Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 60 of 125
Banda wajen Aisha babu inda yake samun sauki, kamar kaddara ta san zai shiga wani halin da zai bukaci taimakon Aisha a cikin shi shiyasa ta hada hanyar su.
"Hamma kace ya saka rigar nan ayi mishi hoto dan Allah"
Layla ta cewa Bilal din tana katse mishi tunanin da yakeyi
"Ka saka ko dan tarihi, kayi abu daya yau da zai nuna da gaske kayi makarantar nan ba siyen takardun kayi ba"
Bilal ya karashe cike da tsokanar da yaso ta dan washe mishi kishin daya taso mishi, amman hakan bai faru ba. Rayyan din dai ya yarda ya saka rigar. Sun danyi hotuna, kafin suka tafi gida dan Rayyan na kiran kan shi na ciwo. Layla hostel suka rakata tukunna. Bilal na kula da kalar kallon da take yiwa Rayyan, kamar tana son daukar iya hotunan shi da zata iya a cikin makarantar kafin ya tafi, sai yaji kamar ya sama mata sauki ta hanyar fada mata plan din Rayyan din.
"Ni in dai zan samu bautar kasar da zanyi anan Zaria ko Kaduna nake so"
Ya fadi kamar daga sama kwanaki yana saka shi tambayar
"Saboda me?"
Kafadu Rayyan din ya dan daga mishi, duk da a idanuwan shi yake ganin Layla ce bayason yayi nisa da ita. Addu'a yake da dukkan zuciyar shi kar Rayyan din ya sami abinda yake so, ya kamata yayi nisa da Layla, ya taimaka mishi yayi nisa da ita ko zai saukaka mishi jin amanar Abbu da bai rike ba, ko zai daina ganin yanda yake raba zunubin duk wani abu da zasuyi shi da Layla din.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Dec 7, 2020
17
A Zaria yai zaman shi, babu yanda Bilal baiyi da shi ba
"Ka zo mu tafi gida. Idan mukayi sati daya sai mu dawo. Ko dan Ayya..."
Kai Rayyan ya girgiza mishi
"Sai sun ganni zan musu laifi. Ka barni Bilal, ka cikani da surutu"
Shine amsar daya bashi, duk wata magana da Bilal din yayi bayan nan bai ko kalle shi ba ballantana ya amsa. Yana kokarin kare Layla ne iya yanda zai iya. Idanuwan Mami ko Abbu ba zasu hana shi riketa ba idan ya tashi. Ko dan Abbu ya nuna bayaso, akwai abinda zai tunzura shi ya rike Layla a gaban Abbu, abinda har yanzun ya kasa gane kan shi, yana fahimtar yanayin mutane tun kafin ya karanci fannin, shisa baya son su. Amman ya kasa fahimtar kan shi, ya kasa gane abinda yake damun shi.
Ya sha cin karo da abinda ake kira "Depression" a turance, yanzun haka yana kan magungunan shine da basayi mishi aikin komai banda kara mishi kuncin da yake ciki. Zuwa yanzun ya hakura, ya saduda da cewa akwai wani likita da zai mishi maganin matsalar shi, ko zaima fahimceta. Ya dai san katangar da take tsakanin shi da tabin hankali bata da kauri. Shisa ya zabi zama a Zaria, shi zai dauki duk wani surutu da za'ayi. Layla ba zata dauka ba, baya son kukanta, baya son ganin hawayen da bashi bane dalilin su a idanuwanta.
Sam ba zai iya zama a cikin gida daya da ita yayi mata nisa ba. Zaman shi a Zaria shine saukin su dukan su. Kuma ya ma tsaya ya karasa project din shi a satika shiddan da aka bayar ya tattara ya basu yasan ya gama. Su yake jira, ya tafi bautar kasa abin shi. Duk da Ayya ta kira shi a satin farko, sallamar da tayi ya amsa yana yin shiru
"Shine baka zo ba ko Rayyan? Yaushe rabon da in gan ka? Baka tunanin idan kai baka kewata ni zanyi taka?"
Akwai wani yanayi a muryarta a ranar da yasa shi fadin
"Ina abune haka Ayya..."
Yanda ta ce
"Hmm..."
Sai da yaji wani iri, kafin ta dora da
"Allah ya taimaka ya tsare"
Bai iya amsawa ba harta kashe wayar, daya sauke daga kunnen shi bin wayar yayi da kallo, lokutta da dama yakan nemi kusancin daya kamata ace ya kasance a tsakanin mahaifiya da danta a tsakanin shi da Ayya ya rasa. Sosai yake so yaji wannan kusancin, yakan ga Bilal na binta da kallo kamar babu macen da zata zamana da muhimmanci, kima da daraja a idanuwan shi kamarta, zai rantse murmushin da Bilal kan yiwa Ayya bai taba yi mishi irin shi ba. Akan fuskar shi zaka ga tsantsar kaunar da yake yi mata a shimfide. Ko a waya ta kira shi, kafin ya daga Rayyan ya san ita ce, saboda yanda fuskar shi take canzawa gabaki daya.
Ko ran Bilal a bace yake idan Ayya ta kira shi sai yayi murmushi, karshen bacin ran kenan a wasu ranakun. A tare da Bilal yake ganin kaunar daya kamata ta kasance a tsakanin shi da mahaifiyar shi. Zai karya idan yace abin baya mishi wani iri, sosai abin yake ci mishi rai, bambancin da yake tsakanin shi da sauran mutane mai girma ne. A tsayin satikan su kanyi magana da Layla, rannan ma tace mishi
"Dan Allah Hamma ka siya babbar waya"
Tun kafin ta karasa maganar ma yake girgiza kan shi
"Um um"
Ya furta
"Dan Allah, za muna chatting fa"
Numfashi ya sauke yana sakw furta
"Um um"
Jin ta fara cika mishi kunne yasa shi fadin
"Idan kika dameni zan kashe wannan in ajiye"
Sallama tayi mishi da sauri tana katse kiran, sai da yayi murmushin da bai bayyana akan labban shi ba, a cikin kan shi kawai ya tsaya
"Mayya... Mayya ta"
Ya tsinci kan shi da furtawa. Ranar da suka dawo kuwa bata yarda Bilal ya kaita hostel ba, da yake wannan karin daga ita sai shi suka dawo. Aisha bata samu dawowa a satin ba, Mamanta tana asibiti, tafi so taga jikin ya kara warwarewa tukunna ta samu natsuwar dawowa makaranta. Bacci ma ta sha a mota har suka isa Zaria din. Shisa ta ga saurin tafiyar, kewar Rayyan takeyi har cikin kasusuwan jikinta. Ko da wasa a satikan da tayi a gida batayi maganar shi ba, Mami ta tambayeta ya yake sau daya ta amsa da
"Ban sani ba Mami, Hamma Bilal zaki tambaya..."
Kuma da gaske a lokacin bata sani din ba tunda kwana biyu jujun ya motsa baya daga wayarta. Kuma da alama Mamin ta karanci gaskiyarta shisa tayi shiru. Tun daga soron gidan take kiran
"Hammaaa!"
Harta karasa ciki inda ta ga Rayyan tsaye a bakin kofa yana kallon ta, sai ta ga kamar gashin fuskar shi ya kara cika yana kara mishi wani kwarjini da taji har a zuciyarta.
"Hamma"
Ta kira wannan karin da tarin kaunar shi a muryarta tana takawa ta karasa inda Rayyan yake tsaye ko motsi baiyi ba. Kallon ta yakeyi, sai ya ga kamar ta kara girma, ko kuma yanayin rashin makaranta ne, zai iya yiwuwa dadewa da yayi bai sakata a idanuwan shi bane kuma. Amman wani irin abune yake motsa mishi da ganinta. Ba zaiyi karya ba yayi kewarta sosai. Duk wani zane da yayi a satikan abune daya dangance ta, idan ba fuskarta ba, wani abu nata, wata jaka da zai iya tunawa, wani takalmi nata daya gani, ko duk wani abu da zai tuna mishi ita.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.