Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 64 of 90

Akan gado na zauna na dinga kuka kamar zan amayar da kayan ciki na,ƙarshe dai sai da aman ya fito,na baje akan gado na canja kayan jiki na zuwa na bacci masu ɗan shara shara,na samu waje na ƙwanta ina kunna ƙarfin A.C na ƙwanta aƙasan tiles ɗin ina ajiyar zuciya.

Bilal ya sallami su jidda da a tafi dasu baki É—aya,da za'a tafi dasu mama Iklima Hajiya kaka ta ce abarsu suje da halinsu,Allsh ya yi musu hukunci da kansa.

Ina ƙwance kawai sai ganin mutum na yi akaina tsaye,na ɗaga kaina a hankali don ganin waye?saurin ɗauke idona na yi daga kansa,a take naji duk wani so da na ke iƙirarin ina yi mai to ayanzu ya juye ya zama tsana,ban san me ya faru ya koma hakan ba,ga ciki na da ya yi wani tsini agaba mugun nauyi ya kemin musamman ma idan na ƙwanta,ya ƙaraso da sauri ya sungumeni sai kan gado,ina ta shure shure cizo harda ya ƴushi hannuna saƙale a wuyansa saboda ina tsoron faɗuwa,yana ajjeni akan gadon ya tsuramin eyes ɗinsa masu sakani awani yanayi,amman yau kallon cikin ido na yi masa na matsa gefe da sauri kamar naga abin tsoro.

Murmushi ya yi ya tsugunna a kusa dani ya shafa cikina sosai,a sannu naga wasu hawaye sun jiƙa fuskarsa tare da farin ciki duk alokaci ɗaya,duk da ina cikin wani hali musamman kai na da ke ciwo,amman sai dana yi mamakin kukansa,na tashi da sauri daga kan gadon,da sauri na riƙe ƙasan marata na ce"ashhh".na tsugunna saboda tashin dana yi da sauri yasa naji wannan zafin.

Da sauri ya nufo inda na ke zai taɓani cikin fushi na ɗaga masa hannu sannan na nuna masa hanyar ƙofa na ce"don Allah kafitarmin acikin ɗaki tunda kai ba muharramina ne ba,kuma ka yiwa Allah ka daina taɓani,tunda dai ayanzu babu wani sauran abu da ya ke tsakanina da kai". . . . .da sauri ya ce"ƙarya ki ke khairat,aƙwai abubuwa da yawa waɗanda yasa har yanzu muke kamar da har ma da ƙarin wasu.haryanzu ke matata ce,tunda acikin fushi na yi sakin kinga addini ya bamu damar mu ci gaba da zama tare,sannan khairat ke ƴar uwata ce ta jini ko badon komai ba,ga kuma ciki na da ke jikinki,kinga kuwa aƙwai abubuwa da yawa atare damu".

Da sauri na kallesa na ce"a'ina ka zama mijin nawa?wallahi ni ban yarda ba tunda dai ai ba'aso dole,ni fa ayanzu wata irin muguwar tsanarka na keji,wacce ni kaina mamakinta na ke,kuma ciki da ka ke maganarsa ai zan haihu ko?idan na haihu sai in baka É—anka,kaga shikkenan babu wani abu tsakanina da kai".

Sosai ya ke kuka kamar ƙaramin yaro me shan mama,na tashi cikin fushi zan bar masa ɗakin,da sauri ya tashi ya sha gabana yana kallona da tsagerun idanuwan nan nasa,duk da tsanar dana yi masa amman sai naji yanzu sam bazan iya kallon idon nasa ba,na sunkuyar da kaina sannan a cigaba da magana kamar haka"Khairat na cancanci ki yimin ko wani irin hukunci ne,amman don Allah ki sassautamin hukuncin naki kada ki yimin tsattsaura,wanda ganinki ma zai iya yimin wahala,wallahi Khairat acan cikin xuciyata na ke jinki".

Da sauri na ce"ni kuma awajen zuciyata na kejin ka,kaga kuwa tsana ce mafi muni na ke maka don haka don Allah live me along".na faÉ—i hakan ina kuka sosai,Hajiya kaka ta shigo da sauri.

*Sirrinki*

Yadda zaki kiyaye  vaginal Discharge ( fitar ruwa a farji)

Amfani da nono mai kyua na Fulani,ki debi cokali daya na nonon sai ki shafa a farjinki,ki kyaleshi ya bushe karki wanke,kiyi haka kamar sau uku a ranaAmfani da tafarnuwa,ki samu tafarnuwa 2-3 ki dake saiki zuba a cikin tafashashen ruwa yayi minti 15,saiki dibi ruwan bayan ya huce ki wanke gun ko wane dare na tsawon sati 1.

3. Amfani da APPLE CIDER VINEGAR,

ko ki zuba kofi biyu cikin ruwa a abin shiga   ki shiga ciki tsahon munti 20  ki wanke gun

*MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

Instagram links👇

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/

Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

MISS
GREEN CE
[23/09, 16:29] Miss Green🍀: 75. . . . .76

. . . . . . a ranar Hajiya kaka ta gyaramin ɗayan ɗakin nata,aka ɗakko ɗayan gadonta har da katifa aka shimfiɗamin a ɗakin aka gyarasa tsaf.sip ɗinta wanda idan baƙi sunzo suke saka kaya itama aka gyaramin,aka ajjemin ita aɗakin,ina yin wanka na shirya cikin doguwar riga dark blue,farin dana yi ya ƙara fitowa sosai ina gama sanya doguwar rigar na shafa cikina wanda ya fito sosai yanzu,na dafe ƙirjina na ce"innalillahi wa inna ilaihi raji'un wai daman ciki ne dani?".na tambayi kaina sai dai babu wanda zai bani amsar,na fashe da kuka sosai.

Sai ga Hajiya kaka ta shigo hankalinta atashe,tayo kaina tana ce wa"yau naga ta kaina yanzu khairat baza ki daina wannan kukan ba,kuka ya zamar maka kamar abinci?don Allah ki daina nima zuciyata bata yimin daÉ—i".ta faÉ—i hakan tana kallona.

Na ƙara fashewa da kuka ina kallon madubin dake jikin ɗakin nawa na shafa ƙasan marata na ce"Hajiya kaka dole ne fa inyi kuka,ahalin yanzu cikine dani fa?".da sauri Hajiya kaka ta dafe ƙirji ta ce"Alhmdh ai ni na yiwa Allah godiya daya sa kina da cikin ma,wannan cikin shine zai ƙara tsone idon maƙiya musamman ma Ruƙayya surukarki,don ɗazu da kiga dawo Ammaru yazo ya bani labari tana cen tana zaginki wai karuwa me bin maza,kinga kuwa yanzu zata tabbatar da hakan sannan hankalinta zai daɗa tashi".ta faɗi hakan tana ɗaga hannunta sama Alamar tana godewa Allah.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.