Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 54 of 90

Sai ga jidda nan ta fito,ganin abinda ke faruwa yasa ta kusa daskarewa awajen,ta kalleni taga harkar gabana na ke,ta kalli mijinta taga shi kuma aikin kallo na ya ke.

Kawai ganinta na yi agabana tana wani muzurai cikin fushi ta ce"dalla malama koma ɓangarenki zaki fito kina wani muskutawa,kina neman ki haukata mutum".

Dariya sosai na yi kamar na mayar da ita mahaukaciya sannan na ce"oh ikon Allah jidda ki ke kowa?don Allah ki matsa daga kusa dani banda lokacinki,saboda ni dai ina da abinyi,kuma don Allah kiɗan matsa don wallahi wari ki ke kamar mushe?". . .✍🏿

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:24] Miss Green🍀: *_🪺ABIN CIKIN ƘWAI🪺_*

📃LITTAFI NA 2

UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

*Matso kiji*👂🏻

Kada ki kasance mai yawan yiwa mijinki musu wallahi yin hakan yana dakushe ki a wajen mijinki don haka a kiyaye,ba da faÆŠa ko fushi miji ya ke saka ya soki ba,A'ah da rarrashi da kissa ake mallake miji.
-------------------------

59. . . . .60

. . .bai ajje ni a ko'ina ba sai kan kyakkyawan gadonsa,da sauri na tashi cikin tsiwa na ce"haba mlm saboda me zaka wani É—auke ni kamar Æ´ar tsana?don Allah ni ka daina shiga harka ta".

Murmushi ya yi irin na gefen baki sannan ya ce"a'ah nifa ban shiga harkarki ba,kece ki ke shiga harka ta ni yanzu ma fitar min a ɗaki na".wani kallo na aika masa sannan na yi hanyar waje na saka hannuna da niyyar buɗe ɗakin,amman naji kamar an rufe ƙofar,ƙarar mukulli naji alamar mukullin yana hannunsa,na juyo na harɗe hannuwa na a ƙirji,ina yi masa kallon ba kada wayo.

Don nima in nuna masa na iya rainin hankalin sai nazo na zauna abakin gado,na harɗe ƙafafuwana waje ɗaya,shima yadda na yi hakan ya yi sannan ya ce"khairat"!.cikin voice ɗinsa mai daɗi.

A hankali na juyo na kallesa sannan ya ce"haƙiƙa kafin a sami mace kamarki za'a daɗe ba'a sami mace irinki ba,Khairat na kasance mai cutarki da kuma shiga haƙƙinki,amman baki taɓa buɗe baki kin cemin kina son haƙƙinki ba,don Allah ina neman yafiyarki,idan har ban nemi yafiyarki bazan taɓa gamawa lafiya ba don Allah ki yafemin".

Kallonsa na yi sosai ina mai mamakin maganarsa na ce"Yaya Bilal nifa baka yimin komai ba,ban kuma ce ka yimin ba,Allah ya yafe mana baki ɗaya,yanzu dai buɗemin ƙofa in fita saboda bacci na keji".

Na faɗi hakan cikun shagwaɓa wacce ta zamomin ji,matsowa ya yi har inda na ke ya tsugunna agabana,ya ɗago haɓata sosai ya kalleni cikin ido sannan ya ce"Khairar nasan abinda na yi miki da zafi da kuma ciwo,amman don Allah ki yafemin,na rasa me ya shiga ƙwaƙwalwata alokaci ɗaya naji na tsaneki,alhalin baki yimin komai ba,khairat ni na nuna miki sona tun kina ƙarama kuma na tafi na barki dashi,shiyasa har ki ka girma da sona. . ."

Da sauri na ce"wa ni?a'ah nifa bance inasonka ba,idan ma ka taɓa jin hakan to ƙarya ne,amman ni bance inasonka ba,don Allah ka barni in tafi".na faɗi hakan ina tashi tsaye.

Ji na yi kawai ya sureni baki ɗaya,ya ƙara ajjeni akan gadon,muzurai sosai na fara yi don na riga dana saka acikun zuciyata bazan sakko kamar yadda ya ke soba,ya shige banɗaki abinsa sai gashi ya fito daga shi sai tawul,ya kalleni sosai na kauda kaina gefe,don baki ɗaya naji zuciyata ta ƙarye akan Yaya Bilal,sam bazan iya wani fushi dashi ba,amman dana tuno nema wa kaina ƴanci na ke sai na share sa.

Ban san lokacin da na ya ƙaraso inda na ke ba ya ce"maza ki tashi kije ki yi alwala kizo muyi Sallar nafila,mugodewa Allah daya nuna mana wannan ranar,khairat ɗin Yaya Bilal ta auri Bilal ɗinta".

Harararsa na yi sannan na ce"wacce rana kuma ka ke magana akanta?ai ni tuni na manta da wata ranar aure,wata na É—ai É—ai har biyu agidan nan amman kace wai intashi inyi alwala?Yaya Bilal yanzu duk kamanta cutar da ka yi min?ka auro ni amman ka mayar dani kamar me aikin gidanka,sai da ka gama cin amarci da amaryarka sannan yanzu kace wai zaka dawo guna?wallahi bazai yiwu ba,bazan yarda ka rainamin wayo har haka ba,ka koma cen wajen matarka wacce ka keso bani khairat wacce ka tsana ba,don haka don Allah ga hanya ka fitarmin a sashe na".na faÉ—i hakan cikin dauriya kuma fa da zai fita É—in da bansan halin da zan tsinci kaina ba,dauriya ce kawai.

Murmushin nan nasa ya yimin mai tsayawa azuciya sannan ya ƙaraso inda na ke,ya ce"khairat bazan gaji da roƙarki yafiya ba,ki yafemin don Allah ban san nima me yasa na yi miki hakan ba,amman wallahi tallahi da zaki huda zuciyata ayanzu da babu abinda xaki gani sai son khairat,fal acikinsa,Khairat ki fahimce ni,ni nasan kina sona kamar yadda na ke sonki".

"Hmm a taka fahimtar ko?har ka ke ganin ce wa inasonka ne?to ayanzu ban sonka,khairar É—in da ka sani ada cen baya to ayanzu ni ba ita bace,don haka ku fita daga idanuwa na kai da matarka,kuma ka gaya mata ta fita daga harka ta".

Sosai naji ya janyo ni har muna jin numfashin juna,ya kalleni sosai sannan ya ce"ƙarya ki ke khairat ina ganin sona acikin waɗannan idanuwanki na ki,sona bazai taɓa gogewa acikin zuciyarki ba khairat,tun baki san menene so ba na koyar da ke,don haka ke ƴar makarantata ce".

Shagala sosai na yi da kallon fuskarsa abinda ban taɓa samin damar yi a arayuwata ba,sosai ya dinga yimin wani abu wanda na ke neman shagala,ai da sauri na yi gefe ina mayar da numfashi,don har yanzu ina nan da burina akan baxan sako da wuri ba.
Haɗe fuska ya yi sannan ya ce"kije ki yi alwalar ina jiranki".jiki na duk a sanyaye na shige banɗakin na ɗauro alwala na fito,yana zaume yana kallon bakin ƙofar banɗakin har na fito.

Daman already ya saka sallaya,muna idarwa ya juyo ya kama goshina ya yimin addu'ar da manzon Allah (S.A.W)ya koya mana ga wanda ya yi sabon aure.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.