Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 76 of 125

Yana nan zaune Abbu ya dawo

"Ya mai jikin? Har ya tashi?"

Abbu ya fadi, kai Rayyan ya jinjina mishi, harya karasa ya murza kofar Rayyan yace

"Ya Layla? Abbu ya take?"

Dan juyowa Abbu yayi

"Taji sauki, na barta da Maminta ma, abinci take ci sanda na fito"

Kai Rayyan din ya jinjina zafin da kirjin shi yakeyi yana yin sauki. Da Mami ta biyo Abbu sun dawo zaije wajen Layla. Amman yasan Mami batason shi a kusa da Layla, saboda haka zai jira sai ta tafi, zaiyi wannan hakuri. Wayar shi dai ya zaro daga aljihu yana tura mata sako

"Baki kirani ba da kika ta shi"

Yana shiga tana dawo mishi da amsa

"Sai da su Mami suka zo na tashi Hamma, naji sauki. Ya Hamma Bilal?"

Numfashi ya sauke

"Ya tashi yanzun shima. Allah ya baku lafiya. Ki kula da kanki, zan zo in ganki anjima"

Har yana shirin mayar da wayar aljihun shi yaji sako ya shigo

"Ina son ka Hamma"

Murmushi yayi, abinda ya kwana uku rabon da yaji ko alamun shi, sosai murmushi yayi har hakoran shi suka bayyana, a hankali wani sanyi yake sauka cikin kirjin shi, sake karanta sakon da ya zauna a kwakwalwar shi yayi saboda yana jin muryarta a cikin kan shi inya karanta daga wayar. Ya jima kafin ya iya mayar da wayar aljihun shi, ya kasa daina murmushi. Yanayin da yake ciki bayason ya bar shi, zaiso ace kullum yana cikin yanayin, kafin yayi mata magana tunanin fita ya nemi sigarin da zai sha yakeyi ko zuciyar shi zata kara rage zafi. Amman yanzun yaji baya bukata, dutsen da yake danne da kirjin shi ya daga da kalaman Layla.

Hamma yayi alamar baccin da yanzun yake jin alamun shi, amman bashi da halin kwanciya. Natsuwa ce ya samu shisa ma har baccin ya samu zuwar mishi.

*

Bacci ta sake komawa bayan tayi sallah, babu ciwon kan, sai zazzabi kadan da kuma duniyar da batajin dadin ta. Ta so ta dan watsa ruwa amman batajin karfin jikinta. Sai kuma lokacin Anisa tace zataje ta dawo, sanda ta dawo ta soyo mata kwai ta taho da ruwan zafi da kayan shayi data kullo su a ledoji. Sai kofi da cokali. Layla ta san tana da lakca shisa ta matsa mata ta tafi

"Baki ga naji sauki ba, kinga an fara test, ana iya yin wani babu tsammani, kuma idan akwai wani abin zan kira wayar ki ai"

Bataso tafiya ba

"Dan Allah ki tafi, ni bacci ma zan koma"

Sai da ta ga Layla din ta juya kwanciya da yake tun wajen karfe hudu da aka cire mata ruwan daya kare sai suka barta ta huta. Tafiya Anisa tayi don tayi shirin tafiya aji. Lokacin ne wayarta ta soma ruri, ganin Abbu a rubuce yasa cikinta hautsinawa, sabon zazzabi na dirar mata, amman idan taci gaba dakin daukar kiran su hankalin su zai tashi fiye da yanda tasan ya tashi. Batayi magana da Bilal ba, amman idan yaji zabinta na barin komai daya faru a tsakanin su tasan zai amince. Ta san boye komai shine saukin su, in ma sunce zasu fada ta ina zasu fara?

Kuma jiya Rayyan yace yana son ta, shi ya saukar da zazzabinta ya rage ciwon kan da takeji, ya rage kusan rabin damuwarta, shi ya bata kwarin gwiwar daga wayar Abbu har tana amsa sallamar shi

"Layla... Ya jikin naki?"

Numfashi ta sauke, kenan sun san bata da lafiya, tana da tabbacin Rayyan ne ya fada musu

"Da sauki Abbu, ina Mami?"

Ta tambaya

"Gata nan tana jinki, yanzun zamu karaso ma, muna Zaria"

Mikewa zaune tayi wata irin zufa na karyo mata, kanta take kallo tana neman alamun da zasu iya nunawa Mami wani abu ya faru da kuma yanda zatayi ta boye

"Hello..."

Abbu ya fadi jin tayi shiru

"Sai kun karaso Abbu"

Tayi maganar tana mamakin yanda akayi muryarta bata rawa. Sauke wayar tayi daga kunnenta, tabbas idan bata saita nutsuwarta ba Mami zata gane akwai wani abu, karyar da zatayi take nema amman gabaki daya kanta ya kulle, tana nan zaune tana tunani sai ganin su tayi sun shigo. Wani kukane yake neman taso mata da ta hango Mami, saboda a tsayin rayuwarta Mami ce komai nata, duk da Abbu ya zame mata mahaifin da ta rasa, Mami daban take, ko da tana cikin damuwar da bata taka kara ta karya ba haka takan shige jikin Mami tana mata sangarta, Mamin kuma zata biyeta ta lallasheta a wasu lokuttan in ta kula da gaske akwai damuwa a tattare da ita.

Yanzun ma kasa daurewa tayi, suna karasowa ta zagaya hannuwanta tana rike Mami, hawaye masu dumi na zubo mata, numfashi sosai Mami ta sauke tana samun natsuwa da taga Layla din, dagota tayi daga jikinta tana zama gefen gadon

"Menene na kukan kuma? Ai gamu mun zo"

Mami ta fadi muryarta na rawa, har cikin ranta take godewa Allah da yasa babu abinda ya sami yarinyarta. Jikinta ta taba tanajin da zazzabi

"Kin ci abinci?"

Kai Layla ta girgiza tana share hawayen da yake fuskarta

"Gashi Anisa ta kawomun shayi"

Abbu ta kalla

"Abbu"

Murmushi yayi

"Sai yanzun kika ganni?"

Dariyar karfin hali Layla tayi, amman tanajin yanda wani abu yake budewa a cikin kirjinta. A lokutta da dama na rayuwarta ta saka kafa tayi fatali da duk wata tarbiya da suke dorata a kai, saboda tana ganin a kasan kaunar su akwai rashin wayewa, akwai dogon bambancin da take gani tsakanin yanda sukayi tasu rayuwar a baya da kuma yanda rayuwa take tafiya yanzun.

"Babu wani abu zamani Jabir, duniya bata canzawa, mutanen cikinta ne kawai suke canzawa, bambancin yanda mukayi tamu rayuwar da yanda ku kukeyin taku yanzun shine zabi..."

Mami ta taba cewa Jabir sanda yake mata maganar cewa zamanin su da kuma na yanzun daban ne, sun jima suna dariya bayan Mami din ta tashi, a ganinsu ba zata taba fahimta ba, ashe sune basu fahimceta ba, akwai tarin ma'anoni a kalamanta, ko kan maganar kaya da take yawan yiwa Layla din, ta dauki shekaru tana mata fada da nasiha a kai sai yanzun take kallon abin da kalar idanuwan da Mami ta ke taso ta duba. Abubuwa da damane suke ta mata yawo. A cikin abinda ya faru a kwanakin nan biyu ta daina kokarin gane ya akayi abinda ya faru ya faru, saboda bata da wannan amsar, ta dai san babu tirsasawa a al'amarin saboda rudanin da take ciki shi Bilal yake ciki.

Abu biyu zuwa ukku ta sani a yanzun, kafafuwanta ta dauka taje gidan su Bilal, da ta tura taga basa nan zata iya juyawa kamar yanda Rayyan ya taba balbaleta da fadan shi harda rankwashi da ta kai musu abinci taga basa nan ta zauna tana jiran su. Yana shiga ya ganta ya rankwasheta yana kama hannunta, dakyar ya bari ta saka takalma

"Idan kika ga bama nan karki kara zama, baki da hankali ke kam sam ko? Baki san maza bane kawai a gidan? Karki kara zuwa ki zauna idan ni ko Bilal bama nan, dakin tura dakin ki juya ki tafi gida, kina jina?"

Harya rakata bai daina fada ba, da tabi maganar shi, tunda ko suna nan din baya bari ta zauna. Tana shiga zai mike, shisa ta daina sallamar masu abin hawa. Ko a ranar dan tana tsammamin zata same sune, shisa ta sallami mai napep din. Tunda tana son taga tafiyar Rayyan din in yaso ita da Bilal sai su koma makaranta. Amman da ta juya da taga basa nan, da ta janyo dakin ta juya, sai ta zabi ta shiga ciki harta zauna. Idan Mami taji tana da yakinin tambayar farko da zatayi mata shine

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.