Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 73 of 90
Sosai Hajiya Ruƙayya ta lallashesa har ya sakko,arayuwar duniya babu wanda yafi sanin kan yaro irin uwa,tun yana jariri take gane abinta,tun Bilal yana ƙarami ta sanshi ƙwarai da mita,ko mama ta hanashi da wuri to sai ya yi ta mita kafin ya amsa,shiyasa tun daga nan ta gane Bilal mutum ne me mita,amman bashi da riƙo ko kaɗan.
Ina zaune ina xaune na yi shiru har yanzu tawul ne ajikina wanda na fito da shi daga wanka,na zabga uban ta gumi sai gasu sun shigo da yaran su Nusaiba ne suka fara shigowa,da sauri na tashi na karɓi Ahmad wanda har ya fara kuka na rungumesa a ƙirjina,bai shigo ba sai ya aiko da yaran,Hajiya Ruƙayya ta zauna abakin gadon duk sai kunyarta ta isheni,bayan mungaisa ne ta ce"Khairat da farko dai zan baki haƙuri ne akan abinda Bilal ya yi na ɗebi miki yara,amman ki yi haƙuri badon saboda ɗanane shiba zan faɗa miki kema baki da gaskiya,ki daina barinsu suna kuka don Allah idan zaki shiga wanka ki samu wani ya zauna dasu kinji?saboda irin haka fa har shaiɗanu suna shigar yara,sai kiga an rasa gane kan matsala,kuma alhali mu iyaye mu ke da alhakin kula da yaranmu,don Allah ki kiyaye kinji"?.
Na ɗaga mata kai kawai tsabar kunyarta na kasa basu mama har sai da ta fita.hannuna na rawa na ɗakko Haidar da Iman na fara shayar dasu,ai kuwa zuƙar da sukemin ta yimin yawa har ƙwaƙwalwata sai da naji zafin tsotsar da suke min,na cije leɓe ina yarfe hannu.
Yana tsaye jikin ƙofa yana ta kallo na,sai kuma yaji tausayina duk ya kamashi,ganin yadda na ruɗe har na rame daga ɗaukesu tabbas kenan har yanzu khairat na sonshi tunda tana son ƴaƴansa.sai da na bari suka ƙoshi dukansu sannan na sakasu a kafaɗa ta suka yi gyatsa sannan na ƙwantar dasu ina tofa musu addu'ah tuni bacci ya ɗebesu,na yi murmushi na manna musu kiss a goshinsu ina shafa sajensu wanda ya ƙwanta luf irin na mahaifinsu,tuni na tuno dashi amman kuma madadin so sai naji tsanarsa ta ƙara samun wajen zama.
Na tashi ina cire kaya na kawai sai ya shigo ɗakin,ina juyowa na ganshi tsaye akaina tuni na runtuma da gudu na ɓuya abayan sif,sai kuwa ya ce"dama kinyi fitowarki don na riga dana ga komai tun ma ba yanzu ba".ya faɗi hakan yana hawa kan gadon shima yana binsu da addu'ah yana wasa da ɗan hannayensu gwanin sha'awa.
Sosai na keji da tsiwa ta na ce"don Allah mlm ka fita tun kafin wallahi in tara maka mutane".ina faÉ—ar haksn har hawaye na ke,sosai abin ya bashi dariya sannan ya ce"ok to yi ihun mana?ki tara mutanen kiga idan zan tsorata".?ganin bazai tashi bane yasa na yi saurin tashi na fara saka kayana.
Ya yi murmushi ya matso inda na ke ya ce,da sauri na matsa gefe na ce"Allah ka matso inda na ke Allah ya isa ban yafe ba".da sauri ya matsa gefe ya ce"khairat ni ki kewa Allah ya isa"?.da sauri na É—aga masa kaina alamar eh dashi na ke.
Bai ƙara magana ba ya fita fuuu kamar kububuwa ni kuwa azuciyata na ce.tafi nono fari daman ni haka na keso.
******
Madarar daya siyo ya aiko da ita,ina haÉ—a musu da ita yara suka yi manya dasu tubarkalla.
Tunda Baba na yasan auren mama ya mutu,sai yaƙi yarda ta koma Garinsu ya dinga aiko mata mutane akan ta yi haƙuri ta komawa gidanshi,sai da ƙer ta yadda sai da muka taru dukkanmu har da maher ƙaraminmu,muka saka mata kuka tausayinmu yasa ta aminci.
Aka mayar da aurensu,tuni aka ƙara gyara ɓangarenmu aka ƙara fitarwa da mama babban farlo da ƙurya biyu.ya yi kyau sosai su mama iklima kuwa rayuwa ta garasu inda ayanzu duk sunyi aure,sai dai duk ranar da yaransu suka je wajensu to fa da kuka suke dawowa,har tausayi suke bani.
Nadiya ma aure ya mutu ta dawo gida,don Yaya Aliyu ya gano har yanzu bata daina lesbian ba,ai kuwa ya sake ta saki É—aya.tuni ta lalace ra rame sosai yanzu idan ka ganta sai ta baka tausayi.
Nadiya me izza da ƙwalisa da rashin kunya,amman yanzu duk babu wannan har ɗakina take zuwa musha hira don tuni ta nemi yafiyarmu nida mama tana kuka.
Rashida ce yanzu agidan,har yanzu bayan ɓarin da ta yi bata sake samun ciki ba,Maryam ma dai haka don ita kamar da matsalar jinnu ma.amman dai an dage da magani.
*After 2 years*
A kullum Bilal hankalinsa na kan Khairat duk zuwan da zaiyi da magiya da naci,don sai ya ɓuge da ɗibarsu haidar wai duk don in dawo masa amman ko kallon ƙurarsa bana yi.
Shi kuwa Ahmad commisioner of police ya yi naci har ya gaji na ce bazan auresa ko don matarsa Xuhra,don tun da na haihu bata zo ba,kuma ko a skull yanzu ta daina kulani tunda ya bata labarin ni tsohuwar budurwarsa ce,shikkenan ta ƙaurace min ko aji bata shiga duk inda tasan ina nan.sosai abin ya bani mamaki sai dai ba abin mamaki bane don daman kushinmu na mata ya gaji haka.
Saboda ire iren wannan ma na ce bazan auresa ba,to shima ɗin dai bai haƙura ba,yana nan yana naci amman naƙi bada fuska.
Ƴan huɗu fa sunyi girma ga baki chaƙwai2 sun san mahaifinsu sosai,don idan yazo nigeria har ya tafi suna wajensa.
Rannan na shirya zuwa gidan Anty Halisa.na saka wata doguwar riga ta atamfa ta amshe ni sosai matuƙa don yadda yanzu na ke na zama babbar mace sosai,komai zan zan babu namiji da zai kalleni ya share fatata ta yi luwai luwai.
Ina fitowa na buÉ—e sabuwar motar da Babanmu ya siyomin zan shiga,sai ga shinan ya fito da Æ´an huÉ—u,ganin zan fita yasa suka runtumo da gudu zasu bini,ganin haka yasa ni kuma na figi motata fuuuuuuuu..... .âœðŸ¿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯â€â™€ï¸ðŸ‘ŽðŸ‘‡ðŸ‘‡*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_*Miss green ce*_🤙ðŸ¿
[23/09, 16:29] Miss GreenðŸ€: 87. . . . . . .88
. . . .sosai abin ya bawa Bilal mamaki wato har ƴaƴanta ma bata barsu ba,ka dinga ƙin ƴaƴanka saboda kana ƙin mahaifinsu,shi kuwa zai ga ƙarshen rashin kunyarta don xai yi maganinta.
Wani super market na fara sauka me mugun kyau da tsari,na shiga na wuce ɓangarensu biskit da halawa na fara siya saboda yaran anty Halisa,ina cikin siya sai naji kamar ana kallo na na tsargu na juyo.wani kyakkyawan saurayi na gani kusa dani wanda yafi kama da balarabe don wannan ko kusa bai yi kama da hausawa ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.