Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 3 of 90
Muryarta na rawa zata yi magana da sauri ya ɗaga mata hannu ran tsohon soja ya tashi ya fita yabar mata ɗakin,ya koma wajen mahaifiyarsa ya cigaba da lallaɓa ta,don yana fatan ya gama da ita lafiya.
Kuka sosai ta yi awajen kafin ta tashi ta fita,tana tunanin ta yadda za ta gayawa ƴan uwanta wannan maganar garinsu da sai a yini a kusan ƙwana ana tafiya sannan sai da yamma ta yi sannan za a ce su koma da yamman nan ko kai amarya ba ayi ba sunga gida.
Ɗaki ta koma tasha kukanta sosai,a hankali na buɗe ƙofar ɗakin mahaifiyata halin dana ganta a ciku shine ya ƙara jagula min tuna nina,na ƙarasa kusa da ita hankalina atashe ganin fuskarta ta jiƙe sosai da hawaye cikin daburce wa na ce"Mama lafiya me ya faru da ke?"
Bata iya ce wa komai ba ta tashi ta fita,binta na yi da kallo ina hasashen abinda ya faru tabbas hajiya kaka ce ba wani ba,don tun ina ƙarama na sha kama mama tana kuka kuma ba kowa ne musababin kukanba sai hajiya kaka,sam bata san mama na ban san abinda ta yi mata ta tsaneta haka ba.nima bani da zaɓi daya wuce in fito daga ɗakin don haka na yo waje don ƙawayenmu duk sunci ƙwalliya don kai amarya,ina fitowa Rashida ta ce"lafiya naga fuskar mama duk ta canza?ko ke ce kika yi mata wani abin".
"hmm Rashida ni kuwa me zanyi wa mama da za ta yi fushi dani haka?kawai dai kin san tsakaninta da hajiya kaka ina ganin wannan ne amman ba ni ba ce."
"kin san Allah Khairat matar nab gaba ki É—aya ta ishemu a gidannan,ni na rasa dalilin daya sa duk iyayenmu suke cikin gidannan kamar dole,ita kuma ba bari take a zauna lafiya ba,kullum sai faÉ—a ni wallahi matar nan ma na matsu ta margaya mu huta da jarabarta.
Saurin rufe mata baki na yi na ce"wallahi Rashida ki kiyayi wannan bakin na ki kinsan dai matar nan kakarmu ce,babu yadda zamuyi da ita suma iyayenmu haƙuri suke da ita,muma ya kamata muyi haƙurin ko?"
Iman da Salimat da suke juyo hirar da su Khairat suke sai kuwa suka ce"Hmm Rashida wallahi ki cigaba da maganarki kada ki biyewa wannan wacce bata san inda ya ke mata feeling ba,don haka ko muma wallahi mun tsaneta wallahi tunda bata san iyayenmu mu ma dole ne mu tsaneta".
ni dai fitowa na yi babban hall É—in da ake hidimar bikin abin mamaki duk babu Æ´an uwan mama na awajen abin ya É—aure min kai sosai,yanzu fa na gansu awajen amman har na nemesu ban gansu ba.
Aranar dangin mama na duka suka koma ba tare da sun tsaya sai washe garin ba,hankalina ya tashi sosai na fito na yi sashen hajiya kaka,tana zaune ita da wata ƙawarta Hajiya Inna,na gaisheta tana tsokana ta tana ce wa saura na mu muma,kunya ce ta rufeni sai kuwa na ji Hajiya kaka na ce wa"Hmm Hajiya Inna kema dai kya faɗa wallahi wataran idan na ga yaran nan suna shiga suna fice agidannan su kusan ashirin duk ƴan mata,sai in shiga ɗaki inyi ta kuka sai ta buɗe injirnta ta ce"kinga duk inda na yi ƙashin wuya saboda yarannan duk dun tsotseni wallahi".
duk da ina cikin tashin hankali sai da na yi dariya sannan na ce"Hajiya kaka kina da masaniyar dangin mamana duk sun bar gidannan acikin wannan daren ko kai amaryar basu yi ba sunga gidan brother".
"brozo na ce ungo ƴar nema. to sai me don sun bar gidan ai ni sauƙina ne don wallahi idan na fito naga waɗannan samudawan mutanen har zazzaɓi na ke wallahi don ni bana son ganin ire iren inya murai sam agidannan itama uwar taki darajarku take ci wallahi da tuni ta daɗe da barin gidannan".
Da sauri Hajiya Inna ta kalleta ta ce"haba Ramatu ashe har yanzu baki manta da wannan abin ba?Har sun tara zuri'ah Da Ɗanki yanzu da aurensu ya kai shekara 30 Fa amman ai yakama ta a manta da komai tun sanda malik ya auro yarinyar nan shekararta 13 har yanzu da take kusan shekara 43,amman ace haryanzu ba a manta da komai ba?gaskiya bai kamata ba Ramatu ki sani kema fa ɗiyanki suna gidan miji fa?bakya tsoron ayi musu haka?don Allah Hajiya Ramatu wannan abin ya wuce in banda yarinyar nan tana da haƙuri ne da irin ƴaƴan yanzu ne da babu abinda zaisa ba zasu yi miki rashin kunya ba,don kin zagar mata uwa a gabanta.
Har hawaye ya fara wanke min fuskata na tashi na fita daga É—akin,wai ita hajiya kaka me take so ne da mamana?wacce irin tsana ce haka".
ji na yi kamar na buge da abu da sauri na juyo saboda buguwar da goshina na ce"wash".
sosai gabana ya faɗi ganin Yaya Bilal,da sauri na take xan gudu ya janyo bayan rigata tas tas ya kifamin maruka har biyu,na dafe ƙuncina hawaye na ƙara fitowa a idanuwa na ya ce"stupid girl kawai ke bakya kallon gabanku ne da zaki bugeni?to wannan shine last warning matuƙar na biyo hanya to ki kada ki biyo don na tsani kallon wannan dirty face ɗin ta ki,don haka ki kiyaye."
maimakon ya bani haushi sai ma ya ƙara burgeni sosai,abin tausayi wato shi so hana ganin laifi.
Ƙamshin tureransa ya ƙi barin wajen sai da na ɓata minti kusan talatin sannan na tashi na tafi,wajen daya mareni ɗin na shafa hannayensa duk sun fito a kumatuna,ina ta shafa wajen maimakon inji haushi a'ah daɗin marin ma naji don ko babu komai ko madubi na k
Da sauri Hajiya Inna ta kalleta ta ce"haba Ramatu ashe har yanzu baki manta da wannan abin ba?Har sun tara zuri'ah Da Ɗanki yanzu da aurensu ya kai shekara 30 Fa amman ai yakama ta a manta da komai tun sanda malik ya auro yarinyar nan shekararta 13 har yanzu da take kusan shekara 43,amman ace haryanzu ba a manta da komai ba?gaskiya bai kamata ba Ramatu ki sani kema fa ɗiyanki suna gidan miji fa?bakya tsoron ayi musu haka?don Allah Hajiya Ramatu wannan abin ya wuce in banda yarinyar nan tana da haƙuri ne da irin ƴaƴan yanzu ne da babu abinda zaisa ba zasu yi miki rashin kunya ba,don kin zagar mata uwa a gabanta.
Har hawaye ya fara wanke min fuskata na tashi na fita daga É—akin,wai ita hajiya kaka me take so ne da mamana?wacce irin tsana ce haka".
ji na yi kamar na buge da abu da sauri na juyo saboda buguwar da goshina na ce"wash".
sosai gabana ya faɗi ganin Yaya Bilal,da sauri na take xan gudu ya janyo bayan rigata tas tas ya kifamin maruka har biyu,na dafe ƙuncina hawaye na ƙara fitowa a idanuwa na ya ce"stupid girl kawai ke bakya kallon gabanku ne da zaki bugeni?to wannan shine last warning matuƙar na biyo hanya to ki kada ki biyo don na tsani kallon wannan dirty face ɗin ta ki,don haka ki kiyaye."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.