Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 34 of 125

Wani irin numfashi Ayya taja, tana duban Hajiya Dije, zuciyarta na wata irin dokawa

"Yaushe Maryama zata kyaleni in huta?"

Murmushin "Na fada miki ai" Hajiya Dije tayi mata

"Da nace miki ki dinga nemar wa yaranki ko da tsarine ca kikayi kamar Maryama ba zata iya cutar da su ba. Kin daiji da kunnuwan ki yanzun ai"

Kai Ayya ta jinjina mata, taji kam, ba waje daya ba biyu ba, kuma ta gasgata tunda zuwan karshe da Rayyan din yayi, saboda ta mishi magana akan Layla yasa shi daina shiga bangaren ta gabaki daya har suka koma. Sosai abin ya bata tsoro, ashe katanga ake mata da dan data tsugunna ta haifa, dan daya fito daga cikinta. Rashin imani irin na Maryama ba zai misaltu ba. Aiki Malam Muazu yace za ayi sosai akan Rayyan din

"Gaskiya kudin ki zaiyi yawa, saboda za'a yanka raguna baki da fari guda daya, da zuciyar su za'ayi aikin, sai an hada guda biyu za'a musanya su da ta danki da take rike a wajen su... Aikine babba, zan kuma baki garin maganin da nake so ki tabbata ko yayane shi yaron yaci dan ya karya katangar da take tsakanin ku"

Hakan kuwa akayi, kudaden duk daya bukata ta bashi su. Daman yace zata ga canji, ba karamin dadi take ji ba ganin yanda Rayyan din ya zauna a makaranta har tsayin wata hudu,mutumin da baya iya hada satika hudu batare da yazo Kano kona kwana daya ba. Shisa take shirya girkin nan da kanta. Duka zata hade abincin ta barbade, har Bilal ma yaci dan shima yana bukatar duk wata kariya da zata ba Rayyan. Dan ma shi tana kula da yanda yake janye jikin shi daga bangaren Maryama, ya rage shiga kamar da, hakan ba karamin dadi yake mata ba.

Gabaki daya cikin nishadi take a duka ranar. Saima da taji sallamar Bilal, da murmushi dauke a fuskar shi. Su Rukayya kance basa bambance muryar Bilal da ta Rayyan musamman yanzun da suka zama Samari, sannan idan a fisge ka kalle su zaka iya dauka Bilal ne, sai ya shigo sosai zaka ga Rayyan ne. Kamannin su har Abbu suke ba mamaki, yana kara jinjina karfin dangantaka ta jini, duk da mutane da yawa kan iya yin kamanceceniya batare da alaka ta komai ta hadasu ba.

Sai dai Rayyan yafi Bilal din haske, kuma yanzun ya dan fishi tsayi duk da su duka dogaye ne, Ayya kan cewa Abbu itama ai doguwar ce duk idan yace tsayin shine yaran suka biyo. Yanzun kuma Bilal na tara suma a kan shi, Rayyan kuma yana asketa kasa sosai sosai, kuma ya tara kasumba a fuskar da ta saka shi wani kwarjini na daban, Bilal gemu ne da samarin yanzun suke ajiyewa da har dariya yake baiwa Ayya. Wani lokacin ma fayau zakaga fuskar shi, ya aske komai.

"Ayya..."

Bilal ya furta yana fadada murmushin shi, kafin ya karasa cikin dakin yana zama kan kujera hadi da sauke numfashi

"Yan Zaria"

Ayya ta fadi tana saka Bilal din yin dariya, yayi kewarta matuka

"Harma mun zama yan Zaria kenan Ayya... Ina kowa? Wallahi nayi kewarki da yawa..."

Sosai Ayya take murmushi, tasan yayi kewarta, tunda yana iya kiranta sau biyar ma a rana. Itama idan ta cika awa hudu bata ga kiran shi ba sai ta neme shi. Rayyan ne ma harta saba, a cikin watannin nan hudune da take tunanin aikin Malam ne ya kirata sau biyu, daga gaisuwa yayi shiru, sai tace ta dinga tambayar shi makaranta da lafiyar shi da ya dinga amsa ta dai-dai

"Ayya gaisuwa ce kawai"

Ya fadi a hankali, da yasan yanda taji dadin gaisuwar da ko sau dayane a wata ya kirata. Tunda yai wayar hannu sai a wajen Bilal ta sami lambar shi saboda yanda bai taba gwada kiranta ba. Idan sunyi magana to Bilal ya bashi wayar shi ya gaisheta, shima daga yanayin yanda zai magana tasan a kunne kawai Bilal ya saka mishi wayar batare daya shirya ba

"Duk idanuwanka yayi zuru-zuru"

Dariya mai sauti Bilal yayi

"Jarabawa ce Ayya... Sai kinga Hamma, gara nima tunda komai na samu ina ci"

Numfashi ta sauke, ai baizo ba ballantana ta gan shi. Da kanta ta mike tare da fadin

"Allah yasa an rubuta a sa'a, bari in dauko maka abincin ku..."

Kitchen ta wuce ta dauko mishi kuloli guda biyu da cokula, mikewa Bilal yayi ya amsa yana ficewa daga dakin zuwa dakin su, tunda ya karya kwana ya hango Layla a tsaye, jikinta sanye da wandon jeans ruwan bula da riga ja a jikinta, sai hula, tayi mishi kyau tun ta gefen ta daya hango, yana jin zuciyar shi ta matse a kirjin shi, cikin shekarun nan ya fahimci muhimmanci da Layla take da shi a rayuwar shi. A cikin shekarun ne kuma yayi kokarin janye jikin shi saboda yanda kusancinta da Rayyan yake wahalar da shi.

Suna zaune su biyu zata zo waje, daga nesa zaka ga yanda idanuwanta suke kafe kan Rayyan, lokutta da yawa in ba kuka Rayyan din ya sata ba, sam bata kula da yana waje. Idan Rayyan yana nan idanuwanta a rufe suke daga sauran abubuwan da bashi ba. Ranar da Rayyan ya riko hannunta ji yayi wani abu na budewa a kirjin shi, shisa yanzun yake tashi yana basu waje, yafi mishi kwanciyar hankali, abinda bai gani ba bazai bata mishi rai ba sam.

Wani lokacin idan Rayyan ya kai mata wani dukan har a zuciyar shi yake jin zafin, amman daya kirata zata sake dawowa. Zaka rantse da Allah rashin kirkin da Rayyan yake mata take so. Bashi da inda yake jin sauki-sauki sai wajen Aisha. Yanzun ma daya huta yayi la'asar wajenta zai tafi ko zuciyar shi zatayi sanyi-sanyi. Da ba kulolin abinci bane a hannun shi sam ba zai karasa inda suke ba, ya koyawa kan shi nisanta da Layla, musamman in tana tare da Rayyan haka. Numfashi yaja yana fitarwa, duk wani karfin hali da zai iya ya tattaro yana takawa har inda take tsaye a bakin kofa, kafin yaga Rayyan da yake tattaro shara.

"Hamma Bilal..."

Layla ta fadi cikin sigar gaisuwa batare da ta kalle shi ba

"Layla..."

Ya amsa a sanyaye, yana shirin karawa da tambayar lafiyarta Rayyan ya dago, da bayan hannun shi ya kai ma Layla wani duka da yasa Bilal runtsa idanuwan shi kamar a kan shi hannun zai sauka, ya bude su a hankali yana ganin Layla da ta kauce tana kara turo baki

"Nace bai sharu ba kika tsaya gardama dani... Uban meye wannan?"

Ya karasa maganar yana nuna mata wata kasa da batasan daga inda ya sharota ba, saboda har karkashin gadon dakin nasu sai da ta share, kujerar shi da teburi kuwa daga su tayi ta ajiye a gefe, sif din kayan su har samanta sai da ta taka kujera ta share, haka ta sake takawa ta gogo daga saman zuwan jiki, tasan halin shi, dan yatsa zaisa ya dangwalo yaga ko da kura babu

"Wallahi shara hudu nayi Hamma"

Ta furta a gajiye, Rayyan din najan wani tsaki

"Ba abinda kika iya sai shirme..."

Ya fadi yana saka abin kwashe shara ya tattare kasar ya mika mata, karba tayi tana juyawa, shima cikin dakin ya shiga. Inda Bilal ya rufa mishi baya yana samarwa kulolin da suke hannun shi mazauni a tsakar dakin. Rayyan links din jikin rigar shi yake cirewa, dan manyan kayane a jikin shi, wani yadi ruwan kwai da ya sake fito da hasken fatar shi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.