Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 31 of 90
na kallesa na fara magana murya ta na rawa na riƘe hannuwansa na ce"Yaya aliyu don Allah ka yi haƘuri kaji?wallahi ban san me ya faru da rayuwata ba?ina cikin ruƊu sosai,akan abinda ya faru dan . . . . .saurin rufemin baki ya yi sannan ya ce"shhh kada in ƙara jin kin yi magana,abu ɗaya zaki yi ki faranta min?shine kada in ƙara ganinki acikin damuwa sam,ki manta komai kamar ma ba'ayi ba kinji?".ɗaga masa kai na yi ina ɗan murmushi ya cigaba da bani abincin sai da na cinyesa tsaf daman na ɗakko uwar yunwa,tun jiya rabona da abinci.
maimakon ya ƙeleni ya tafi,sai ya samu waje ya zauna ya dinga bani labari har da na abin dariya,sai gani ina dariya kamar bani ba,daman hakan ya ke buƙata ya tashi ya fita har fita kuma sai ya dawo ya sa ke zama ya ɗauki wayata da ke gefena,ya buɗe ta ya shiga playstore ya buɗemin manhajar arewabook,ya yi murmushi ya ce"yauwa kinga wannan manhajar ina son ki kasance da ita a kullum ammanfa garin karatu kada ki dinga zama ba sallah ko rashin tsafta,duk da dai nasan ƙanwar ta wa aƙwai tsafta."ya faɗi hakan yana murmushi,ya sanya min data har ta wata ɗaya sannan ya bani wayar ya fita.
Yana fita na danna number mamana na kirata bugu ɗaya ta ɗaga,na fashe mata da kuka, sosai ta hau yimin faɗa da nasiha sosai nasiharta ta ratsani na bata haƙuri akan bazan kuma ba,ta bawa mamansu waya wato kakarmu sosai ta yi min nasiha itama tare da ƙwantar min da hankali,sannan ta yi min alƙawarin suna nan zuwa idan matar Aliyu ta haihu,sosai na yi farin ciki don ayadda cikin anty khadija ya ke yau ko gobe ma za ta iya haihu don cikin ya yi girma sosai kamar cikin ƴan biyu.
*****
Tun safe da abin ya faru hajiya kaka baki ɗaya taƙi sakin jikinta,duk wanda ya shigo sai ya ganta ta rafka uban tagumi,tana zaune yanzun ma mero na ta takalarta faɗa amman taƙi koda kula ta,koda aka kawo abinci ma mero ta takurawa kaka wai sai ta ci,amman taƙi ce tun abincin safe ne acikinta,tunanin halinda khairat kawai take ciki take,anya kuwa ba wani abu aka yi wa yarinyar nan ba?i'ta dai ta yarda da khairat yadda ta haƙiƙa ba ta tunanin za ta aika ta irin wannsn ta'asar.
Sallama har sau uku ƴaƴan hajiya kaka sukayi amman bata ma san sunayi ba,Baba usman da Baba auwalu,suma duk sunji abinda ya faru shiyasa suka shigo sashen mahaifiyar tasu don su ƙara jin komai,don dai su har ga Allah basu yarda da abinda aka faɗa ba,don kaf yaran gidannan ta fisu nutsuwa yadda ya kamata,ba tada surutu ko wata fitina ko kuma rawar kai,don haka dole ayi mamakin hakan.
Azabure hajiya kaka ta ɗago tana kallonsu don ta tsorata da shigowarsu,ta tsuke fuska ta ce"ko kuma lafiyarku kuka shigomin ɗaki babu sallama".da faɗanta take musu magana,alamar tana cikin tsananin damuwa da kuma ɓacin rai.
Ganin haka yasa Baba usman ya fara magana don duk ya fisu sanin kan hajiya kaka ya ce"hmm umma daman hankalinmu ne wallahi duk a tashe,da wata magana da mukaji mara daɗ?shine mukazo muji gaskiyar lamari"?.ya faɗi hakan kansa yana ƙasa don yasan halin mahaifiyarsu maganar da kai ka ke tunaninba komai ba ce to awajenta komai ce.
Ai kuwa sai ta ce"yau naji ikon Allah?to su guntsi fesin matan na ku da suka faɗa muku basu gaya muku komai ba?sai ni kuka zo kuka tsare kuke son in gaya muku?to bari in gaya muku, khairat dai ban yarda da abinda ya faru da ita ba,wata ƙulalliyar aka ƙulla mata don haka yanzu inason ku tashi kuje ku samu munfukan matan na ku,ku ce inji ni na ce"sharri aka yi mata kunji"?.
dukkansu sunkuyar da kawunansu suka yi,suna son ƙwantar mata da hankali i'ta kuma taƙi yarda da hakan don sun san da ƙer idan baza ta yi rashin lafiya ba,don yadda take son khairat akaf cikin jikokinta,wai don khairat ɗin sunanta taci.
Babu yadda suka iya haka suka fice don taƙi basu damar magana,hankalin hajiya kaka bai ƙara tashi ba sai da ta aiki mero kai mata abincin dare aka ce bata nan,anan ne hankalinta ya tashi sosai ta tafi ɓangarensu khairat ai kuwa taci karo da mama iklima tana jin abinda hajiya kaka take faɗa sai kuwa ta ce"hmm ni fa lamarin yarinyar nan mamaki ya ke bani,yarinya sai kace shaiɗan".
azafafe hajiya kaka ta juyo ta ce"akanki wallahi idan shaiÉ—anun yara ne kina nan dasu,amnan wallahi ba akan khairat ba,ke ni fa wallahi ban ma yard daku ba?yadda kuka tsani yarinyar nan zaku iya yi mata komai don daman ba sonta ku ke ba?amman babu komai Allah yana tare da i'ta,don shi Allah ba azzalumin bawansa bane.
[04/09, 18:40] Ummu Maher(Miss Green): Sosai mama iklima ta tsorata sa jin hakan sai dai idan hajiya kaka tasan wata bata wata ba,za tayi maganin shegen akun bakinta.
***
"Hajiya daman fa ke ca ki ke son wannan yarinyar amman ni daman cen na tsane ta wallahi,tsana mafi muni arayuwata,yanzu ai gashinan ta fito da halinta afili,sai ku gane halinta a'i".
Ce war Bilal wanda ya ke danna computer ɗinsa,hajiya Ruƙayya ta yi mamako sosai sai dai ɗan adam ba abin yarda bane musamman ma yaran yanzu,sai dai kawai addu'ah.
Wasa-wasa sai ga hajiya kaka ta fara ciwo don ko iya magana ma bata yi,sosai abin ya taɓa ƴaƴanta sunyi kuka har sun gaji kuma kullum magani ake amman shiru.
Yaya Aliyu da kansa yazo ya samu Babanmu ya faɗa masa ina wajensa,amman buɗar bakinsa sai ce wa ya yi"ni fa na cire ta daga cikin ƴaƴana idan taso ma ta shiga uwa duniya wannan bai shafeni ba,tunda haka ta zaɓa".sosai maganat ta daki zuciyar yaya Aliyu amman ya daure kawai,don mahaifi ya wuce gaban wasa.
Yaya Aliyu san bai gaya min ciwon hajiya kaka ba,sai abakin Rashida naji wacce ks kawomin ziyara akai-akai,ita ma ta yi baƙin ciki,ta yi kuka abisa ƙazafin da aka yi min a kullum bani haƙuri take don haka yanzu damuwata ƙadance akan ta da,yaya salim ma yana yawan zuwa,maher ƙanina da ke skull shima ya dawo yaji duk abinda aka yi min,kai tsaye ya ce ƙarya ne sharri ne,kuma asannu sai ya tona musu asiri.
Abinda ya ƙara saka rayuwata acikin garari bai wuce kai kuɗin yaya Bilal da saka ranarsa da jidda da aka yi ba,naci kuka har na godewa Allah,wato ni tawa ƙaddarar kenan?kamar wadda ba tada sa'a a rayuwarta?haka dai na dinga sambatuna ni kaɗai a ɗaki,daman idan na gama aiki na sai in shiga ɗaki in ɗakko wayata in ta karatu a arewabook don ina jin daɗin manhajar anan naci karo da wani littafi wanda miss green ta rubuta silar fyaɗe sosai littafin ya ɗaukemin hankali don kusan abinda ya faru dani shine ya faru da yarinyar cikin littafin,anyi mata fyaɗe amman bata san waye ba?anan naji hankalina ya daɗa ƙwanciya don yarinyar cikin book ɗin ta yi haƙuri sosai ƙarshe kuma komai ya zama labari.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.