Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 37 of 90

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

Instagram links👇

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/

Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*A C Ƙ*

MISS GREEN

*39⬜40*

. . . .ban gama mamakin ba sai da ya matso har kusa dani sannan na buɗe baki na a hankali na ce"daman kai ne"?.Murmushi ya yi har fararan haƙoransa suka buɗe sannan ya ce"Eh ni ne duk da ni ban taɓa ganinki ba?Amman nasan ke ko da a tv kin taɓa ganina,zan gabatar miki da kai na duk da nasan kin san sunan nawa,Ahmad A.Abubakar,commisioner of police bani da aure ayanxu amman ina da niyyar yi ƙwanan nan tunda dai yanzu na samu wadda na keso".

sunkuyar da kaina ƙasa na yi,kaf duniya ina tunanin babu macen da za tace bata son Ahmad don babu abinda baagi dashi,ƙyau,kuɗi,addini,ilimi,tarbiyya,kamala,sanin ya kamata,kai har dama waɗansu abubuwan.

Ganin na yi shiru sai ya ce"a gaskiya ni ada na fitar da yin aure arayuwata saboda bazan ɓoye miki ba na taɓa yin aure acen baya sai dai gaskiya ko kusa banji daɗin auren ba,saboda banyi dacen mata ba,zanso inji sunanki baiwar Allah don naga kamar wayo ki ke son yimin ina ta zuba ba tare da kin faɗa min sunanki ba?".

a hankali na ce"sunana Rahma amman ana kirana da khairat".

"Wow nice name,sunan mahaifiyata ne da ke gaskiya naji daɗi,ammsn ina son ki faɗamin kina da ra'ayina ko kuwa?Don gaskiya ni arayuwata bana magana biyu,kawai idan har ina son abu to babu tabbas shi ɗin na keso babu mai canjamin tsari na,don Allah khairat inason ki faɗamin gaskiyarki akaina?Ni dai har ga Allah kin tafi dani baki ɗaya,na sadaukar da aikina na awa kusan huɗu saboda ke,wanda atarihi na ban taɓa yin hakan ba".

Sunkuyar da kaina na yi don a gaskiya bazan ɓoye masa komai ba,don ayanzu an bada ni kuma ma gaskiya ko da ba'a bada ni ba,maƙalalliyar zuciyar nan ta wa tana wajen Yaya Bilal,duk da babu abinda Yaya Bilal zai nunawa Ahmad ɗin sai dai kawai fari,amman banda wannan babu abinda zai nuna masa.

A hankali na ce"kayi haƙuri C/M ayanzu haka har an saka ranar aure na nan da sati uku masu zuwa za'ayi bikina,amman ka yi haƙuri gaskiyar daka baƙata ita na faɗa maka".na faɗi hakan ina sunkuyar da kaina ƙasa.

Wani mugun jiri yaji yana ɗibarsa duk da jikinsa yadda ya ke kamar rainon ƴan rastling amman sai da ya kusa faɗuwa,ya buɗe kyawawan idaniyarsa sannan ya ce"khairat haƙiƙa kin burgeni da faɗamin gaskiya da ki ka yi amman ko babu komai inason ƙulla zumunci da gidanku,idan an tashi ɗaurin aurenki zanzo,ga wayata sakamin number ɗinki".?Ya faɗi hakan yana jin adadin zafin zuciyarsa na ƙaruwa,ciwon kansa nasan tashi masa ƴan awanni da haɗuwa da yarinya yaji kamar zai mutu idan bai aure taba,gaskiya wannan yarinyar tana da sa'a sosai don matan da suka amsa sunansu mata masu ji da kuɗi da komai,sunsha zuwa wajensa da furucin soyayya amman ko kallon ƙurarsu baiyi yanzu gashi kan yarinya ƙarama wacce a ƙiyasinsa bata fi 17 zuwa 18 ba.

Samun kaina na yi da murmushi na amsa na saka masa na bashi,ya yi murmushi sai naga kawai hawaye suna zubo masa ya ce"khairat Allah yasa albarka acikin wannan auren na ki,idan babu Albarka Allah ya wargazar ko Æ´ata Inaas ta samu uwa tagari kamarki".

BuÉ—e idanuwana na yi sanna na ce"au daman kana da Æ´a ne?".Murmushi ya yi sannsn ya ce"ina da Æ´a shekararta biyar amman yanzu mun rabu da mamanta tana hannun mahaifiyata,kullum burinta in samo mata momi amman na kasa hakan tunda bab haÉ—u da wacce na keso ba,sai yanzu Allah ya yi gashi kuma wani mai sa'ar ya rigani,to shikkenan ni zan tafi khairat saduwar Alkhairi".

Tafiyarsa ma kaÉ—ai abin kallo ce ina tsaye naga sun tsaya akusa dani ya ce"khairat idan babu damuwa shigo mu sauke ki agida?wannan titin babu kowa kuma bai kamata ki tsaya ke kaÉ—ai ba,alhalin kuma kina amatsayin mace,macen ma mai daraja".

Samun kaina na yi da yarda dashi na shiga muka tafi,har mukaje bai ƙara ce wa komai ba nima kuma bance ƙala ba,da zan fita har na saka ƙafufuwana awaje ya ce"khairat"!.

Juyowa na yi cikin mamakin jin kirana da ya yi,na juya ina kallonsa na sunkuyar da kaina don bazan iya kallon cikin idaniyars ba,don yana da ƙwarjini sosai.

Ya ce"khairat idan na yi miki ƙyauta zaki amsa"?.Ya kunnomin wannan tambayar na ce"zan amsa C/M tunda daga hannun mutum mai alfarma ta fito kuma mai mutunta mutane".

Ɗan murmushin jin daɗi ya yi sannan ya ɗakko wani envelope ya miƙomin,amsa na yi cikin nutsuwa sannan na ce"na gode!ka gaida min da Inaas".

Sosai naga murmushi ya bayyana akan fuskarsa saboda aduniya yana son mai son nasa,musamman ma kuma Inaas Æ´arsa ya ce"naji daÉ—i khairat insha Allah zan kai gaisuwarki wajen Inaas".

Nima murmushin na yi sannan na ce"to na gode sai anjima".ina faÉ—ar hakan na juya zan tafi gida sai naga Yaya Aliyu da Anty khadija zasu fita.

Tsoro ya kamani don nasan sun riga da sun ga C.M don haka na sunkuyar da kaina,ganin hakan yasa M.C fitowa suka gaisa da Yaya Aliyu sannan ni kuma na yi cikin gida kunya duk ta isheni.

ina shiga Anty Khadija ta shigo ita ma sai naga tana wani washe min baki ta biyo ni har ɗakina lokacin ina cire kaya da ɗaurin ƙirji ajikina, sai kuwa ta ce"am daman khairat tambayarki zanyi"?.Ɗan ɗaure fuska na yi kaɗan don nasan tambayar daza ta yi kenan na ce"uhm ina jin ki"?.

Sai ta nemi waje ta zauna ta ce"yauwa me ye kuma haÉ—inki da Commisioner of police"?.Tambayar ce tazo min abaza ta sai na ce"babu komai sai zumunci".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.