Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 40 of 90
Dariya mero ta tintsire da ita sosai sannan ta ce"ah to mudai ma idan mayun ne ai sai dai kece kika shafamin?Tunda nidai Babana ƙaninki ne,ita kuma khairat kece ki ka haifi Babanta,kinga kuwa sai dai daga kene wannan matsalar".
Hawaye kaka ta farayi sannan ta ce"Allah ya isa na mero da wannan zagin da ki kayimin,kuma wallahi ki yi asannu,don ba ƙaramin aikina bane in saka jikana ya fasa aurenki".
Dariya sosai mero ta yi sannan ta tashi taɗan riƙe doguwar rigarta mai kalar blue da fari da ƙaton takalminta me tsini kalar blue,ta tashi a hankali don takalmin shirin faɗar da ita ya ke,a kunnen hajiya kaka taje ta raɗa mata wani abu,ai da gudu ta fita Hajiya kaka tana ce wa"wallahi uwarki hansai ki ka faɗawa magana bani ba,ƴar banzar yarinya mara kunya".ta faɗi hakan tana fashewa da kuka.
Kunsan me mero ta raÉ—awa hajiya kaka?Hmm ku matso kunnuwanku kuma kuji,cewa ta yi to idan ya fasa aurena ke zai aura ki haifa masa yara.
kun san kuwa dole maganar ta yiwa hajiya kaka zafi,har aka fara tayi party ɗin bani da niyyar tashi,mama sai rarrashina take amman kukan ƙara bulbulowa ya ke tamkar dai an buɗe famfo.
Itama hajiya kaka na bata tausayi sosai,ta rungumeni tana bubbuga bayana sosai da ƙer dai hawayen ya tsaya.Rashida tana tsaye itama kukan take tana sharewa.
Tabbas dole ne khairat ta yi kuka,saboda ko ba don komai ba sai abinda ya faru da ita,tasan halin yayanta tsaf yana da zargi sosai,bazai taɓa amsarta amatsayin matarsa ba,musamman yadda taga mahaifiyarsu na nunawa akan auren yaya Bilal da khairat,ta kasa gane cewa komai muƙaddari ne daga Allah,Daman Allah ya ƙaddara khairat matar Yaya Bilal ce babu yadda kuma za'ayi don Allah ya ƙaddara faruwar hakan.
Da gudu Rashida ta taho ta rungume khairat,ta bayanta tana ta kuka itama,tuni suka fara bawa Hajiya kaka haushi ta ce"Innalillahi gaskiya nidai ku fitarmin daga É—akina tunda babu wanda ya mutu balle ku sakani agaba kuna kuka,kamar za'a kaita inda za'a dinga figar namanta ana miya dashi?Haba abinnan ya yi yawa wallahi,duk kowa ya tafi wajen partyn har wannan uwar rawar kan mero ta tafi amman ke kina zaune kina aikin kuka."
Mama ce ta rarrashemu mu duka har bakin motar da zata ɗaukemu sai da ta kaimu sannan muka shiga ita kuma ta dawo,ƴan uwanta da sukazo tare muka tafi,don ita ta ce baza ta jeba,don haryanzu zuciyarta bata mata daɗi idan ta kalli gidan mijinta da ta bari abisa sharrin da aka laƙabawa ƴarta,shi kuma Malik ba tare da binciken komai ba ya ɗora mata laifi,bayan wannan ma har da tukuicin saki,ta goge hawayen da suka zubo mata.
Hajiya kaka na kallonta tausayin ta duk ya cika mata zuciyarta,ita fa har yanzu bata yadda da abinda aka faɗa akan khairat ba,tabbas aƙwai saran ɓoye acikin lamarin.
****
wani irin mummunan bugawa naji gabana ya yi,hango Jidda wacce ta gaji da haɗuwa wajen yin ado da ƙwalliya,ga gogan A.D a kusa da ita,ta saƙalo hannunta ta bayansa ana musu hotuna,na kalli kujera ta babu kowa akai,na rasa tudun dafawa na tsaya kawai,ganin abinda ke faruwa yasa Rashida zuwa wajena,ta riƙemin hannuna ta kalleni sosai cikin dakiya ta ce"khairat ki nutsu fa,kada ki diririce yadda ki ke aduk sanda kiga yaya Bilal,muje ki zauna".ta riƙe hannuna har kan kujera ta.
Na zauna duk jikina a sanyaye,ina kallonsu ta gefe,ko ƙura ta basu kalla ba hotunansu kawai suke cikin farin ciki,kana kallon fuskokinsu kasan cike suke da son junansu.
Juyar da kaina gefe na yi ina ɗan kallon mutanen wajen,hall ɗin ya cika ɓam,kamar ba gobe kowa sai harkokinsa ya ke,sai dai fa ƴan gulma sun kasa sun tsare don suga abinda zai faru.
Ƙawaye na da suka zo sai rungumeni suke muna hotuna,suna dariyarsu sai dai suma sun fuskanci ce wa nifa ko tani mijin ma ba ya yi,wata ƙawarmu Safiya ta ce"hmm ni dai idan baka mutu ba ka yi kallo?ki duba kiga namiji har namiji amman khairat ki ka damu sai kin auresa,yanzu ai gashinan ya samu kyakkyawa irinsa,sun barki sai ka ce wata bolarsu".
wani malulu ne ya tsayamin aÆ™oÆ™on zuciyata Æ™walla ta sauka akan fuskata,wata me suna Hajara É—aya daga cikin Æ™awayen namu ta ce"Haba Safiya ai bai kamata kice haka ba,shifa ubangiji babu ruwansa da mai kyau da kuma mara Æ™yau,idan Allah yasa ka auri miji mai kyau dole ne ya kula da kai,matuÆ™ar yana so ya gama lafiya".. . . . .âœðŸ¿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯â€â™€ï¸ðŸ‘ŽðŸ‘‡ðŸ‘‡*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_*Miss green ce*_🤙ðŸ¿
[23/09, 16:21] Miss GreenðŸ€: 43. . . . .44
. . .taɓe baki Safiya ta yi sannan ta ce"hmm ni dai duk da haka wallahi ina jiye mata zama da miji irin wannan,yawancinsu kansu kawai suka sani,babu ruwansu da mutum za kiga har wani ɗagawa matar kai suke wai su gasu masu kyau,ko kuma kiga ana miki layi agida na neman mijinki".
"To Safiya ko ma dai menene ta auresa,don haka daga baya kenan,Allah dai ya basu zaman lafiya".cewar Hajara.
Ni dai sunkuyar da kaina kawai na yi,sai hotuna ake a hakan ni kuwa hankalina sam baya kansu,na tafi duniyar tunanin halin da zan sinci kaina aciki,don yaya Bilal sam bai son haÉ—a inuwa É—aya dani.
Tunda akazo wajen ko kallon ƙurata Yaya Bilak baiyi ba,hankalinsa duka yana ga jidda wacce take wani yimin kallon tara saura ƙwata,ni dai Allah2 nake atashi daga wajen don duk jikina amatuƙar sanyaye ya ke.
Cen sai ga Hajiya kaka ta zo ansha gwaggwaro itama leshinta fari ne tas,ta yi sosai farinta na salin fulani da kuma kyaunta ya fito sosai,kai tsaye ɓangarena ta taho,ta kalleni sheƙeƙe sannan ta ce"yau naga ikon Allah ke saboda ba'a sonki sai suka matsa cen ke shine suka barmin ke anan?To yanzu zanji dalilin yin hakan?yadda waccen mara kunyar ta matsa sosai jikinsa kema haka zaki yi,yo in banda kalan dangi ai kece ma ƴar uwarsa amman shine zai wani matsa cen gefe,zanji abinda ya kawo wannan wariyar."
tana faÉ—ar hakan ta yi gaba abinta,ina janyo mayafinta don in hanata amman sai da taje,ta kusa dasu maryam ta wuce wacce ke zaune kusa da Yaya Aliyu sai zuba soyayya ake,ta wuce kusa dasu Yaya Salim da mero,su dai ba lallai ka gane basa son juna ba,don dukkansu sai hotuna ake gwanin sha'awa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.