Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 108 of 125

Sun kuma karbeshi a mutunce haka amsar duk tarin tambayoyin da yayi. Kananun kayane a jikin shi, rigar mai dogon hannu, shigar da baka raba Bilal da ita. Bai taba tsintar kan shi a yanayin da yake ji ba yau, musamman da ya kasa tuna wanne kalar passport ne Bilal ya manna a jikin takardun su, ko kamannin su sun fito ko basu fito ba. Sauran semester daya Bilal ya kammala karatun shi, yana ji a jikin shi zai dawo, yana kuma fata da addu'ar dawowar ta zamana a kusa, ya iya kalar signature din Bilal, dan ya ko shi Bilal yakan yi mamaki

"Dan dai kana zane ne, shisa bai maka wahala ba"

Cewar Bilal wani lokaci can baya, bai sha wahalar tsayar ma da Bilal karatun ba, yayi amfani da uzurin rashin lafiya ne. Kusan rabin rana yana abu daya, dan akwai kudin da ake biya kafin a iya. Wajen uku saura ya samu ya kammala komai, saiya tsinci kan shi da samun wata natsuwa da baisan daga inda ta fito ba. Baisan kafafuwan shi na daukar shi zuwa gidan su ba sai da ya gan shi a kofar gida, akwai mukullin daki a jakar shi, dan haka bai sha wata wahala ba daya shiga, ya daiyi mamakin yanda jikin shi ya dinga bari wajen budewa.

Yaji dadi sosai da bai samu kowa daya sani ba harya shiga. Dakin zaka rantse anyi watanni ba'a shiga ba saboda kurar da yayi. Sai yaji zuciyar shi ta matse a kirjin shi, tsaye yayi a tsakar dakin yana ganin rayuwar da sukayi a cikin shi kamar an kunna film, yana ganin Bilal a ko ina na cikin daki, yana jin shi a ko ina na zuciyar shi da take wani irin ciwo da baiyi tsammani ba. Ba zaice ga lokacin daya dauka a tsaye a wajen ba, wayar shi da ta fara ihu a aljihun shi ce ta katse mishi tunanin da yayi zurfi a ciki, ko dubawa baiyi ba bayan ya dauka ya daga kiran, karawa yayi a kunnen shi

"Hello..."

Ya fadi muryar shi na fitowa daga can kasan makoshi

"Rayyan"

Yaji muryar Haris cikin kunnen shi da ta saka shi yin gyaran murya saboda yanayin da yake ji

"Hamma"

Ya iya fada, muryar shi na fitowa a shake

"Kana ina? Me ya faru?"

Haris ya tambaya cike da kulawa, yanzun da ya dawo kamar kowa yake jin yanda bai cancanci tarin kaunar da yan uwan shi sukeyi mishi ba, saboda sam bai tuna wani lokaci daya nuna musu ko da kadan a cikin kalar kaunar da sukeyi mishi ba. Amman yana tuna yanda duk ture sun da yayi bai hana su kokarin kusantar shi ba. Kaunar su daban take, kaunar su na da alaka da jinin shi da yake yawo a nasu.

"Rayyan kayi mun magana dan Allah"

Numfashi ya sauke

"Zaria, ina Zaria Hamma"

Haris ya dan jima kafin yace

"Zan kwashe kayan, munyi maganar da Ayya, ka bar shi karshen makon nan da yardar Allah zan shigo Zaria din"

Numfashin Rayyan ya sake saukewa

"Kar ka bayar da komai, duka komai da komai"

Duk da baya gani yasan kai Haris din yake daga mishi

"Babu abinda zan bayar, duka zaka zo gida ka samu kayan. Ka dai fito daga gidan idan kana can, kana jina, ka fito ka tafi...zaka iya ai ko?"

Dan murmushi ya kwacewa Rayyan

"Ba yaro bane ni Hamma..."

Yanajin dariyar Haris din, bai jira yace wani abu ba ya sauke wayar daga kunnen shi yana katse kiran kafin ya mayar da ita aljihun shi. Da gaske kirjin shi zafi yakeyi, kasancewa a cikin dakin ya dawo mishi da abubuwan daya dauka ya rabu da su. Kasancewar shi a dakin ta saka mishi wasi-wasin da bayason zurfafa tunanin shi a kai sam. Shisa ya dauki shawarar Haris din ya fice daga dakin ya mayar da shi ya kulle yana fita daga gidan. Ko daya karasa ya shiga motar da ta mayar da shi Kaduna bai daina jin kirjin shi na zafi ba.

"Magana fa nake tayi maka"

Muryar Bappa ta daki kunnen shi tana dawo da shi daga tunanin daya zurfafa ciki. Mikewa yayi yana fadin

"Dole dai saika fitar da ni..."

Bappa bai kula shi ba ya juya, shima bayan Bappa yabi har suka fita daga gidan zuwa inda motar Bappan take suna shiga.

*

Ba zatace duka duniyar ta daina yi mata dadi ba, saboda yanzun duniyarta ta tattaru ta dawo cikin dakinta. Anan take gudanar da rayuwarta ta yau da kullum, ko da safe ba kullum take samun karfin zuwa su gaisa da Mami din ba. Sai dai ita ta shigo ta dubata, saboda cikinta daya fara fitowa sosai, bata son Mami na ganinta, kowa ma na gidan bataso yana ganin ta. Sai taga kamar basa ganin komai a tare da ita, kamar hatta da sunanta ya bace, banda cikinta babu wani abu da kowa yake gani a tattare da ita yanzun. Jafar ne kadai yakan fito da ita falo wasu lokuttan.

"Malama fito kiga wani abu"

Yakan ce, duk iya kokarin shi na ganin bai nuna cikin jikinta ya dame shi ba, a muryar shi takan ji canjin da ya faru da rayuwar su gabaki daya. Ta kan biye Jafar din suyi kallo tare har su danyi hirar film din, amman gabaki daya babu wani abu da take jin dadin shi. Ba dai ta iya cin wani abu sai mai manja, in dai ba girkinta ita kadai Mami takeyi mata ba to duka dakin su an koma cin abinci ne da manja. Shima kawai wasu lokuttan takan ji idan bataci ba kamar zata mutu, sai kuma yoghurt da baya yanke musu a cikin fridge.

Lokutta kamar irin yau da take zaune dafe da cikinta, hawaye ne masu ciwo suke zubar mata, tun tana daukar zasu kare har ta daina yanzun. Takan yi kukan halin da take ciki, takan kuma yi kukan rashin Bilal ba kadan ba, a hankali a hankali mutuwar ta dinga tabata kamar ciwonta ba zaiyi mata sauki ba. Anisa kuwa yanzun ba sosai suke magana ba, tunda Layla ta fada mata anwa Abbu transfer ne zuwa kudu, shine suka koma gabaki dayan su, sukan gaisa lokaci zuwa lokaci ne. Zuwa yanzun makaranta ce karshen abinda yake ranta, ta rigada ta cire karatun daga zuciyarta.

Rayyan na kokarin kiranta, shima batasan me zatace mishi ba a yanzun. Ko wanka ta shiga bata tsayawa kallon kanta, saboda bata son ganin yanda gabaki daya jikinta ya canza. Jiya ma sai taga kamar har fuskarta ta canza, bata san ko dan ta jima bata kallo mudubi bane ba. Yau ma sam batayi marmarin kallo ba, da ta sau wata doguwar riga ta zira a jikinta sai ta koma kan gadonta. Idan har bata son ganin kanta, tana da yakinin Rayyan ma ba zaiso ganinta ba, ita da kanta ba zataso yaga canjin da yake tare da ita ba.

Zatayi karya idan tace zuciyarta bata mata zafi, amman a cikin abubuwan da ta nisanta zuciyarta da su, samun Rayyan na daya daga cikin su. Ba abu bane mai sauki, amman da duk ranar da zata wayi gari da yanda take kokarin yin wani tunani na daban, tana hasaso dirowar abin da yake cikinta. Tana kuma tunanin yanda rayuwa zata kasance mata bayan hakan, duk ta yanda ta hasaso abin ba mai sauki bane, tsoro da zullumi sun bata taimako wajen danne Rayyan can kasan zuciyarta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.