Complete Hausa Novels

Martabar Mu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Martabar_Mu_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 102 of 125

Haka kawai ya tsinci kan shi da bude bangaren sakon shi, yana cin karo dana Layla sun fi guda arba'in. Can kasa yayi yana cigaba da dubawa, na MTN ya dinga goge su, saina banki ma duk yabi ya goge. Zuciyar shi nayin tsalle zuwa makoshin shi, jikin shi har bari yake lokacin da yaga sakon Bilal. Da sauri ya bude yana soma karanta na farkon:

"Ban san me zance ba Hamma, na ce ba zan roki ka yafe mun ba saboda ina jin ban cancanci hakan ba. Amman na kasa, rokon yafiyar ka na daga cikin abu na farko da nake son yi. Ka yafe mun, dan Allah ka samu waje a cikin zuciyarka ka yafe mun"

Numfashi yake fitarwa a hankali lokacin da ya sake bude wani sakon

"Kana cikin rudani kamar yanda nake ciki daga randa abin ya faru zuwa yau. Baka tambayeni ba, nayi kokarin maka bayani iya yanda zan iya kaqi saurarena, dan Allah ka karanta abinda zan fadi, bance ka fahimce ni ba, ni kaina ban fahimci komai ba. Amman ka karanta"

Jikin shi Rayyan yake ji ya dauki dumi kamar ana hura mishi wuta, dakyar ya iya samun karfin motsa yatsan shi ya latsa wayar yana samu ya shiga wani sako da alamu ya nuna mishi dogo ne

"Na kaika ta sha ranar na koma gida, laifina ne da ban kunna fitilar dakin ba, amman mun saba Hamma, sai muyi shiga nawa da duhun dakin, ban san tana ciki ba, wallahi ban kawo ma raina Layla na ciki ba, watakila daga baya ta shigo, shima ban san shigowar ta ba. Ruwa kawai na dauka akan tebir na sha, sai kaina ya fara nauyi na kwanta. Ban san me ya faru ba, ban san ya akayi abinda ya faru ya faru ba, ba ina kokarin wanke laifina bane. Ina so ka sani ne kawai, kaji nawa bangaren Hamma, wallahi ban san ya akayi ba. Ka yafe mun, ka yafe mata itama, karka bari kuskurena ya shiga tsakanin tarin kaunar da takeyi maka"

Rayyan bai ma duba dayan sakon Bilal din ba, saboda zuwa lokacin ya tashi zaune, da sauri yake shiga sakonnin Layla yana son tabbatar da abinda tunanin shi yake kawo mishi

"Dan Allah Hamma, wallahi ban nufin in kwanta bakwa nan ba, ruwa kawai na sha sai in dan huta in tafi, jikina yai mun nauyi, naji bani da lafiya lokaci daya. Shine na dan kwanta in nutsu..."

Bai karasa karantawa ba saboda yanda komai yake hautsina mishi. Numfashi yake kokarin fitarwa cike da tashin hankali, baisan lokacin daya danna lambar Layla ba ya kara a kunnen shi, baima ji tayi ringing ba sai dai muryarta da yaji cikin kunnen shi

"Hamma... Hamma na"

Ta furta tana saka wani abu ya tsirga mishi, dakyar ya iya lalubo yawu ya jika harshen shi da yake ji a bude kafin ya bude bakin shi

"Ruwan da kika sha... Layla ruwan da kika sha a roba ne?"

Harya bude bakin shi zai sake tambayar ta ta amsa

"Eh..."

Wani nannauyan numfashi yaja kirjin shi kamar an kulle

"Zaki tuna a ina kika dauka? A cikin dakin mu a ina?"

Wani shirun ta sakeyi da yake ji har bayan zuciyar shi

"Na zauna a gefen gado, anan nagan shi, an sha ne an ajiye kamar, me ya faru?"

Wayar ya sauke daga kunnen shi, baima kashe ba ya mike yana dora hannuwan shi saman gwiwoyin shi ya dan rankwafa kamar mai shirin yin raku'u kafin ya sake mikewa yana furzar da iska ta cikin bakin shi. Ruwan da ya ajiyene suka dauka, daga ita har Bilal ruwan da ya durama kwayoyi ne suka dauka suka sha. Laifin da yake fadama Bilal ba zai yafe mishi ba, laifin da ya ke son taba zuciyar Layla kamar yanda ta taba tashi a kai ne yayi yawo ya zagayo ya shaqe mishi wuya yana girgiza gabaki daya rayuwar shi. Dakin yake gani kamar yana kara zurfi, ko kuma shine yake shigewa cikin wani irin rami da baisan akwai a dakin ba ya rasa.

Sai da tafukan kafar shi suka taka kasa ya gane sun dauke shi zuwa wajen dakin, sun kuma ja shi zuwa bangaren Ayya. Kamar su suke da iko da shi, yanajin dai zuciyar shi take iko da gabaki dayan su, saboda ita ce take son kallon idanuwan Ayya ta fada mata yanda shine sanadin rayuwar Bilal, dan da tafi shakuwa da shi sama da su. Da bai zuba kwayoyin a ruwa ba, da ya zuba din daya shanye abin shi, ko ya fitar da shi. Da ba su dauka ba, Bilal da Layla da basu gani ba sun sha har sunzo in da suke yanzun. Da suna zaman su lafiya, suna rayuwar su cikin walwala. Duka laifin na shi ne, ko da bai ganta a falo ba dakin baccin ta ya karasa yana kwankwasawa, sai da yaji ta bashi izinin shiga sannan ya tura kofar ya shiga yana mayarwa ya rufe

"Ayya laifina ne, ni na kashe Bilal..."

Murmushi Ayya tayi mai ciwo, idan aka tsaya zaqule-zaqule tana da tabbacin laifin zai rarrabu, kuma daga Mami har Abbu ba zasu fita ba. Mami ta dauko musu Layla kamar yanda Rukayya ta fadi, Mami kuma tabarta zuwa Zaria da yardar Abbu. Duk da wani abu a kasan zuciyarta yana fada mata kaddarar da tabi Layla da Bilal Zaria zata iya samun su a cikin gida. Amman kuma ba zata ji kamar laifin na su Mami bane ba, idan har kaddarar ta biyo su Bilal har gida, ba zataji duk wannan abin da take ji ba.

"Ka bar fadin haka Rayyan, mutuwar sabuwa ce shisa. Kowa ma idan ya zurfafa tunani zai iya ganin kamar laifin shine"

Saboda itama tanajin akwai nata laifin, da ta duba Bilal din da dare, bayan yabar dakin Abbu da taje tayi magana da shi. Da ta canza mishi tunani da cewar tafiyar ba mafita bace ba, tafiyar kuma ba zata kawo sauki a zukatan su ba. Amman batayi ba, laifin nan zai zauna da ita na lokaci mai tsayi. Kai Rayyan ya girgiza mata, sosai take kallon shi, zuciyarta na matsewa a cikin kirjinta, duhun da yayi a kwanakin sai kamanin shi da Bilal suka kara fitowa, sai dai Bilal kullum baka raba fuskar shi da fara'a

"Laifina ne Ayya... Ni na zuba abu a ruwa ya sha, duka laifin nawa ne"

Cike da rashin fahimta Ayya take kallon Rayyan din, Haris yace sai ta dinga mishi addu'a saboda yanda mutuwar Bilal ta dake shi, karya samu matsala. Bata dauki abin da muhimmanci ba saboda itama mutuwar ta dake ta. Sai yanzun da yake mata wasu zantuka da bata ganewa. Numfashi yaja yana kokarin bude kafofin shigi da ficen iskar shi da suka toshe, ba zai manta wayar Bappa da Baba ba, kuma Bappa yace mishi

"Sihiri gaskiya ne Rayyan, mutane ba su da kirki wani lokacin, Baba bai gayamun kai tsaye ba, amman ciwon ka na da alaka da hakan"

Bai amsa Bappa ba, saboda bashi da abinda zaice, baiga dalilin da wani zai yi mishi sihiri ba, idan anayi din kenan. Kuma ace tunda karancin shekarun da yasan bai isa daukar hakkin kowa ba balle aji haushin shi, ko a yanzun da girman shi bashida wani abu da zai tsarewa wani komai. Kuma sihirin ace an hana kusancin shi da iyayen shi? Abin da wahalar dauka, sai dai a halin da yake ciki yanzun zantukan dawo mishi sukeyi, ko zai samu wanda zasu raba laifin da yake ji tare, dan nauyin laifin yana gab da danne shi idan har bai raba da wani ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.