Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 57 of 125

Wayarta ta dauka da take ajiye a gefe jin sakonnin da suke ta shigowa. Tun a hanya an mayar da ita group daman, duk yanda taso ta daina karance-karance da takeyi sai ta tsinci kanta da kasawa, duk idan Nanaa ta turo mata sai ta karanta. Da kanta tace a mayar da ita tun tana mota, duk da wani abu a kasan zuciyar ta na son nuna mata tarin kuskuren da yake cikin hakan, yanayin da take jine ya rinjayi wancen kashedin. Gara taji da abu daya, duk da kome ta karanta din sai ta dinga hasaso Rayyan a tare da ita, cikin yanayin koma meye yake faruwa a abinda take karantawar.

Mafarkai takeyi a kwanakin nan da suka kara addabarta, kallo daya zakayi mata kaga tsantsar ramar da tayi, sai idanuwan. Amman wuyanta duk kasusuwan sun kara fitowa. Sosai taji dadin shigowa Anisa da suka rungume juna kamar sun shekara basa tare

"Nayi kewar ki"

Cewar Anisa tana kara rungume Layla din, sai kace tunda akayi hutu basa manne a waya da chatting

"Nima haka Allah...tun dazun nake duba hanya"

Layla ta karasa tana sakin Anisa, suka karasa suna zama

"Yunwa nake ji, su Yaya zasu kawoni suka tafiyar su yawo..."

Cewar Anisa, Layla ma najin yunwa ta taso mata, tunawa tayi ko abinci bata ci ba itama, ba yanda Mami batayi ba taqi saboda tana zumudin barin gidan.

"Ko mu dafa indomie? Sai mu siyo kwai?"

Dan shiru Anisa tayi tana nazari kafin ta jinjina kai, Indomie din zatafi musu sauri akan duk wani abu da zasuyi tunani. Sai su dora a risho daya, dayan kuma su soya kwai a kai. Layla ta fita siyo musu kwan, Anisa kuma ta dora indomie din.

*

Sosai yake mamaki idan yaji mutane na hirar wani abu da ya saka su nishadi, ko suna hirar ranakun farin cikin su. Baisan ko farin ciki shine lokuttan da Bilal kan fadi wani abu da zai saka shi dariya ba, ko kuma lokuttan da Layla zata kalle shi kamar duniyar ta babu wani abu da take gani banda shi, ko da ya bata mata raine. Akwai wani yanayi mabanbanta da zuciyar shi take shiga a duka lokuttan, amman yanda ake labarin farin ciki yana saka shi tunani sosai. Watakila shi har yanzun bai san wannan yanayin ba, kullum duniyar a cunkushe yake jinta.

Ko da yaushe akwai wani duhu a cikin kan shi, akwai wani kunci da ya zame mishi abokin zama. Akwai ranakun da yakan samu saukin kuncin idan yana tare da Bilal, yakan samu saukin shi sosai duk idan yana tare da Layla, musamman idan hannun shi yana cikin nata. A kwanakin nan ko zanen da yakan dan samu ya rage mishi cunkoson cikin kan shi ya kasa samun natsuwar yi. Ba karamin kokari yayi ba nakin neman Layla. Ba dan Abbu ko Mami ba, sai dan ita din da kanta, ba zai iya jure ganin Mami ta daketa saboda shi ba.

Har yanzun idan ya rufe idanuwan shi yakan ga marin da Mami tayi mata, zuciyar shi kuma na zafi sosai da hakan. Saboda Layla ne yayi nisa da ita badan wani ba, in dan Abbune babu wani abu da maganganun shi suka kara mishi banda tunzura shi ya kusanci Layla din, a lokaci daya kuma wasu daga cikin maganganun suna nisanta shi da ita. Yanayine da shi kan shi ya saka shi a cikin rudani marar misaltuwa. Ba bacci yake samu ba, shisa tsakanin safiya zuwa wata safiyar yake yi mishi nisa matuka. Idan ya ga Bilal yayi bacci sai ya kwanta akan bayan shi ya kalli ceiling din dakin yana tunanin da ba zai iya cewa takaimaimai na menene ba.

A kwanakin ko sallar daya kan tashi yayi sai jikin shi yayi matuqar nauyi. Bilal dai bai fasa mishi hira ba idan ya tashi, duk da baya iya ce mishi komai. Yana dai jin dadin hirar, fiye da yanda zai iya fada. Saboda ita kadai ce yake ji ta zame mishi katanga tsakanin shi da tabin hankali. Tun sanda ta shigo cikin motar yau da zasu dawo yake jinta a wajaje fiye da zuciyar shi, sai yake jin inda maganganun Abbu suka dauketa suka jefa yana budewa. Zai rantse yana jin idanuwanta na yawan neman fuskar shi kamar zasu huda kujerar da yake a kai su leqo shi. Bayan sun sauka ma haka, yana jin yanda take kokarin yi mishi magana.

Sai take kara mishi wahalar da yake ciki, saboda tana yi kamar ita ka dai take azabtuwa da nisan da sukayi da junan su. Duk yanda yake daurewa sai da tayi mishi magana

"Hamma..."

Kawai ta furta sai da tsikar jikin shi gabaki daya ta mike, komai yana neman kwance mishi, shisa ya daga gilashin motar. Jikin shi har bari yakeyi da son fita daga motar ya riketa a jikin shi, so yake ya zagaya hannuwan shi ya riketa dam, yaji duminta ko zai nutsar da hayaniyar da take cikin kan shi. Amman babu wannan damar, zaiyi duk kokarin da zai iya na ganin damar bata samu ba. Sanda suka karasa gida har wani numfashin wahala yake saukewa. Kayan su ma Bilal ne ya shigar musu da shi.

Basu huta ba suka fara share share, har wankin su labule sai da Rayyan din yayi. Yanajin Bilal na fadin

"Kabari a bayar a wanke mana"

Bai saurare shi ba, saboda yana son yin wani abu da zai rage mishi tunani. Sanda ya gama duk wani aiki da zai iya takalowa kan shi har azahar ta kusa, yanayin wanka ya fita yayi sallah ya dawo. Bilal ya sai musu biredi a hanya saiya dafa musu shayi, shi Bilal din yana zaune kan gado ya bude laptop din shi, Rayyan kuma yana zaune akan kujera da kofin shayin da yayi mishi zafi a hanny yana hurawa a hankali da iskar bakin shi cikin son ya huce.

Wani series film ne Bilal din yake kallo tun suna gida mai suna "Suits". Shi kallo ba damun shi yayi ba, idan Bilal ya saka wata rana sunayi tare, tunda ya fara sukan kalli wasu episodes din tare. Duk dai inda ya samu Bilal din na kallo shima dorawa yakeyi. Yanzun ma idanuwan shi ya natsa kan screen din laptop din suna kallon.

"Trevor din nan ba abokin Mike bane wai?"

Rayyan ya tambaya yana kurbar shayin shi, juyawa Bilal yayi saboda yana son tabbatar da cewa Rayyan din magana yayi bayan satikan daya dauka yana azumin yin maganar.

"Abokin shi din nan da suke daki daya"

Rayyan ya sake fadi ganin kamar Bilal bai gane tambayar shi ba, idanuwa Bilal ya runtsa yana bude su akan Rayyan. Baisan yana rike da wani numfashi ba sai yanzun daya sauke shi. Sosai abinda duk yake damun Rayyan din yake ci mishi zuciya. Yayi tambayar duniya Rayyan yayi banza ya kyale shi, har fushi yayi ya gaji ya sauka da kan shi. Yakan dauki kwanaki biyu batare da yace komai ba, amman bai taba daukar wannan kwanakin shiru haka ba.

"Dan Allah Hamma karka sake tsoratani haka... Ko ba zan iya taimaka maka ba, ko banda maganin damuwar ka idan ka fadamun zan saurara. Wasu lokuttan kana bukatar wanda zai saurari matsalarka ne saika sami saukin ta..."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.