Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 56 of 90

Maryan ce tsaye tana rarraba idanu,muka rungume juna na ce"matar babban Yaya Hajiya maryam".kallona take sosai ta magantu dai ta ce"kai Hajiyata Khairat kinga kyaun da ki ka yi?kinyi ɓul ɓul kamar ba ke ba.?gaskiya kinyi kyau tubarkalla.wallahi kamar me ciki?".da sauri na ce"akanki wallahi yaushe ma aka yi auren?gaskiya ni dai ki bari."dukanmu muka saka dariya harda ƙel ƙelewa na ce"ni kuwa Ina su Anty khadija tunda na yi aure bata zo ba?Allah dai yasa lafiya"?.

"hmm lafiya lau dai za'ace kinsan yanzu ciki gare ta,kuma naga yana bata wahala,amman wallahi ni har na fara gajiya da masifarta,rannan fa haka ta gayyato ƙannenta suka zo har gida har ɓangare na suka dinga zagina ta uwa ta uba,wai iyaye na talakawa masu mutuwar zuciya,wai daman ƙwaɗayin abin duniya ne yasa suka auramin Yayanki".tana faɗar hakan ta fashe da kuka.

Sosai ta bani tausayi na ce"gaskiya Maryam banji daɗin abinda ya faru ba,amman idan zan baki shawara har ki ɗauka.kada maganar Anty khadija ta ɗaɗasa ki da ƙasa,har kizo kina damuwa,idan ta faɗa miki duk abinda bai yi miki ba,kawai ki rama Hajiyata a wuce wajen,idan ba haka ba baza ta daina yi miki ba,nima abinda yasa kiga ina ƙyaleta ba komai bane,saboda matar yaya na ce,kodon babu komai zan bata girma.shiyasa na ke ƙyaleta,amman fa ke kishiyarta ce,zata yi ta faɗa miki ne don zuciyarki ta yi rauni akanta,ƙarshe sai kiji bakyason zaman gidan."nan dai na bata labarin zamana agidan Yaya Bilal.

Maryam ta riƙe baki ta ce"oh ikon Allah yanzu daman duk tsanar da ya yi miki abaya bayin kansa bane?haba shiyasa mana tsanar ta yi yawa,gaskiya nidai tun kafin ayi nisa shiga ki ɗakko min ƙwalbar wannan turaren nima in ƙwashi romon damukaraɗiyya,don baza ayi babu ni ba".

Ta faɗi hakan tana murmushi,na ce"ƙwantar da hankalinki ai na riga dana bada kuɗi a kawo muku ke da Rashida,don haka kima daina damuwa,idan har aka kawo har gida zan kawo miki amman idan Hubby ya dawo,sai ya kawoni daman ban taɓa zuwa ba tun bayan aurenmu".murmushi Maryam ta yi ta cigaba da tsokana ta da Ta hubby lallai ana shan soyayya".

Muka cigaba da hirarmu ta aminai,na É—akko wasu abubuwan sirrikan na bata,sosai ta dinga yimin godiya kamar za ta goya ni.

*Ga É—aya daga cikin sirrikan*

*KI KARAWA KANKI DADI*

Kisamu dan bashana da gyadar mata dayayan kankana da farar biya rana da yayan zogale da mazar kwaila ki hadasu waje daya ki dakasu kirinka sha da madarar shanu zakiga yanda me gida zaiyi…

sai yamma Yaya Aliyu yazo ɗaukar Maryam,ta cika cikinta fam da wani haɗi dana yi mana na fresh milk ƙwaƙwa da kuma dabino,ina ɗaga mudu hannu har suka tafi,na kalli sashen jidda har yanzu bata dawo ba don gashi motar nata ma batanan,ayanzu ƙarfe shida na yamma amman bata dawo ba.zuciya ba tada ƙashi sai naji na fara zargin jidda,tun sanda yasa ƙafarsa ya tafin Holand shikkenan itama ta mayar mana da gida kamar ƙofar kasuwa,ko kuma ta tara uban ƙawayenta,marasa tarbiyya irinta suyi ta rashin mutunci.

*****

da ƙer na shirya na tafi skull duk jikina babu daɗi,yau dai na shirya indai na dawo daga skull zanje asibiti don in san meke damuna,don na kasa gane kai na ko kaɗan.abin mamaki kawai sai naga Xuhra da Ahmad wai ya kawo ta makaranta,abin ya bani mamaki sosai amman sai na ɓoye mamakin nawa na ƙarasa don mu gaisa,Ahmad ya ce"Kinga abin mamaki ko?to a gaskiya ba abin mamaki bane don ayanzu tsakanina da Xuhra mun sasanta kanmu,insha Allah nan da wasu ƴan watanni zamu angonce."

Murmushi na yi inajin daÉ—in hakan har zuciyata na ce"kai masha Allah amman fa naji daÉ—i sosai wallahi Allah ubangiji ya barku tare".na faÉ—i hakan ina murmushi.

Ranar yini muka yi muna shan hirar Ahmad awajen Xuhra,har sai da Xainab ta gaji ta ce"kai Xuhra mudai yau wallahi mungaji da wannan hirar,ayi ta hirar abu É—aya?haba ai da gajiya"?.

wannan magana sai da taso ta haddasa matsala,ni ce ma na shiga tsakaninsu har aka samu dai daito,gashi kaina kamar zai rabe gida biyu,na kasa motsa koda yatsana,ganin ina cikin wannan halinne yasa duk kuma hankalinsu ya tashi suka shiga tambayata abinda ke damuna,É—aga musu kai kawai na yi,saboda ni kaÉ—ai nasan abinda ya ke damuna.

Tun kafin driver na yazo suka kaini gida,duk hankalinsu atashe,kamar jira na ke muxo gida sai kuma amai sosai na dinga yinsa kamar zan amayar da ƴaƴan cikina.daman kuma gashi ba wani abin arziƙi na ke ci ba,abin ma da ƙer ya ke samun waje.

Basu tafi d wuri ba,amman sun sanar agida abinda ya sakasu tsayawa,to dukkansu an yarda dasu agidansu,basu da wata matsala don haka suka gyara inda na ɓata suka kaini har kan gado na suka lulluɓeni,suka dafa min ruwan lipton suka ajjemin acikin flask kusa dani,wai idan na tashi insha ko da cikin dare ne,sai kuman Bread ma da suka ajjemin.tuni bacci ya ƙwasheni,suka tafi gidajen iyayensu,duk hankalinsu akaina.

*******

To fa ɓarnar Jidda bata tsaya a iya mijinta ba,har satar yara yanzu take tana kaiwa Alhaji Damas,waɗan nan yara ana satar odojinsu ne,don siyarwa waɗansu mutane ɓata gari,wanda ba ƙaramin kuɗi suke samu da wannan ba,sannan sai a ɗinke cikin yaran kuma baza a mayar dasu wajen iyayensu ba,ƙarshe sai a kaisu ƙasar waje ana lalata dasu,don dole su zama ɓata gari.

Wa'iya zubillah!don Allah iyaye ku dinga kula da Æ´aÆ´anku yadda ya kamata,wallahi musamman ma Æ´aÆ´sn talakawa haka zaki gansu akan titi,a layikansu,suna yawo kamar basu da iyaye,daga nan sai kiga ko a sacesu ko kuma a lalata mana yaranmu,don Allah mudinga kula dasu amanar ubangiji ce awajenmu.

Waɗannan satar yara da aka yi ba ƙaramin tashin hankali Bilal ya shiga ba,tun yana Holland yaji Allah Allah ya ke ya dawo don gani ya ke kamar za'ayi ta Ɗiban yaran ne,ai kuwa washe gari Bilal ya dawo,kai tsaye sai daya fara zuwa ofishinsa, ya shigar da wannan rahoton a kundinsa, suka zauna meeting akan wannan matsalar.

Aranar Bilal ya saka tsasttsauran bincike akan waƊan nan mutanen,ai kuwa direct majiyarsa ta nuna masa daga Ɓangaren Alhaji damas ne, yana son taimakon waƊan nan yaran don baya son rayuwarsu ta shiga babbsn hatsari.

Yana zaune gaban ogansa ya ce"Admiral ba wai muna hana ka shiga shirgin damas bane,mutumin yana da hatsari yadda baka tunani,kuma mutum ne me hatsari sosai don haka sai ka kiyaye sosai,ni zan taimaka maka da dakaru don su taimake ka,amman Bilal ka kula da kanka saboda muna ji dakai sosai acikin sojojinmu,don kai na dabanne acikinsu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.