Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 59 of 90
Kuka Bilal ya fashe dashi kamar ƙaramin yaro,ya buɗe bakinsa wanda ke masa ciwo ya ce"Hajiya khairat ce,ta cuce ni ta cuci rayuwata,kama ta nayi da ƙwarto."
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email É—inki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taÉ“a *Sign Up* shikenan an buÉ—e account a ArewaBooks💃ðŸ»ðŸ˜‚.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MISS
GREEN CE
[23/09, 16:29] Miss GreenðŸ€: 75. . . . .76
. . . . . . a ranar Hajiya kaka ta gyaramin ɗayan ɗakin nata,aka ɗakko ɗayan gadonta har da katifa aka shimfiɗamin a ɗakin aka gyarasa tsaf.sip ɗinta wanda idan baƙi sunzo suke saka kaya itama aka gyaramin,aka ajjemin ita aɗakin,ina yin wanka na shirya cikin doguwar riga dark blue,farin dana yi ya ƙara fitowa sosai ina gama sanya doguwar rigar na shafa cikina wanda ya fito sosai yanzu,na dafe ƙirjina na ce"innalillahi wa inna ilaihi raji'un wai daman ciki ne dani?".na tambayi kaina sai dai babu wanda zai bani amsar,na fashe da kuka sosai.
Sai ga Hajiya kaka ta shigo hankalinta atashe,tayo kaina tana ce wa"yau naga ta kaina yanzu khairat baza ki daina wannan kukan ba,kuka ya zamar maka kamar abinci?don Allah ki daina nima zuciyata bata yimin daÉ—i".ta faÉ—i hakan tana kallona.
Na ƙara fashewa da kuka ina kallon madubin dake jikin ɗakin nawa na shafa ƙasan marata na ce"Hajiya kaka dole ne fa inyi kuka,ahalin yanzu cikine dani fa?".da sauri Hajiya kaka ta dafe ƙirji ta ce"Alhmdh ai ni na yiwa Allah godiya daya sa kina da cikin ma,wannan cikin shine zai ƙara tsone idon maƙiya musamman ma Ruƙayya surukarki,don ɗazu da kiga dawo Ammaru yazo ya bani labari tana cen tana zaginki wai karuwa me bin maza,kinga kuwa yanzu zata tabbatar da hakan sannan hankalinta zai daɗa tashi".ta faɗi hakan tana ɗaga hannunta sama Alamar tana godewa Allah.
Haushin Hajiya kaka ya kamani na ce"ayya hajiya kaka bazaki gane abinda na keji acikin zuciyata ba,sosai na kejin tsanar Bilal araina,na rabu dashi har abadan,ashe harda ƙullin cikinsa ajiki na?wallahi kaka zubarwa zanyi".na faɗi haka ina share hawaye harda majina.
Hajiya kaka ta yi salati ta sanar da ubangiji sannan ta ce"ikon Allah ikon gaske,idan baka mutu ba zaka yi kallo khairat kina cikin hayyacinki kuwa?ko kuwa dai kin samu taɓin hankaline?kin zama me taurin kai Khairat,ba khairat ɗin dana sani adacen baya bace khairat ɗin dana sani acen baya yarinya ce me jin maganar nagaba da ita,amman ba wannan wadda ta tsaya agaba na tana yimin musu ba."
"Kaka nifa wallahi zubar da cikin nan zanyi,tunda ubansu ma bai san da cikin ba,kuma gashi yana zargina kinga ai zai iya ce wa shi ba cikinsa bane,to kinga idan har na bari na haifesa zai iya ce wa shi ba cikinsa bane,kinga me zan ce wa yaron?ce masa zanyi ubansa ya ce shiba shine ubansa ba?kinga kaka bani da amsar da zan bashi dole in zubar da cikin yanzu kinga kowa sai ya huta".
"To dan ubanki Malik baza'a zubar ba,zanga yadda za'ayi ki zubar da cikin idan har ban baki damar hakan ba,daga yau babu ke babu fita daga gidan nan sai inga ta yadda zaki xubar,tunda ke Æ´ar taurin kai ce".tana faÉ—ar hakan ta fita fuu cikin fushi,Hajiya kaka bata fiya saurin fushi ba idan kuwa kaga ta yi fushi to abin ya yi yawa ne.
Ranar nasha kuka kamar me,da yamma Rashida tazo waje na lokacin ina cikin ɗakin naƙi ci naƙi sha Hajiya kaka ta kawo min abinci amman ko kallon abincin banyi ba,saboda fushi itama bata ƙara bi ta kaina ba ta yi zamanta afalo ta kunna radionta,ta ware ta sosai sai ƙara take,haushi duk ya isheni idan na gaji sai in toshe kunnuwa na duka.ina jinta tana ce wa"oho dai babu inda mutum zaije,ko inyamura ce tazo nan baki isa ki fita ba,zan saka akiramin likita har gida ya duba ki eh tunda abin rashin mutunci ne,ai tattaɓa kunnen basu isheni ba eh so na ke sai sun kai ɗari sannan Allah ya ɗauki raina".
Tana cikin wannan maganar Rashida ta shigo,ta ce"a'ah Æ´ar tsohuwa ina khairat É—in?naji banji É—uriyarta ba?."chono baki Hajiya kaka ta yi ta nuna hanyar É—aki na sannan ta ce"tana ciki Æ´ar nema kin san fa tana da ciki to wai shine take son ta zubar eh saboda rashin mutunci,to nidai ba a gidana xa'ayi wannan kisan kan ba,ciki gashi nan har ya turo kai amman wai a haka akeson a zubar,saboda shashanci to wallahi baki isa ba".
Da sauri Rashida ta faɗo ɗakin dana ke ta rungumeni ta ce"Allah na gode maka daka nunamin wannan ranar da zanga ƴaƴan yaya Bilal,don Allah khairat kada ki zubar da cikin nan kome za'ayi kada ki zubar da cikin nan,wannan cikin shine zai kawo ƙarshen komai".ta faɗi hakan tana kallon ciki na wanda ya turo kai sosai.
Na ce"ni fa Rashida sai na zubar da cikin nan,saboda me xan barshi ubansa bai so,ko so ki ke in haihu É—in yazo yana ce ba shine ya yi cikin ba?a'ah wallahi sai na zubar wannan sharrin ma da ya yimin abarni dashi,don haka ki bar wannan ma maganar sai na zubar."na faÉ—i hakan ina tashi daga É—akin don dukkansu haushinsu na keji.
Farlo na fito na zauna Hajiya kaka na ƙwance ta yi matashi da filon kujera ta saka radionta akunne tana ji,ta kalleni ta watsar sannan ta ce"ai kin banza ai ko uwarki ce ta harareni sai na faɗi magana balle ke tabi'i tabi'ina."banza na yi mata ina jin yadda ɗan cikina ke juyawa kamar juyin waina,ya tattaro ya dawo ƙasan mara,ga wata muguwar yunwa dana keji.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.