Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 83 of 90
Anty Halisa ta sakani agaba sai da na sake wanka,da ya ke har wankan tsarki zanyo tare da wasu sirrika waÉ—anda na har haÉ—a kuma ya kamata duk wata mace wacce ta gama al'ada ta yi sa.
Ki dinga tsarki da ganyen magarya da kaninfari baysn gama al'ada yin hakan yana sakawa ki koma dai dai bayan gama haila,sannan ki samu misk ɗan asali da audiga ƴar kaɗan kina goge duk inda jinin ya taɓa.wannan yana ƙarawa mace kima sosai awajrn mijinta.kuma wannan ba sai matar aure ba hatta bazawara ko budurwa za ta iya yinsa.
Zuwa dare kowa ya watse daga ni sai halina na kimtsa cikin doguwar rigar bacci wacce ta amsa sunanta na taje gashi na wanda yasha gyara da mai na gashi masu daɗin ƙamshi,da sanyaya zuciya.
Fara ce ƙal rigar wacce ya ƙwantamin sosai kamar daman anyi tane saboda ni,na sanya hijabina na tada sallar magrib na ɗaga hannaye na sama ina godewa Allah da wannan ni'imar da ya yimin.na aurar salihin bawa irin Shahid na roƙi Allah ya rayamin yara na da al'ummar musulmi baki ɗaya,Allah kuma ya dawo da hankalin ɗana kai na don abin ya razanani sosai a ƙananan shekaru irin na Irfan wai har yasan ya ƙullace ni.na shafa addu'ar sai naji shahid ya ce"Amin".
Da sauri na juyo ina kallonsa,yana sanye cikin pakistan irin wanda ƴan idia ke sakawa irin fari ƙal ɗinnan ya yi kyau sosai.na shagala a kallonsa sai kawai naji ya janyoni baki ɗaya na.ya ce"ni dai adaina kallona haka ƴan mata".ya faɗi hakan cikin salon yaudarata.
Wani yarrr naji tun daga ƙafata har ƙwaƙwalwata na ce"ni ba kallon ka na ke ba.to ma da wani idon kasan ina kallonka"?.sosai na burgesa yadda na yi maganar cikin yana yi shagwaɓa ya lakato gefen kumatu na ya ce"Hayatee yaya ki keji da ki ka ganmu a matsayin mata da miji"?.
Harararsa na yi nima cikin tsoka na ce"ni babu komai".ƙara janyo ni ya yi har muna jin numfashin juna daga nan fa salon ya canja.
Sam Shahid bai da takura kuma yana da matuƙar haƙuri da bi da mace yadda ya kamata.bai matsamin akan komai sai abinda na ce,sosai muka raya darenmu cikin so da ƙaunar junanmu.kuma gaskiya jarumi ne sosai don ba ƙaramin gajiya na yi ba,shi kuwa har kuka ya yi saboda wani irin mugun daɗin dana jiyar dashi.
Sai sakamin albarka ya ke,yana ganin babbar wautar da Bilal ya yi na saki na,don shi gani ya ke babbar wauta ce a saki mata iri na don na haɗu ta ko'ina,sosai Shahid ya mori kayarsa,nima sosai naji daɗin kasancewa dashi,don bashi da takura kamar yaya Bilal,shi shahid dai dai buƙata ne gashi da tausayi sai lallaɓani ya ke yana bani haƙuri kamar ya yimin laifi.ni abin nashi ma dariya ya bani.
Rayuwa da shahid ya nunamin menene daɗin aure,menene shi kansa auren,ashe daman haka aure ya ke da daɗi?ashe ni da acen baya ba aure na yi ba?haƙiƙa sai yanzu shahid ya lasamin zumar aure.bani da matsalar komai agidansa don Ammi ma mutuniyar kirki ce babu ruwanta ko kaɗan.
Na zaɓi in dinga yiwa miji na girki tare da gyara masa ɗakinsa,don ko ina na gidan ma'aikata na shiga su gyara ammanfa nan na yi musu iyaka ciki kuwa har da ɗakina.
Na yi wani irin mugun kyau da fari,ashe dai nima farar ce ba baƙa ba?to me ya hanani yin fari dacen ɗin?".sosai na ke tambayar kai na musamman ma yanzu yadda na yi wata iriyar ƙiba musamman ma hips ɗina kamar an bubbuɗa ni.
Ranar daren farko na Shahid ya yimin kyautar danƙareriyar mota,da kuɗi wanda kawai sai jin alert na yi,na duba na zaro ido alokacin shi kuma yana wajen amminsa na murza idona sannan na duba wani saƙo da ya turomin.
"Hayatee dafatan kin tashi lafiya kada kiga ban tsaya awajenki ba.Ammi ce babu lafiya tun jiya da daddare.ilove u too my wife".
Shafa saƙon na yi ina jin mugun ƙara son shahid har rai na.
Na tashi kenan xan shiga banɗaki ya turo ƙofa ya shigo gabana ya yi mugun faɗuwa.tuno abinda ya faru na sunkuyar da kaina kunya ta isheni.ya ce"ayya meye kuma na kunya?munfa zama ɗaya kenan komai nawa ya zama naki.kin zama ni na zama ke don haka ni gaskiya bana son kunyar nan tana cutar dani.
Ya faɗi hakan yana sungumata sai banɗaki,duk yadda naso wajen hanasa amman bai haƙura ba da kanshi ya ɗakkomin kayan dazan sanya wata doguwar rigace ta atamfa wacce ta yi matuƙar yimin kyau sosai.
Da ya ke shahid na mugun son atamfa sosai,atare muka tafi dashi wajen Ammi ta rungumoni ina yi mata ya jiki ta ce"kai son yanzu sai da ka gaya mata?"ta faÉ—i hakan tana harararsa.
Sosai rayuwarsu tak burgeni don su basa É—aukar rayuwa da zafi gashi dai suna da kuÉ—in amman kuma babu ruwansu da wani saka ido ko wani abu.
Ana cikin wannan ɗan yanayin ne na fara laulayi sosai,wannan karan tun watan farko ya nuna kansa,don ba kaɗan na sha wahala ba duk na yi sanyi babu yadda baiyi da muje asibiti ba naƙi,daya gaji ya kiramin likitansu yazo har gida.
Likitan yana murmushi ya ce"congrat matarka nada ciki amman ƙarami ne sosai,sai kuma an kula da ita don ulcer nason kamata saboda bata cin abinci."
Ya rubuta magunguna yana tafiya ya ɗagani sai yawo ya ke dani yana murna,ni ma sosai naji daɗin hakan don gaskiya inason in haihu musamman dana daɗe ban haihu ɗin ba.Ammi har kyauta ta yimin na gwal shi kuwa gogan wai har ya fara yi wa ɗansa tanadin wani campaninsa wanda ya keji dashi a ƙasar dubai.ni mamaki ma suka dinga bani kamar basu taɓa ganin haihu ba.?
*********
Rayuwa kenan alhaji damas har gidan yari yasa akaje aka fito da Jidda sai dai daga baya akaji labari mara daÉ—i ya kashe ta har lahira,saboda kada ta tona masa asiri.
*Miss green ce*
[23/09, 16:31] Miss GreenðŸ€: *ðŸ®ABIN CIKIN ƘWAIðŸ®*
littafi na 3
*byâœðŸ¿*
Ummu maher(miss green)ðŸ€
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
*SIRRINKI👂ðŸ»*
1
*Yadda ake maganin ƙurajen fuska.*
Daga ummu maher
Asamu garin alim da ma'ul wardi cokali biyu a haɗa arinƙa gogawa a fuska abarshi ya kai minti 15.
2
ko kuma a samu zuma da lemon tsami a dinga shafawa idan mutum zan ƙwanta bacci idan ya tashi ya wanke.
by ummu maher
99. . . . . . .100
. . . .sosai abin ya ɗagawa mutane hankali ba iya su Bilal da captain ba,Bilal da captain suna cikin motar Bilal ɗin ya nisa cikin tunani ya jiyo captain na ce wa"kai Bilal nifa abin Damas yanzu mamaki ya ke bani,tun bayan daya gudu ƙasar waje bamu sake jin ɗuriyarsa ba,ya yi tafiyarsa abinsa ya koma cen yana cigaba da harkokinsa na masha'a da lalata yaran mutane ashe abin yana nan aransa shine ya dawo ya kashe jidda?gaskiya Damas shu'umine ba nawa sa ba."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.