Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 30 of 90

ɗan murmushi mama ta yi wanda ake ce wa yafi kuka ciwo,babu abinda ta ɓoye mishi tun farko har izuwa yanzu.

I'danuwansa suka yi jawur alamar zuciyar Ali gadanga ta motsa bakinsa ya yi masa nauyi sosai,ya ma rasa wani irin mataki zai ɗauka akansu mama iklima?ko da kashesu ya yi ba zai daina jin baƙin cikin ɓatawa ƙanwarsa suna da aka yi ba,ƙanwarsa da ya ke so ya ke ƙauna fiye da kansa?don yana matuƙar jin tausayinta tunda i'ta kaɗai ce mace acikinsu.
[03/09, 20:31] Ummu Maher(Miss Green): "Aliyu ba na faɗa maka bane don ka ɗauko mataki,a'a na faɗa maka ne don ka kula da ƙanwarka,kana da gida Allah ya hore maka don haka ka kai khairat gidanka,ban yarda daga yau ta ƙara ƙwana acikin gidan nan ba,saboda nasan abinda zai biyo baya,mahaifinku mutun ne mai matuƙae zuciya musamman idan abu ya fice masa aransa,don haka ka kula,kada ka ce don mun rabu wai zakajo haushinsa,a'a mahaifinka ne kuma shima yana da haƙƙi mai girma akanka don haka a ƙarshe ina ƙara jadda da maka ka kula da ƙannenka kai ne babba don Allah".

Cikin kuka ya riƙe hannun mahaifiyar ta su sannan ya ce"haƙiƙa na yi baƙin cikin rabuwa da ke mamana,mahaifiya ta gari,mai son cigaban ƴaƴanta ako da yaushe,aduk inda ki ke ba zanyi ƙasa a guiwa wajen zuwa ba,insha Allag zaki sameni a mai yi miki biyayya ko da bakya nan."

Sai ya ƙwantar da kansa a hannun mahaifiyar tasa abin tausayi,ako da yaushe idan ya shugo gidansu idan mahaifiyarsa bata nan sai yaji gidan tamkar kango ne,tafiyar wuni kenan?ina ga kuma tafiyar da mutum zai yi baki ɗaya izuwa wani gari na daban?.a dai dai nan Aliyu ya ƙara fashewa da wani irin kuka mai ciwo,tabbas uwa garkuwa ce a wajen ƴaƴanta,uwa ita ce tushen al'umma.

Anan na ke janyo hankalinku ƴan uwa na,muso iyayenmu so na haƙiƙa ba wai son ƙarya ba,musamman ma uwa,uwa ita ce mau tattalin ƴaƴanta da son farin cikinsu a ko da yaushe,uwa ta ƙwammace da taci abinci bata bawa ɗanta ba gwara ta bawa ɗan yaci i'ta ta zauna a haka.

Wa'iya zubillahi!a wannan lokacin namu na yanzu wasu sun mayar da iyayensu tamkar bayinsu,sun ƙwammace su farantawa ƴaƴansu da matayensu akansu,tabbas duk mutumin da bai gama da iyayensa lafiya ba,to wallahi ya yi asarar zaman duniya da kuma na lahira,Allah ya tsaremu aminya bamu damar gamawa dasy lafiya,waɗanda iyayensu suka rasu Allah yajiƙansu amin.
[03/09, 20:40] Ummu Maher(Miss Green): KuÉ—i sosai yaya Aliyu ya ciro a acc É—insa ya bawa mahaifiyarsa,yana tsaye har motarsu ta tashi sai Benin,asalin garin iyayen mamanmu.

goge hawayen fuskarsa ya yi yana jin wani irin zafi acikin zuciyarsa.

***

aranar na bar gidanmu tafiyar da ban taɓa tunanin zanyi irinta ba,ga shi mahaifiyata sanda ta tafi ban sani ba,na yi kuka har na gaji zan shiga sashen hajiya kaka don yi mata sallama,yaya Aliyu ya riƙe hannuwa na yana girgiza min kai alamar a'ah.

Ina ji ina gani na shiga motar muka tafi,kewar mahaifiyat dana gidanmu suka taru suka yi min yawa,haƙiƙa bawa baya taɓa tsalla ke wa ƙaddararsa,Allah ya bamu ikon cinye dukkanin ƙaddarorinmu.

Yaya Aliyu sai tarairaya ta ya ke tun acikin mota,ni kuwa sai kallonsa na ke ina kuma tausayinsa don nasan dannewa kawai ya ke don ya farantamin amman hankalinsa duk atashe ya ke,fiye da na wa nima.

Muna isa gidan da kansa ya fitomin da kayana har cikin gidan na kallesa na yi murmushi idanuwa na da ƙer na ke ganinsu saboda kukan dana sha.

"A.ah don Allah ku tsaya anan!ina zaka jemin da wannan gantalalliyar ƙanwar ta ka?".

*miss green ce*
[23/09, 16:19] Miss Green🍀: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI*

ummu maher(Miss green)🍀🍏

*sirrinmu*
rarrashin mai gida ya yin fushi😃💋🤝

*haba mijina abin alfaharina,haƘiƘa fushinka agareni kanar garwashin huta ne,ka taimaka ka yafemin ko da zan samu sassauci,Allah yabarmu tare my hubby,sai ki shafa hannayensa a hankali*

Wallahi ko shaiƊan ne shi sai ya sakko😃😒

*By miss green dr mata😃*

31🟨32

. . . ."haba wannan abu har ina?ƙanwar ka ta yi cikin shege har ta yi Ɓari,shine ni yanzu za a wani kawo min i'ta gida na?a to wallahi ku koma inda kuka fito amman wallahi ni dai ba dani ba".

"Ke ce dai zaki bar min gida na,kuma idan naji kin Ƙara zagin Ƙanwata da mummunar kalma wallahi sai kin Ƙwammace baki zage ta ba,ya janyo hannuwa muka shiga gidan.

kallonsa kawai take yi da mamaki don da zasu shiga na har bugeta ya yi,hankali na duk a tashe ya ke,wato kowa yasan abinda ya faru kenan?i'ta da take nan har an bugo mata waya an gaya mata,ina zaune a babbar kujera ina kallon saman ÆŠakin kamar dai wani hotone aka ajjemin shi a saman ÆŠakin.

Ina zaune naga yaya Aliyu ya fito daga Ɗaki dagashi sai t.quater da singlet ya shiga Ɗakina wanda na zauna Ƙwanaki dana zo,ba dai wani datti ya yi sosai ba ya shiga ya sharesa tsaf har ban Ɗakin sai da ya share tsaf,sannan ya fito ya sameni na zabga uban tagumi hawaye wasu na bin wasu.

Kawai sau naga yaya Aliyu a gabana ya tsugunna ya cire min ta gumin dana yi,ya saka hannayensa ya gogemin hawayen a hankali sannan ya ce"khairat!me yasa baki yadda da Ƙaddararki ba ne?ashe Allah bai i'sa ya jarabci bawansa bane?to daga yay kada na sake ganinki acikin makamancin wannan halin,ni nasan ke wacece fiye da sanin kanki,ni yayanki ne uwa Ɗaya uba Ɗaya,ko da ace abinda ya faru da gaske ne babu abinda zau saka in guje ki,don Allah khairat ki Ƙwantar da hankalinki ki cigaba da rayuwarki kamar da,gidanmu da mutanen gidanmu ki Ƙyalesu ki manta dasu kamar yadda suka kasa fahimtarki asannu gaskiya xa ta yi halinta kinji Ƴar Ƙanwata".ya faƊi hakan da murmushi akan fuskarsa.

anty khadija na tsaye ta harƊe hannuwanta akan Ƙirjinta ta wani taƁe bakinta a zuciyarta ta ce daga baya kenan,ammsn bata baru maganar na ta ya fito ba,saboda duk iskancinta tana matuƘar jin tsoronsa.

yaya Aliyu da kansa ya shiga kitchen ya dafamin indomie har biyu da Ƙwai wanda yasha su tumatir sai tashin Ƙamshi ya ke,ya dafamin ruwan Ɗumi da madara wadatacciya,har Ɗakin ya kawo min ina ganinshi na yi saurin cire tagumin ina murmushi don naga halin da ya ke shiga idan ya ganni acikin tashin hankali.

da kansa ya dinga bani,na kallesa wasu zafafan hawaye na zubowa acikin idanuwa na,na saka hannuwa na gogesu saboda tausayin yaya Aliyu hannuwansa har kakkarwa suke don ya ciyar dani,shima kana ganinsa zai baka tausayi don ciyar dani ya ke amman jijiyoyin kansa duk atashe.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.