Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 80 of 125

Dariya Bilal yakeyi daya kwana biyu baiyi irinta ba, idan kaga fuskar Rayyan din zaka rantse da Allah wani abune mai girma ya faru

"Allah ya shiryaka Bilal"

Rayyan ya iya kara furtawa, har lokacin yana jinjina yanda zaka mika wannan kudin ka dauko wata waya. Karasa daukar abinda duk zai bukata Bilal yayi suna fitowa, shiya kulle dakin, Rayyan kuma ya kama hanya yana ficewa daga dakin. Sai da zage zip din jakar shi daya goya ta gaba ya kara saka hannun shi ciki ya laluba yaji magungunan shi suna nan, kafin ya sake kuskuren barin su. Bai san inda zai samu ba a Kaduna, chemist ba zasu siyar mishi babu rubutun likita ba, kuma rabon shi da wani likita kusan shekara daya da wani abu yanzun.

A hanya Bilal ya tsaya ya sai musu ruwa kafin su kama hanyar Kaduna. Hira suke danyi kadan-kadan, Rayyan na sauke wata ajiyar zuciya marar sauti da baisan yana rike da ita ba. Sai yake jin duk surutun Bilal kamar wani sauti daya saba da shi shekara da shekaru sai lokaci daya yaji yayi mishi shiru. Akwai hayaniya a cikin kan shi ko da yaushe. Amman surutun Bilal bai taba zama hayaniya ba, da babu shi a cikin kan nashi sai yake jin shiru a bangaren Bilal din, sai yanzun yaji ya samu wani dai-dai to.

Gyara zaman shi yayi a cikin kujerar yana kwantar da kan shi hadi da lumshe idanuwan shi, bacci ne ya dauke shi, baccin da ya kwana biyu bai samu ba ko da rana, saboda yana kula da yanayin Bilal.

*

Zuciyar shi a makoshi yake jinta lokacin da yayi parking din motar, kan shi ya dora a jikin abin tuqin yana wani irin mayar da numfashi, ji yake kamar zai sume. Ga zufa da take tsatsafo mishi ta ko ina, tunda akayi abin nan rabon shi da ya saka ta a idanuwan shi, ko yanzun ma text yayi mata da ta fito yana bakin hostel din su.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Yake iya furtawa, ga shi Aisha ta riga su gama jarabawa, anzo an dauketa tun shekaranjiya, saboda za'ayi bikin yayarta a cikin satin. Daga shi sai ita zasu tafi, bai san mintinan daya dauka a zaune cikin motar ba. Layla ma tun da taga text din shi cewar yana kofar hostel din su wani abu ya kulle a cikinta, a tsorace take, ita tace mishi su manta da komai, amman ta karanta text din yafi sau hamsin kafin ta iya goge shi, ko itama sakon zai isar mata, ko zata iya mantawa da abinda ya faru.

Amman har yanzun tana jinta kamar babu suttura a jikinta, ko da ita kadai ce a kwance. Sam a aji bataso wani ya zauna kusa da ita, kamar abinda ya faru ya saka mata tsoron maza gabaki dayan su, tayi jimla ne saboda yanda har kanta sarawa yayi ranar farko da Rayyan ya daga hannun shi da niyyar ya kai shi jikinta, wani irin matsananci tsoro taji ya shigeta, sai take ganin duk idan tayi kuskuren yin kusanci da wani namiji abinda ya faru tsakaninta da Bilal zai iya sake faruwa, ta kara shiga wani sabon rudanin.

Tana son Rayyan, wata irin soyayya da har tashin ta take da tsakar dare, rokonta karya taba ganewa ko sanin wani abu ya taba faruwa a tsakanin ta da Bilal, group din su ma fita tayi, dan tafi sati tama manta da shi, sai ranar da ta dan samu natsuwa taga sakonnin su, fita tayi tana goge komai, babu wanda ya tambayeta dalili, a aji ma basu ga fuska ba, ta daina musu dariya, ta koma hade fuska kamar yanda takeyi daga farko, da yake babu wanda baisan ta iya masifa ba duk sai suka kiyayeta. Duk da suna mamakin canzawar ta lokaci daya haka.

Sosai ta kan dauki waya ta gwada kiran Bilal, ko gaisawa suyi kamar yanda suka saba, amman sai ta tsinci kanta da kasawa, bata san me zatace mishi ba, saboda kafin ma ta kira din take jin zufa na karyo mata. Tashin hankalin da take ciki daban yake, dakyar ta iya janyo akwatinta ta sauko da shi, amman ta dade bayan ta sauko kafin ta sami kafafuwan ta su motsa ta fita waje, tana ganin motar shi ta hango shi a ciki ya hada kan shi da gaban motar sai da zuciyar ta tayi wata irin dokawa, kamar ta koma ciki da gudu haka take ji.

Bakinta ko yawu babu sanda ta karasa wajen motar, hannuwanta duk sunyi gumi saboda tashin hankali, ta kama baya ta bude saita kasa, hakan yasa ta kama gaban motar tana budewa, cikin yanayin da ya sanar da Bilal ta karaso. A firgice ya dago yana juya kai ya kalleta, sai ya bude nashi bangaren ya fita kamar tana shirin shigowa da bomb, itama yanda kafafuwanta suke rawa yasa ta shiga cikin motar ta zauna tana mayarwa ta rufe

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Kawai yake furtawa bayan ya fita daga motar, jikin shi babu inda baya bari saboda tashin hankali. Dakyar ya zagaya ya dauki akwatin Layla ya saka a bayan motar, amman ya kasa shiga, ya rasa ta inda zai zagaya ya shiga cikin motar. Ya kusan mintina goma kafin ya samu ya karasa, ya bude ya zauna. Jikin shi ko ina bari yake sanda ya tayar da motar, babu kowa, babu komai a bayan shi, amman sai yaji kamar yana kara motar da wani abu, dakyar yayi kwana, ya runtsa idanuwan shi ya bude su yafi sau biyar yaki daina ganin kamar akwai yana a cikin su.

Sai da suka fita titi, taga yanda yake gefe da gefe, motar na yawo, in suka kara mintina goma akan titin tabbas zai bugawa wani, ko ya giftawa wani su a buga musu

"Hamma..."

Layla ta kira tana jin hawaye sun cika mata ido, mutane zasu ce Rayyan na abubuwa a nutse, amman har gobe ba zata ga mutum da yake komai da natsuwa kamar Bilal ba, shisa take gane idan ran shi a bace yake, ko Haris baya abu da natsuwar da Bilal yakeyi. Ba sanyin jiki gare shi ba, wata irin nutsuwa yake da ita, kamar komai a lissafe yake yin shi. Shisa yau da karara take ganin natsuwa ta kwace mishi abin yake kara tabata

"Hamma kayi parking dan girman Allah"

Ta karasa maganar muryarta na karyewa. Parking din Bilal yayi, zuciyar shi zafi takeyi, baisan da wanne ido zai kalleta ba, baisan me take ji ba idan har shi yana jin kamar duniyar shi tazo karshe. Kan shi ya sake hadewa da jikin steering wheel din, baisan hawayen shi na zuba ba, sai da yaji digar su akan cinyar shi. Kuka yake saboda baisan yanda zaiyi ba, baisan inda zai saka ran shi yaji sanyi ba, yanayin kafadar shi tagani tasan kuka yake marar sauti. Nata hawayen zuba sukeyi itama.

Batajin kowa zai fahimci kunci na zuciya sai ka farka cikin dare, jikinka ko ina yana bari da tashin hankalin da ba zaka iya sanar da mutanen da kasan zasu sama maka sauki ba, mutanen da suka fi kusanci da kai akan kowa, saboda kana tsoron tashin hankalin da kake ciki zai hargitsa tasu duniyar, a lokacin hawayen zasu fara zubar maka, kukan da kake tsoron fitar sautin shi dan kar wani yaji yai maka tambayar da ba zaka taba iya amsa shi ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.