Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 38 of 90
Sai kuwa ta ce"a'ah fa khairat bana son ƙarya ni dai a iya sanina kaf ƴan uwanmu ban taɓa jin ance ɗan uwan mu bane,sai dai idan saurayinki ne?Ammsn gaskiya kuwa idan haka ne kin more saurayi mutum har mutum a tsaye kamar shi ya yi kansa,ga kuɗi ga komai,kuma naji ma ance ɗan sarauta ne ko"?.Ta faɗi hakan tana washe baki.
Ban kula taba sai kuma ta ce"amman khairat yanzu sabida Allah ai an kusa bikinki sai dai ya yi haƙuri,amman wallahi ni dai da so samu ne ki aureshi don ni har yafi min yaya Bilal wanda a kullum ya ke wulaƙanta ki".
Banza na yi mata sannan na yi shigewa ta banÉ—akin dake manne ajikin É—akina ina mamakin shegiyar gulma irin ta anty khadija.
Ganin banyi magana ba yasa ta tashi ta fita,babu abinda M.C ya ɓoye wa Yaya Aliyu a game da haɗuwarmu,ya amshi number yaya Aliyu ya ce"idan auren Khairat ya tashi ku faɗa min".sosai Yaya Aliyu yaji daɗi sannan suka yi sallama da M.C ya shige mota.
Bai dawo gidan ba ya shige mota don ɗakko mama a filin jirgi da ƴan uwanta har uku,saboda bikin khairat don Yaya Aliyu ya yi mata bayani sosai amman fa mama ta yi baƙin ciki sosai,don gani take ai itama uwa ce kuma ya kamata ayi mata uzuri a nemi shawararta don za'ayi wa ƴar ta aure ba tare da saninta ba,badon Aliyun ya faɗa mata ba sai dai taji a gari kuma ga auren Salim da kuma Auren Aliyu ɗin,mama ta dinga yi wa Aliyu faɗa akan ƙarin auren nasa,amman sai Aliyu ya yiwa mamansa bayani sosai na abinda yasa zai ƙara auren,itama maman tasan wasu daga cikin halin Khadija ɗin, ta yi musu fatan alkhairi da samun zaman lafiya mai ɗorewa.
***
"Ahmad lafiya naga yau duk idanuwanka sun kumbura kamar ka yi kuka?me ya faru da kai"?.Hajiya Ramatu ce ke yi wa É—anta C.M wannan tambayar?.
Babu abinda ya ɓoye wa mahaifiyarsa akan Khairat,ya ƙara da faɗin "Hajiya yanzu mata nagari sunyi ƙaranci acikin wannan al'ummar tamu,za kiga mata suna shiga ba-ga matan aure ba ba-ga ƴan mata ba,haƙiƙa babu abinda yasa ni son khairat sai wannan Hajiya shigar tama kaɗai kamar ta matan aure ce,uwa uba tarbiyya."
"Ka yi haƙuri Ahmad Allahn daya jarabce ka shi zai baka mace tagari,wacce zaka yi alfahari da ita,khairat kuma ka cireta aranka kada ka faɗa halaka tunda dai kaga ita yanzu ta kusa zama matar wani,kuma kasan neman aure cikin aure haramun ne".
Suna cikin maganar Inaas ta taho da gudu ta rungume Abbanta tana ce wa"ireally miss u my dady".É—aga ta sama ya yi yana mata wasa suna ta dariya gwanin ban sha'awa.
****
Sosai aka shiga hidamar biki,Anty khadija har da tafiya gida yaji wai don yaya Aliyu zai ƙara aure kuma ya munafunce ta,Alhmdlh Hajiya kaka ta samu lafiya sakamakon wajen magani da aka kaita wadda ƙawarta Hajiya Inna ta kaita. Kuma aka tabbatar musu ce wa asiri ne.
Ai kuwa Hajiya kaka na samun lafiya ta sanya rigima wai sai dai in dawo gidan ayi buki anan,don dole muka dawo har Mama.
Ƴan gidanmu na nan da halinsu na ƴan munafunce2,Mama ta hure kunnunanta ko nemansu bata yi ba,wanda dai yazo wajenta shikkenan,don maman Arman kullum tana wajenmu don duk muna ɓangaren Hajiya kaka,su Mama Iklima baƙin ciki kamar zai kashesu tun daga kan haɗin da aka yi har zuwan mama gidan,don gani suke kamar ta dawo ne,don yadda suka tsani mutuwarsu haka suka tsani mama.
*****
"Jidda don Allah ki yi haƙuri abisa duk abinda ya faru,wallahi bana son yarinyar nan dole kawai za'ayi min,na yi miki alƙawarin ko shiga ɗakinta ma bazanyi ba".
Murmushi jin daɗi jidda ta yi sannan ta ce"hmm gaskiya ni dai duk haka banji daɗi ba,amman ba komai ka riƙemin alƙawari.
Nan dai suka gama Æ´an hirarrakinsu na masoya,sannan ya bawa jidda check na kuÉ—i ta siya wasu abubuwan don hatta kayan É—aki shi ya É—auki nauyin yinsu.
****
Alhaji Damas ya ce"goje ayau na ke son nunawa ɗan talikin nan bai isa ya ce zai ja dani awajen ɗana morewa da amaryarsa ba,zan nuna masa shi har yanzu yaro ne ƙarami,zan koya masa babban darasi wanda sai ya yi dana sanin taɓani,zan koya masa hankali da kuma jan kunne yadda ya kamata,maza ku tafi ko kawo min ajiya ta".
*miss green ce*
*MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email É—inki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taÉ“a *Sign Up* shikenan an buÉ—e account a ArewaBooks💃ðŸ»ðŸ˜‚.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
[23/09, 16:20] Miss GreenðŸ€: 41. .. . . 42
Bilal yana tafiya Jidda ta shiga gida tana shiga gidan kuma wani yaro ya shigo ya ce"wai inji Bilal wai jidda tazo"?.Ɗan murmushi jidda ta yi sannan ta ce"oh yau kuma A.D soyayyarcs bata ƙare ba ko kuwa?".Ta faɗa wa mamansu Bilal ne yazo bari taje,mamanta ta
"ikon Allah ai naga yanzu ya tafi kuma daman bai tafi bane ki ka dawo"?.ɗan murmushi jidda ta yi sannan ta fita tana ƙara jin son Bilal aranta.
Irin motarsa sak ta gani a ƙofar gidansu babbar jip mai shegen ƙyau,ta ƙarasa ta ɗan ƙwanƙwasa ganin ba'a buɗe mata ba,janyo ta taji anyi cikin motar,ta buɗe idanuwa sosai saboda tsoro,wani mummunan mutum ta gani akusa da ita yasha malun-malun fara ƙal,dariya sosai ya ke ɓaɓɓakawa sannan ya ce"kada kiji tsoro na ƴan mata amaryar wannan satin".sai ya ƙara ƙelƙelewa da dariya.
Sosai taji tsoronta ya ƙaru ta ce"don Allah bawan Allah kai waye"?.
Babu abinda Alhaji Damas ya ɓoye mata na dangan takarsu da Bilal na yadda suke takun saƙa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.