Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 10 of 90
Rannan malamarmu bata da lafiya mai koya mana karatun qur'ani da asuba aka turo wai inzo zan ƙarawa wasu hadda,abin mamakin ko da nazo su sai naga ƴan ajin su Nadiya ne gabana yana ta faɗuwa na zauna har na ɗakko qur'anin sai na ji Nadiya na ce wa"Hmm wai arasa wacce za ta ƙara mana karatun sai wannan tuban muzurun har yanzu fa wasu daga dangin uwarta basu musulunta ba,adanginsu uwarta ce kawai ta fara musulunta sai manyan arna kakanninta suma suka musulunta kakanta fa babban fasto ne sai ace kuma wai ita ce za ta koya mana karatu?".
wasu zafafan hawaye ne suka fara zubomin ba tare da na yi tunanin tare su ba saboda hawayen daman na ke son yi ɗin,dariya sosai suke min big girl oganniyar cikinsu ta ce"au shine kullum ake wani yawo da ƙaton hijab na munafunci?to yau sai mun buɗe hijab ɗin munga abinda ake ɓoye mana?.
ban san ta zo kaina ta tsaya ba,ɗaga kan da zanyi naga big girl akaina tana neman ciremin hijabij jikina,da sauri na tashi na matsa lungu idona ya yi jawur ta ƙara matsowa tana ce wa,ai yau Khairat baki da wajen guduwa a hostel ɗinnan muradina na shekaru kusan biyar yau saina cika sa akanki."
tana faɗar hakan ta riƙe hannun da na riƙe hijabin ta yi wa su Nadiya fito da sauri suka taho suka rirriƙeni ni kuwa sai kuka na ke ina ihu,wani wawan mari big girl ta yimin sannan ta ce"duk ihunki da wani fizge fizgenki yau wallahi sai na wulaƙanta ki a skull ɗinnan don daman haushinki na keji sosai na karɓemin saurayin da ki ka yi sir Kamil don haka yau sai na rabaki da abinda ki ke tutiya dashi.
Sosai na ke kuka ina roƙonta da ta yi haƙuri amman sai naga kamar zugata na ke ita dasu Iman duk sun yayyaga min hijabina ya yi kaca kaca dashi bakina duk ya fashe saboda tsabar shan bugun da ya yi,amman har yanzu ban daina kukan ba,sunyi nasarar cire min hijabina na riƙe rigata sukayi sukayi duk yawansu su cire amman suka kasa wani ƙaton abu Nadiya ta ɗakko tana ce wa"tunda kin ƙi ta daɗi bari muyi miki mai gaba ki ɗaya.
Saukar abu na ji akaina,nan da nan na fara ganin wani iri duk sun komamin bibbiyu,ana cikin haka wata secutyn skull ɗin tazo wucewa ta hango duk abinda ke faruwa da dauri ta kaɗa ƙararrawa sai ga duk securityn sun bayyana suka biyota cikin ajin don ganin abinda ke faruwa.
Da sauri suka sakeni suna wani wiƙi wiƙi da idanuwa alamun rashin gaskiya,ai kuwa suka cafkesu alokacin ni tuni na yi suman wahala don ban san inda kaina ya ke ba,duk sun yayyaga min rigata,da sauri ɗaya daga cikinsu ta cire hijabin da ta saka ta rufemin sutura ta,don samana duk a buɗe ya ke har hawaye sai da matar ta yi don ba ƙaramin ba ta tausayi na yi ba.
Daman sun daɗe suna jin labarin yaran da kuma ta'asar da sukeyi na lalata ƴaƴan mutane amman aka ƙi ɗauƙar mataki akansu ana tunanin sharri ake musu.
A ruÉ—e Rashida da Hasiya suka fito daga Hostel É—inmu,daman duk sun damu da rashin dawowa ta da wuri don har sunyi mana abincin karyawa amman ban dawo ba.
Alokacin an fito dani kamar matacciya zuwa ƙaramin asibitin da ke cikin skull ɗin na mu,su kuma su Nadiya aka wuce dasu ɗakin hukumar makaranta.ɗalibai kowa ya yi cirko cirko masu saurin kuka sai yi suke.
Rashida kuwa har bakin ƙofar da aka shiga dani ta shiga tana ta kuka tana ce wa"shikkenan sun kashe khairat wallahi nima bazan taɓa barinku ba nima sai na kashe ku".haka take ta maganar kamar ta ɓaɓɓaɓiya.
Hukumar makaranta suka kirawo Abbanmu a waya daman duk shine ya sakamu a skull É—in don haka hankalinsa a tashe yaje ya tashi yayansa ya ke faÉ—a masa anyi masa kiran gaggawa daga makarantarsu Khairat.
Shima hankalinsa atashe suka fito a hanya suka haÉ—u da Baba tijjani da Baba Auwalu suka shaida musu abinda ya ke faruwa,suma ka sa tafiya aikin sukayi suka ce zasu bisu makarantar don suma hankalinsu duk a tashe ya ke.
Bilal ya fito daga shi sai wandon aikinsa na sojoji da ƴar fal maram itama ta sojojin ce,sunyi masa ƙyau kayan kamar don shi aka yi su,saukarsa kenan awajen iyayen na sa duk yaji abinda ke faruwa don haka kai tsaye ya bisu ko ajje kayansa baiyi ba.
Anyi min allurar bacci wani baccin wahala ya É—aukeni,duk inda naji ciwo kuma an daka plasta an mannesa.
Ko da su Nadiya sukayi ido huÉ—u da yaya Bilal au fitsari sai da sukayi ga shi belt É—in jibga na jikinsa,ai kuwa ko da yaji abinda ya faru jijiyoyin kansa har wani tashi suke idanuwansa sunyi jawur kamar gauta.
Baba Tijjani kuka kawai ya fashe dashi jin ƴaƴansa har guda uku acikin wannan mummanar rayuwar,Baba na ma da ya ke mai dauriyar zuciya ne baiyi kukan ba amman fa hankalinsa ya yi matuƙar tashi ƴaƴansa har guda biyu a cikin wannan ƙazantacciyar rayuwar.
*Miss green ce*
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨*
_Miss Hajo_
Guda É—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huÉ—u N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
...........🥚👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ’¥ðŸŒŽ....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
[23/09, 16:16] Miss GreenðŸ€: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_
📃Littafi na 1
By🪶
*Ummu maher(Miss green)ðŸ*
*GAWURTATTU 5*
---------------------
masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.
SIRRINMU👂ðŸ»*
Manzon Allah (s.A.W)ya yi mana jan kunne ga idan zamuyi magana mufaɗe da tausashen harshe,idan kuma ba zaka iya hakan ba to ka yi shiru ko,faɗi alkhairi ko ka yi shiru🤫
-------
Team
*GAWURTATTU 5*
11🟩12
. . . .rarrashinsu Baba na kawai malaman ke yi don sun san wannan wani maudu'u'i ne na daban,babu wani mutum da zaiso Æ´aÆ´an da ya haifa na cikinsa su zamo suna da irin wannan halin na neman mata ba tare daya shiga wani hali ba,duk zuciyoyinsu sam babu daÉ—i.
Bai san sanda ya cire belt ɗinsa ya hau jibgarsu ba,zuciyarsa kamar za ta fito saboda zafi,wai yau ƙannensa ne acikin wannan halin?ai kuwa rufe idanuwansa ya yi yana ta jibgarsu malaman na ta bashi haƙuri amman ko ta kansu ma bai bi ba,duk wanda kuma ya yi gangancin saka hannunsa wajen cetonsu to fa dashi za'a haɗa,har ita big girl ɗin da sauran muƙarrabanta duk ya haɗesu ya jigba,su Baba kuwa suna gefe basu da niyyar hanashi,sai da ya jibga don kansa sannan ya barsu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.