sakata jin wani irin ciwo na ban mamaki. Ba manta yanda aka sami Nur tayi ba, amman na rana daya tana so ta rufe idanuwan ta, ta bude su ta kalli yarta a matsayin ya, ta kalleta batare da taga tabon da tayi mata ba, tabon da shi kowa yake fara dubawa. Ba son kai zatayi ba, amman Nur tana da kyau, sosai tana da kyau saboda tana kama da Bilal, kamannin da yasa in ba sanin su kayi ba sam ba zaka gane ba daga jikin Rayyan ta fito ba, gashi tana da hasken fata kamar na Rayyan din. Sai dai kyawunta ya kasa dishe munin tabon da yake tare da ita.
Shekarar su daya da aure, Rayyan ya saka ta sake yin jamb ta nemi gurbin karatu a BUK.
"Kina da buri kafin faruwar komai, abubuwa da yawa sun canza miki, bana son ya zamana harda wannan...ki koma makaranta Layla, kiyi karatu, ki fita da sakamakon da kike burin fita, ki nemi aikin da kike fatan samu"
Shine kalaman shi, kalaman da suka bude mata zuciyarta suna dawo mata da burin ta sabo. Ko ba komai makarantar ta rage mata damuwa, yanzun tana shekara ta biyu, ta sha wahala a farkon zango na biyun a shekarar saboda laulayin cikin da yake jikinta, ga kula da Nur, tunda Rayyan yaki yarda a sakata makaranta sai a sabon zangon da za'a shiga, dan ma bakomai take yiwa yarinyar ba saboda Rayyan in dai yana gida fiye da rabi da kwata na lokacin shi yana kan Nur dinne, in ba bacci tayi ba ita Layla bata samun kan shi sam. Duk da haka ta sha wahala, tunda in dai aikin safe yakeyi sai ta dafa mishi abinda zai tafi da shi. Wata ukku na farkon cikin ta wahala sosai, yanzun ne ma ta dan samu saukin laulayin.
Yau da ya kama asabar zasu je gida ne gabaki dayan su. Basu ma tashi da wuri ba, indomie da kwai ta dafa ma Rayyan din da Nur, ita tana da sauran doyar da sukaci da daddare, ita tayi warming taci. Yanzun ma mai ta shafa ta dauki kayanta tana ficewa daga dakin ta kyale su. Sanda ta dawo ta gama shiryawa tsaf
"Ki gyara mata kan, ina takalman ta?"
Ya bukata, inda suke Layla bata kalla ba
"Magana fa nake yi"
Rayyan ya sake fadi da alamar dariya a muryar shi, sarai yasan ta kule, ranta a bace yake. Babu yanda zatayi da shine kawai tunda ya fita rikici, ya kuma fita iya fada. Baisan sau nawa zai gaya mata ta daina ma Nur kitso ba, duka yarinyar yaushe kanta yayi kwarin da za'a kama shi ana mai kitso, ko gashin kirki ma babu, keyar ba komai har yanzun. Kawai salon a saka mata ciwon kai. Ya ce ta dinga shafa mai sai tayi mata kalba ta saka mata hula, kan da za'a rufe in ba rigima ba meye nayi mishi kitso. Sanin Layla ba kula su zatayi ba yasa ya mike yana daukar Nur din, da kan shi ya karasa in da kayanta suke ya samo wata farar hula mai duwatsu a jiki ya saka mata, takalman ma shi ya dauko mata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.