Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 19 of 90
buɗe cikinta ta yi sosai taci abinci kamat wata sabuwar mahaukaciya tasha lemon sosai tana gamawa ta ce"kai Khairat kin samu ladana wallahi rabon da naci abinci haka har na manta wallahi".ni dai bance komai ba ko da ta tashi daga baccin ko brush bata yi ba ina kallonta amman wai tazo har ta iya cin abinci gaskiya Yaya Aliyu yana ƙoƙari.
***
"Umma wallahi Alhaji Damas ya tsaya sosai akan wai sai mun sayar masa da gidannan,kin san wannan mutumin yana da hatsari sosai wallahi,shiyasa muke binsa a hankali".
Hajiya kaka ta kalli Abdul malik sannan ta ce"kai ni fa aduniyar nan ina ganin ikon Allah ace mutum ya dinga tsoron mutum?a i'na aka taɓa haka?ashe duk zafin zuciyarka na banza ne?shi dan ubansa ya isa ya karɓi gidan ya siya to wallahi kuce masa inji uwarku ƴar ƙasar uman bai isa yazo ya ce zai wani amshi gida awaje na ba,da a uman ne da banu shakka sai an garƙame shege,ɗan arnan kan dutse kawai".
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨*
_Miss Hajo_
Guda É—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huÉ—u N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
...........🥚👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ’¥ðŸŒŽ....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
[23/09, 16:17] Miss GreenðŸ€: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI🥚*
MALLAKAR
*ummu maher(miss green)*ðŸ€ðŸ
masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.
*Sirrinmu*
yawan bin ƙwaƙƙwafin miji ma'ana yi masa bincike a ma'ajiyarsa ko a wayarsa yana saka kullum a zauna zargi kuma kunsan aure da zargi haramunne don haka don Allah mata mu kiya ye.
21🟪22
.. . . . .a ƙofar ɗaki na tsaya na bashi jakar na wuce don shiryo masa abinci,ko da ya shiga ɗakin ya hangeta cen nesa da gado tana ta sharɓar baccinta abinta harda yawun bacci,san baiyi mamakin ganin gidan fes ba saboda yadan khairat tana nan,yana shigowa yaji gidan ko ina sai tashin ƙamshi ya ke,tunda sukayi aure da khadija zai iya ce wa bai taɓa ganinta dai-dai da rana ɗaya ta ɗauki tsintsiya ta yi shara ba,kulli yaumin bacci,babu abinda ta iya sai bacci kamar kasa musamman ma da ta samu ciki duk sai abin ya ƙara jagulewa,filon ya fara ɗan bugawa a hankali ta buɗe idanuwanta ta yi miƙa ta buɗe hammatarta gashin nan ya cunkushe sosai ya kauda kansa yana jin rashin daɗi har cikin zuciyarsa ya ce"ke wai me yasa ko da yaushe babu abinda ki ka iya sai baccine?kuma ga ƙazanta ko da khairat tazo ai ba yana nufin ki sakar mata aikin komai bane?musamman yanzu da ki ke da ciki,ai ba'a son yawan ƙwanciya ko ka jibge waje ɗaya kama ta ya yi ace ki dinga ɗan exercise saboda kema zaki fi jin daɗi amman sai ki jibge ki yi ta bacci kamar kasa".
yana gama faɗar hakan ya fita ta kallesa ta baya ta ɗan hararesa ta ce"to ai ya dawo kuma yanxu babu zaman lafiya,wato don ƙanwarsa tana aiki kada ta yi?to wallahi ina ganinta bazanyi aikin komai ba,ƴaƴan ne tsafta duk ta lalatu da wani tsafta-tsafta a damu mutum kawai".tana faɗar hakan ta tashi ta fito waje da kayan jikinta tun na bacci mai makon ta shiga banɗaki ta tsala wanka ta saka kaya masu ƙyau ko babu komai ko don mijinta ya gani yaji daɗi.
ina cikin jera abinci ta fito na kalleta ta gefe na gaisheta,ta amsa tana wani ya mutsa fuska azuciyata na ce"oh Allah ya haɗa yaya da gamonsa mace har mace amman babu tsatfa yadda kasan bola haka ta mayar da kanta,su asalin babarsu ma buzuwa ce,agidanmu ana saka ƴan ɗakinsu a jerin masu ƙyau fari da kyakkyawar halitta amman fa sai dai ƙazanta ce za ta yi maka sallama dasu suna dai ƴammata idan zasu fita idan suka ɗauki ado sai ka rantse ba ƙazai bane amman fa ƙazanta na nan cunkushe jikinsu.
Abincinta ta Zuba ita kaɗai tana ya mutsa fuska ta fara ci,yaya Aliyu ya kalleta ya ce"yanzu don Allah khadija ke bakiji kunyat kanki da kanki ba?yanzu fa ki ka tashi daga bacci ko alwala bakiyi ba bare brush sannan har kizo ki fara cin abinci a ture ma ta bani haƙƙina don bakisan haƙƙina da ke kanki ba sam".
ture abincin ta yi gefe tana tura baki ta ce"gaskiya honey kana takuramin wallahi?daga dawowarka ai ka bari ka huta ma?amman ka balbaleni da faɗa agaban ƙwanwarka salon ta rainani ko"?.
"raini kuma na nawa khadija?ai wallahi sai dai idan mutum bai san halinki,amman babu komai ki cigaba da wulaƙanta ibada wataran kema sai ta wulaƙanta ki".yana faɗar hakan ya fara cin abincinsa hankalinsa ƙwance,a zuciyata na ce Allah sarki yaya aƙwai haƙuri muddin kaga ya yi magana to abu ya ƙure ne musamman akan ibada,ko sanda kafin ya yi aure ba ƙaramin takura mana ya ke akan ibada ba,sai gashi Allah ya jarabcesa da mace mara ibada wacce sam hakan bai dame ta ba.
ko ajikinta sai ma ƙara lomar abincinta da ta yi tana ta lodawa cikinta abinci wanda ya fito sosai ina tunanin ma ta kusa haihuwa,ana haka ya ce "ƙanwata kun gama waec da Neco ko?".
"Eh yaya mun gama sai jiran sakamako a tayamu da addu'ah".ɗan murmushi ya yi sannan ya ce"to Allah ya baku sa'a ai nasan sister ɗina aƙwai ƙoƙari da bada himma insha Allah sai kin fito da good result".ya faɗi hakan yana murmushi.
Na lura haushin hirar da muke yi Anty khadija ke yi don haka ni ko inda take ma ban kalla ba,muna gama cin abincin na ƙwashe kayan na kai kitchen na dawo na gyara wajen tsaf,ya janyo wani ɗan kit ƙarami ya ce"ƙanwata ga wannan tsarabarki ce daman Baba ya yi muku alƙawarin idan kun gama makaranta xai yi muku suprise so shine ni na riga sa".da murna ta na amsa ina yimai godiya.
Anty Khadija ta ya mutsa fuska,na buɗe ƙwalin zaro idanuwa na yi ina kallon kan screen ɗin hamshaƙiyar wayar na zaro ta daga cikin ƙwalin aiphone ce mai masifar ƙyau sai sheƙi take.da tsalle na na rungume yaya ina godiya.sai kuwa naji anty khadija na ce wa"ah ah me ye kuma haka xaki wani rungumesa sai ka ce wata yarinya".ta faɗi hakan tana wani muzurai,da sauri na sakesa na cigaba da yimai godiyar ya ce"su Rashida dasu Nadiya anjima zan kai musu tasu".
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.