Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 53 of 90

anya ma kuwa xanyi wannan jan ajin da anty halisa ta ce inyi?Kai gaskiya bazan iya ba.mutumin da na ke matuƙar so arayuwata na samesa ai bazan bari inyi wani jan aji ba.garin jan ajin ya tsinke.

Da Sauri na É—akko wayata na kira anty halisa,cikin zumuÉ—i tana É—agawa ta fara tsokana ta da "khairat ta Bilal bada kanki asare kije gida kice ya faÉ—i."sosai naji wani irin nisha É—i ya cika zuciyata na ce"hmm anty albishirinki?".

Da sauri ta ce"goro".na ce "fari ko ja"?.da sauri ta ce"fari".duk abinda ya faru sai dana gaya mata,sosai ta taya ni murna sannan ta ce"hmm wa yaga ya masa barni gabas take.ai wallahi wasan ma yanzu aka soma,wannan turaren da ki ke ganinsa ko asiri idan aka yi wa mutum to tabbas alokacin ya ke warware wa,don haka ki kula da saka sa sosai duk wani gurbi na jikinki kibi turaren dashi.kici gaba kuma da addu'ah insha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe".godiya na yi mata sosai sannan na kashe wayar na rungume filo a ƙirjina ina tuna ranar da zan ganni gani ga yaya Bilal muna zaman aure na haƙiƙa,yana sona ina sonshi.
***

"Wai ni honey lafiya ƙlau kuwa ka ke? Tun ɗazu naga sai tunani ka ke?wallahi duk ka sanya ni cikin damuwa?".jidda ke faɗan hakan tana shigewa jikinsa.duk abinda take bai ma san tana yi ba.kaf tunaninsa ya tafi ga khairat,sau tari yarinyar yana saka ta acikin munana,amman tabbas yarinyar kyakkyawa ce sosai sai yau ya yadda da hakan.

Ganin tana kiɗanta tana rawar tane yasa jidda ta ce"oh wai ni Bilal wani salon wulaƙancin ka koyo ne?da ina ta yi maka abinda zai sakaka farin ciki amman kai hankalinka yana wani wajen cen daban".?

"Jidda!".da ƙarfi Bilal ya faɗi sunanta sannan ya ce"ki shiga hankalinki sam ni ba lusarin namiji bane,wanda mace za ta yi ta faɗa masa magana yadda take so ya kyale taba,ki shiga tai tayinki".ya faɗi hakan yana nuna ta da yatsa,tasan halin Bilal ƙwarai da gaske,idan zuciyarsa ta hau yana iya aika tawa mutum ba dai dai ba,ta zauna kan kujera tana rufe bakinta da ƙarfi ta firfirto da idanuwanta waje,ba komai yasa ta yin hakan ba,bai wuce yadda Bilal ya yi mata ba,a iya saninta Bilal bai taɓa koda yi mata kallon banza ba,ko da ma ace ita ce da laifi to shine ke bata haƙuri.
****

"Wai Aliyu me yasa kullum ka ke yimin wulaƙanci duk akan matarka Maryam?idan ka gaji dani ne ka sake ni mana?amman irin wannan cin fuska da me ya yi kama?".khadija ce ke faɗin hakan tana kuka.

Ya kalle ta sosai cikin nutsuwa ya fara mata magana"khadija ban tsane ki ba?ina sonki sosai kamar yadda na keson Maryam,harma fiye da ita saboda ke ƴar uwa ta ce,duk da babu hadisin daya zo akan idan kana da ƴar uwa ka aure ta,kafi sonta akan waccen saboda ita wannan ƴar uwarka ce,amman ki sani Khadija an halacci zuciya abisa son wanda ya ke kyautata mata,sannan kuma tana ƙin duk wanda ya ke munana mata,to kinga abinda ya ke tsakaninki da Maryam kenan".

"Ai daman nasan haka zaka ce ita tafi kyautata maka,ni dana ke gutsirar naman jikinka ina nama dashi ai sai ka yi ta zagina,tunda wannan matar taka ta shanye min miji".ta faÉ—i hakan tana kuka.

Aliyu mutum ne mai sanyin hali sosai,matuƙar mace tasan kan na miji da gudu zata iya dashi,don sam bai da zafi sosai sai dai idan ka ƙure shi,Salim ne ɗan zafin kai irinsu Bilal.

A hankali ya ƙaraso har gabanta,wani wari ya bugesa kamar ya toshe hanci,amman sanin hakan zai ƙara janyo wani hargitsin sai ya share,ya tsugunna agabanta ya kamo hannuwanta duka biyu ya manna musu wani irin hot kiss,tuni jikin Khadija ya yi mugun sanyi don yadda ya yi mata kiss ɗin.

Ya kalle ta sosai ya kashe mata ido ɗaya,ai tuni khadija ta sallama masa,ya yi murmushin cin nasara sannan ya ce"ummu khairat ina alfahari dake sosai,inason ki yi min wasu alƙawarurruka har guda biyar?".

Da sauri ta ce"insha Allah zan riƙe maka alƙawari mijina,Abban Khairat".ta faɗi hakan ita ma tana kashe masa ido ɗaya.

Yauwa alƙawari na farko shine,kada ki dinga saka damuwar Maryam akanki har ta yi miki illa don kin san halin da ki ke ciki yanzu,ɗan cikinki yana buƙatar kulawarki sosai don haka don Allah ki daina damuwa.sannan abu na biyu ina son ki kasance mai tsafta da kula da kanki da ƴarki khairat,abu na uku ina son ki dinga tausasa zancenki wajen yi min magana,sannan abu na huɗu ki dinga yimin girki kullum a ƙalla sau biyu matuƙar ina sashenki,sannan abu na biyar ina son ki dinga riƙe min sirrina,tare da yimin ƙwalliya da kula dani".

Ya faÉ—i hakan yana yi mata mugun smile É—insa mai tafiya da ita,ta hango asalin kama da mahaifinta akan fuskar Aliyunta,ta magantu ta ce"insha Allah mijina daga yau zaka same ni a mai kula da kai,ta yadda zaka yi alfahari da ni."
Sosai Aliyu yaji farin ciki ya mamayesa,ya rungume ta sosai,da kansa ranar ya yi mata wanka fes suka haɗu suka yi aikin ɓangarenta dashi,zuciyarta fal farin ciki.

Maryam ma da ta gama aikinta nan ɗin tazo,sai dai khadija taƘi bada fuskar yin hakan,kuma ranar Aliyu a ɓangaren maryam ɗin ya ke,sai bayan magrib sannan ya shigo,Maryam ta amshe sa kamar wani abu ma bai faru ba,ya kalle ta sosai ganin kawai dauriya take,ammsn sauran kaɗan ta fashe da kuka.

Da ya ke yasan kan abinsa tuni ya bi da ita yadda ya keso.kafin wani É—an lokaci ta saki jikinta sosai suka faÉ—a hirarsu gwanin sha'awa.

*****

To fa tun daga wannan ranar ne na buÉ—e shafi salo salo,sai na lura yana guest É—insa yana shan iska zanzo in wuce wata,ina shawagi na ko kallonsa banyi,sai in fake da motsa jiki,ai kuwa sosai ya ke shagala da wannan É—in,amman girman kai ya saka shi wani jan aji.

Yauma kamar kullum na fito daga ni sai tree quater ɗin wando baƙi,wanda yabi jikina irin me bin jiki ɗin nan,sannsn na saka wata riga t shart wanda ta ɗameni sosai na ɗakko ruwan gora mai ɗan sanyi,na ƙulle gashin kaina ma'ana na saka ribom ai kuwa ba ƙaramin kyau hakan ya ƙaramin ba,da ya ka irin gashina mai taushi ne wanda ake kiransa roba roba,kuma sai ya yi kamar na yi doughnut ɗinsa ya yi cukus,kamar black american,na saka konbus ɗina mai kyau,irin na mata na fito abina ina ɗan gudu kaɗan,ai baki ɗaya ya shagala da kallona ina kallonsa,na cigaba da bubbuɗawa kamar yadda na saba yi masa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.