Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 8 of 90

Hajiya kaka ita da mijinta Æ´an asalin jihar baushi ne fulanin usul,amman mahaifiyar Hajiya kaka Æ´ar zaria ce babanta ne É—an Bauchi.

Mijin Hajiya Kaka sojane tun zamansu a bauchi sukayi sa,amman ana yi musu transfer sosai daga gari gari,har Allah ya kasu garin kano suka fara zama a gidan haya daga baya ya yi na sa,amman zaman kano ɗin ya fi yi musu daɗi,don unguwar da suke unguwa ce mai ƙƴau unguwar jan bulo,Allah ya azurta su aƙwai filaye sosai a kusa dashi ya dinga siya yana ajjewa har Allah yasa ya siya filaye a kusa dasu sunfi 15,kuma a waje ɗaya suke kusa da gidansa suna zaune a kano ƙwatsam aiki ya mayar dasu a kaduna unguwar malali.amman suna zuwa kano akai akai.

Hajiya kaka tafi son zaman kano don haka ya barta anan ya ɗakki mata ƙanwarta suke zama tare,ƴaƴansu sun fara girma yanzu don haka ma bata fiya zuwa kaduna ɗin ba.

WaÉ—annan filaye da ya siya ya siyawa yaransa ne,ko kafin yabar duniya Æ´aÆ´ansa sha 11,sanda ya mutu bata ma san tana da ciki ba sai daga baya ta haifi autarta Aisha.

Wannan shine taƙaitaccen tarihin rayuwar Hajiya kaka.
*Washe gari*

babu wacce bata shirya a cikin mu ba,saboda ayau za a mayar damu boarding daman kusan duk ƴan matan gidan kusan mu goma duk boarding muke kuma muna a shekarar ƙarshe yanzu.

Duk jikina a sanyaye ya ke bayan na haɗa kayana na nufi sashen hajiya kaka,tana ganina ta hau kuka tana ce wa"Allah sarki jikata bana son rabuwa da ke wallahi,ke kaɗai ce a cikin jikokina baƙya yimin rashin kunya,ABIN CIKIN ƘWAI ya fi ƙwan daɗi haƙiƙa Allah ya bani jikar da nake alfahari da ita,sai ta rungumeni tana kuka na riƙo hannunta muka fito inda motar da za ta ɗaukemu take,motar gidanmu ce wacce daman an ajjeta ne don kai yara skull.

Hararar hajiya kaka suka fara yi,Nadiya da Samira Karaf a don kaka ta ce"to amman dai ba ni kuke harara ba ko?fulanin daji da sadakar yalla kukewa amman ni ba ni ba.Nadiya ta ce"wai ke kaka waye ma ya kalle ballanta na ma a harareki?kema da wani idon har kika san ana kallonki idan baki kallemu ba"?.

"shut up"!
yaya abeed ya ce wanda muke uba É—aya dashi kuma yayan nadiya, sannan ya cigaba da ce wa"wallahi ban san rashin kunyarki har ta yi tsamari haka ba,ki dinga iya bakinki idn ba haka ba kuma jikinki zaiyi tsami."

"a'ah ɗan nan da a uman take da bata isa ta yimin haka ba,da na haƊa ta da askarawa sunci ubanta malik".Dariya aka sheƙe da ita don abu kaɗan sai kaji ta ce da a uman kake da baka isa kayi mata abu kaza ba,kawai don ta yi zaman cen shikkenan.Ko da muka shiga motar sai da aka so ayi faɗa don su iman da nadiya waje ɗaya suke zama Rashida ta zauna kusa dasu don haka sukace sai ta tashi, yaya abeed ya ce"wallahi duk shegen da ya yi min rigima zan saukesa ne a duk inda naga dama don haka kada kowa ya dameni,ku baƘwa ko yi da ƴar uwarku khairat tana zaune baka jin bakinta amman ku sam baku da nutsuwa.
Ai fa wannan maganar da yaya abeed ya faɗa sosai abin ya bawa su Nadiya haushi,suke ta hararata ni kuwa ban ma san suna yi ba,Rashida ce taso biye musu amman na hanata don suna sane suke hararata don sun san halin Rashida ba tada haƙuri kuma ba za ta bari a zageni ko aci mutunci na ba.

Tunda daga lokacin babu wanda ya ƙara magana,ni Rashida,iman,nadiya,samira,unaisa,khalisat,intisar,raudat,Amina.

Duk babu wanda ya ƙara ce wa kanzil don sun san halin yaya Abeed bai da mutunci sun sansa kamar wutar cikinsu.
Muna zuwa makaranta kowa ya yi hanyar ɓangarensu tunda muka koma skull hankalina ya koma kan karatu wani lokacin Rashida har tsokana ta take wai yanzu na dain tunanin yaya Bilal hankalina ya koma kan karatu,sai dai kawai inyi dariya don na san son yaya Bilal a zuciyata ya ke bazai taɓa gogewa ba har abadan.

*Miss green ce*

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_

Guda É—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huÉ—u N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
[23/09, 16:15] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_

📃Littafi na 1

By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*

*GAWURTATTU 5*
---------------------

masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.

*SIRRINMU*

Mu kasance masu tsarkakkiyar zuciya,kada mu dinga hassada ko baƘin ciki.

9🟨10

. .. ."Rashida gaskiya irin wannan zaman da mukeyi a tsakaninmu dasu Nadiya bai kamata ba,ko da ace ma bamu san juna ba ai ya kamata ko gaisuwa ta dinga haÉ—amu?".

"Hmm Khairat kenan ni ina mamakin hali irin na ki wallahi waɗannan mutanen fa babu abinda suka sani illa su zageki su baƙanta miki,to me ye amfanin zuwa wajensu?ranki ne kawai zai ta ɓaci a banza wallahi,amman ni bazan hanaki zuwa wajen ƴan uwanki ba,amman ni dai ba zanje ba idan kinga ke zakije ga ki gasu amman ni dai La-La-La ina da abinyi ne ni dai."tana faɗar hakan ta yi shigewarta banɗakin da ke jikin ɗakin ƙwananmu.wata ƙawarmu mai suna Hasiya tana zaune tana karatun wani novels ta juyo tana kallona ta ce"gaskiya ne abinda Rashida ta faɗa miki duk da ni ba ƴar'uwarku ba ce amman zan faɗa miki gaskiya ku fita daga harkarsu nadiya dasu iman saboda wallahi yanzu kaf ma skull ɗinnan babu wanda bai san grp ɗinsu ba,yanzu haka suna da grp mai zaman kansa a makarantar nan na ƴan lesbian so be careful da waɗannan duk da su Nadiya babanku ɗaya amman idan zan baki shawara idan har kun koma gida ki sanarwa da mahaifinku duk abinda ya ke faruwa idan da hali ma ayi musu aure kawai shine zai kawo ƙarshen komai".ta faɗi hakan tana kallona.

Tabbas wannan abinda Hasiya ta faɗa min ya girgiza tunani na sosai,an daɗe ana faɗamin abinda su Nadiya suke a skull sam basa karatu yanzu,daman tunda muka shiga makaranta suka haɗu da ƙawaye suka hure musu kunne shikkenan suka ƙara tsanata da hantara ta tunda ni dai a kullum gaskiya na ke gaya musu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.