Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 125

Shagon da yaje siye sai da mutumin ya tambaye shi har sau biyu idan sigari yake son siye

"Malam idan babu ne ka fadamun in tafi"

Rayyan ya fadi maimakon amsa tambayar da mai shagon yayi mishi

"Akwai, wacce iri?"

Cewar mai shagon da wani yanayi a muryar shi

"Ni dai kabani kowacce iri"

Hakan kuwa ya siyi sigarin da sai bayan an bashi ita da lighter din daya siya yabar shagon tukunna ya duba kwalin yana ganin an rubuta aspen a jiki. Zuqar farko da yayi wani irin tarine ya sarqe shi kamar zai shide, amman yana gama dawowa ya sake gwadawa, har ya sha kara biyu bai gane dalilin da yasa mutane suke sha ba, banda bakin shi, da makoshin shi da yaji suna wani qauri-qauri, kirjin shi a cike yake fal da hayaqi. Daga ranar ne kullum idan ya fita sai ya busa yakai kara biyar, har zuwa yanzun ba zaice ga dadin sigari ba, ba zaice ga dalilin shi na sha ba, abu daya zai iya shaidawa, yanda idan yaji yana son sha din jikin shi har wani iri yake yi mishi.

Ya gane dalilin da yasa ake cewa sigari na da wahalar barin sha, duk sanda zai sha a waje zai saka minti a bakin shi dan ya daina warinta, amman shekaranjiya har Ayya sai da tace

"Ni kam bansan inda hancina yake dibomun warin sigari ba"

Sanda ya shiga ya dauki abinci, hakan yasa shi yana shiga daki ya sake kayan jikin shi yana kuma watsa ruwa. Bilal a satika ukkun bai gaji da tambayar shi ba, shikuma bai daina yi mishi shiru ba, har sai jiya da yaji yana son ya sha, amman bayason fita daga gida kuma, saboda zaune yake yana zane, yanzun daya zana jarabawar shi ta gama sakandire yana zaune jiran sakamako ya fito, yakan tsinci kan shi da jin kadaici na rashin abinyi. Musamman idan Bilal yana makaranta, shisa zanen ne kawai abinda yake debe mishi kewa, ba abokai yake dasu ba ko a cikin unguwa ballantana yace zai fita suyi hira.

Idan yagaji da zama a daki yakan fito ko zai ga giccin Layla, haka zai ta mata aiken rashin dalili har saita kosa ta mayar mishi da magana yaga yasa ta kuka tukunna, to jiyan sam bai ganta ba, sanda ya aika a kirata ance mishi kanta yake ciwo ta sha magani ta kwanta. Zai iya cewa harda son ya ganta da yakeyi, ya duba yaga ya jikinta da kuma kin son ganinta da ya hade mishi waje daya ya kara mishi son busa hayakin, ko ba komai zai kalli yanda ya gwanance yake fitar da samfur samfur na hayakin cikin satika kadan haka.

Ya zuqa sosai yana fito da hayakin Bilal ya shigo, bai ma gama ba ya koma mishi ciki yana saka shi fara tari

"Hamma..."

Bilal ya fadi da bayanannen tashin hankali yana karasawa inda Rayyan din yake hadi da mika hannu zai karbe sigarin, Rayyan ya janye hannun shi yana fadin

"Meye haka? Ka daina yi kamar baka san ina sha ba"

Ya san yana sha, tun ranar farko da yaji warinta a jikin shi, da yana da abokai ne ma sai yayi zargin wani daga cikin sune yake shan sigarin suka zauna waje daya har jikin shi ya dibo warin hayakinta, amman Rayyan ne, bashi da zuciyar hakuri da mutane har suyi sabon zama abokai, koya kaso jurewa shine zaiyi fada da kai ya daina maka magana.

"A waje kake sha, me yasa zaka fara a cikin gida? Me yasa? Idan Ayya ta gani fa? Idan Abbu yagani me zaka ce?"

Sake kai sigarin shi Rayyan yayi a bakin shi yana zuqa hadi da fitar da hayakin

"Dan Allah, dan girman Allah ka kashe, idan dole ya zame maka sai kasha, kayi a waje, kar kabari Ayya ko Abbu sugani... Ni dai na roke ka"

Bilal din ya fadi kamar zaiyi kuka, idan har zuciyar shi na zafi akan wannan sabuwar dabi'ar da Rayyan ya kwaso musu, baisan me Ayya da Abbu zasuji ba, maimakon halayen Rayyan din su gyaru, kullum kara watsewa suke kamar ba'a mishi addu'ar shiriya

"Hamma..."

Bilal ya kira yana kallon yanda Rayyan din yake cigaba da busa tabar shi kamar bada shi yake magana ba. Idan yayi wani abin Layla tace

"Jujun ne ya motsa"

Sai abin yaba Bilal dariya, amman yanzun da gaske ya fara yarda da maganarta, Rayyan ba zai rasa almatsutsai ba, in ba haka ba, kana zaune lafiya ba zaka tattago abinda zai saka ran kowa da yake kusa da kai ya baci ba. Tsaye yayi har sai da ya gama shanye sigarin, dan yasan idan gidan Radio zai bude a wajen saboda surutu Rayyan ba zai kula shi ba. Karshen da ya ajiye kan tebir Bilal ya dauka ya saka a aljihun shi

"Ka rufa mun asiri, ka boyeta inda wani ba zai gani ba"

Daukar kwalin Rayyan yayi yana sakawa cikin aljihun wandon shi. Yana sake gyara zama a cikin kujerar da yake zaune, yana kallon Bilal din ya dinga feshe dakin da turaruka. To yau ma da yayi sallar isha'i a waje ya tsaya suna zancen wasan kwallon kafa da matasan unguwa shisa bai shigo gida da wuri ba, ganin lokaci na jira, kuma yasan Ayya na can tana tunanin dalilin da yasa har lokacin bai shiga ya dauki abincin ba yasa shi yi musu sallama ya shigo gida. Yayi niyyar wucewa bangaren Ayya kai tsaye, sai kuma yaji yana son shiga bayi, shisa ya nufi dakin su, inda ya sami Rayyan zaune yana shan sigarin shi kamar yana abin kirki.

Fada yakeyi kamar zai ari baki, ya karasa ya kwace karshen sigarin kenan ya kasheta jikin tebirin da yake ajiye ya sake bude baki zaiyi magana Abbu ya shigo. Tun tasowar su akwai kananun laifuka da Rayyan din zaiyi ya dauke mishi su, zuwa yanzun kuma ko a aiko Rayyan ya kira shi bai fada mishi ba, zai ce ya fada shine ya manta baije kiran ba, irin kananun abubuwa haka da zai iya dauka na laifukan Rayyan duk yanayo. Shisa yau sam karyar cewa shi yake shan sigarin batayi wahalar fitowa daga bakin shi ba sam. Musamman da yaga abinda yake cikin idanuwan Abbu, yanda ya nuna ba zai iya jure wata gurbatacciyar halayya daga bangaren Rayyan din ba.

Sai dai maganganun shi sun daga hankalin Bilal fiye da yanda yayi zato, ya dauka maganganun sun taba zuciyar Rayyan, sai yanzun da yake kallon shi ya sake kunna sigarin shi kamar komai bai faru ba, kamar Abbu bai fadi abinda ya fada ba

"Anya akwai hankali a tattare da kai kuwa Hamma? Ko zuciya ce kai ba'a halliceka da ita ba, da gaske sigarin kake kara kunnawa? Baka ga halin da Abbu ya fita a ciki bane halan? Baka ga me kasa nayi ba?"

Karan sigarin Rayyan ya cire daga bakin shi, saboda baiga dalilin da zaisa Bilal ya tsare shi yana mishi fada kamar kanin shi ba

"Me nasa kayi?"

Ya bukata yana tsare Bilal din da idanuwa, dariyar takaici mai sauti ce ta kwacewa Bilal din

"Tambayata kakeyi? Hamma tambayata kakeyi?"

Yana kallon yanda kowa a gida yake fadin ba'a batawa Bilal rai, jinsu kawai yake, ko suce Bilal na da hakuri, Bilal baya fada, Bilal baya fushi, suna magana kamar a duniya babu wanda yake da halaye nagartattu kamar Bilal, bayan rana bata fitowa ta fadi baiga kalar rashin hakurin Bilal ba, baya saukewa akan kowane sai shi, yanzun ma ga bacin rai nan bayyane a fuskar shi

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.