Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 86 of 90
sosai take kallona cikin mamaki,wato khairat micijin sari ka noƘe ce,wato duk tsanar da take ce wa ta yiwa yaya Bilal ashe duk Ƙarya ne?to idan ba Ƙarya ba me yasa ta damu don ba shida lafiya?.
ganin khairat Ɗin ta dage ne yasa ta ce"to khairat muje".ta Ɗakko min jaririyar muka fito,ina dafe bango ina tafiya jirin yana Ɗiba na amman a haka har muka isa Ɗakin,duk naji jikina ya Ƙara yin sanyi sosai.
da mutane sosai a Ɗakin duk suka zubomin ido mamaki Ƙwance kan fuskarsu har da shahid a Ɗakin,da ammi mahaifiyarsa da kuma mama har dasu yaya Aliyu,ga hajiya kaka a gefe su Rashida,sai maryam wacce bata fi wata biyu da haihuwa ba,ta haifi Ɗanta na miji,me sunan yaya Bilal.
saurin dafe jikin bango na yi ina waro ido waje,ganin yaya Bilal Ƙwance kamar matacce an saka mishi abin shan numfashi ya yi wani irin fari fauu ga kuma ramar da ya yi,an saka masa kaya ruwan skye blue irin na marasa lafiya.
wani irin kuka na fashe dashi tuni na tsugunna Ƙasa da rarrafe na Ƙarasa bakin gadon,saboda Ƙafufuwa baza su iya kaini wajensa ba,na ce"Yaya Bilal anya kuwa kai ne?me ya faru da kai?wani irin ciwo ne wannan?".duk ni kaƊai ke sambatu na kamar mahaukaciya sabon kamu,babu wanda ya cemin Ƙala,sai ma harara da wasu ke bina dashi.
ban ma san na riƘe hannunsa ba sai yanzu na Ƙara ƘamƘame hannunsa na ce"don Allah yaya Bilal ka tashi,idan ka mutu nima tabbas zan iya mutuwa,da kai na saba yaya Bilal tun ina Ƙarama ta ka nuna min so,ka nunamin Ƙauna,haƘiƘa banyi maka adalci ba".
Da sauri shahid ya tashi ya fita waje,duk zuciyarsa babu daƊi wani irin kishi yaji ya turniƘe masa Ƙirjinsa,ya zauna kan wani benci ya saki kuka kamar Ƙaramin yaro,mutane sai wuce wa suke suna kallonsa yana son khairat da duka zuciyarsa yana jin ciwon rabuwa da ita,amman ya zama dole ya yi hakan don ayanzu ya gano ce wa ba Ƙaramin so khairat ke yi wa tsohon mijinta ba.
Yana zama ammi ta biyo bayansa don ganin halin da ÆŠanta ke ciki,itama duk zuciyarta babu daÆŠi ko kaÆŠan,ta ce"shahid ka yi haƘuri ka ka baiwa Allah lamarinsa,sam banji daÆŠin hukuncin daka ÆŠauka akan aurenka da khairat ba,ka sani shi Allah yana tsara lamarinsa yadda yaso,khairat suruka ce ta gari a azamana da ita dana yi,bata taÆa yimin wani abu da raina zai Æaci ba,kullum ƘoƘarinta shine ya za'ayi ta kyautatamin,don haka ni sam banji daÆŠin wannan abinda ka aikata ba."
Murmushi shahid ya yi wanda masu iya magana suka ce yafi kuka ciwo ya ce"Ammi ki daina magana ki yi shiru,saboda ni kaÆŠai nasan halin da nake ciki xuciyata tana yimin zafi sosai akan wannan sakin da na yi wa khairat,wanda ita kanta bata san na yi mata ba,ammi jiya fa dana shiga wannan bawan Allahn kiran sunan khairat kawai ya ke,sannan ciwon zuciya ya kamasa saboda Ƙaunar khairat da ya ke yi,Ammi ina da imani ina kuma da tausayi bazanso nima ayimin hakan ba,ni nasan nima zan iya shiga wannan halin akan Ƙaunar khairat,amman babu komai zan karÆi Ƙaddarata insha'Allah".
ya rungume mahaifiyarsa yana kuka me tsuma zuciyar me sauraro,shahid kiran sunan Allah kawai ya ke yi,halisa ta fito daga cikin Ɗakin da jaririyar a hannunta ta tsaya a tsaye tana kallon shahid wanda ke Ƙwance kan cinyar mahaifiyarsa yana kuka kamar Ƙaramin yaro.
sosai ya bata tausayi ta matso a hankali inda suke ta fara magana cikin harshen turanci ta ce"shahid ka yi haƘuri ka fauwalawa Allah komai,amman banji daƊin sakin da ka yiwa matarka khairat ba,don ba'a wasa da aure".
a hankali shahid ya tashi daga kan cinyar ammi ya ƙarasa wajen halisa ya amshi ƴarsa.wacce ke ta baccinta hankali ƙwance.me kama dashi sosai ya zauna yana kallon ƴarsa cike da so da ƙaunarta.sai yanzu ma ya tuno bai yi mata huɗu ba ba.wasu hawaye suka zubo masa ya share su tuno da halin da yarinyar zata kasance na rashin mahaifiya akusa da ita.shi da yarasa mahaifinsa ma ya damu sosai balle kuma mahaifiya.gashi nigeria ba wajen zaman bane dole zai koma masar.ko england tunda dai shi ɗan asalin ƙasar england ɗin ne.
yana gama raÉ—a mata sunan Ammi ta amshe ta.tana manna mata kiss a goshinta na jin daÉ—in ganin jikarta Æ´ar shahid gudan jininta.lallai wannan yarinya zata sha gata.ya ce"Ammi na raÉ—a mata suna da Rahma(khairat)taci sunan mahaifiyarta.
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯â€â™€ï¸ðŸ‘ŽðŸ‘‡ðŸ‘‡*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_*Miss green ce*_🤙ðŸ¿
1003. . . . . . .1004
---------Ammi ta ce"Allah ubangiji ya raya mana ita.amman ni dai zuciyata bata yimin daÉ—i wallahi,shahid ba kai kaÉ—ai ka yi rashin khairat ba har ni,ni kaÉ—ai nasan irin kyautatawar da take yimin.Allah ya tashi kafaÉ—ar baban yaran na ta".dukkansu suka amsa da amin.
Hajiya kaka ta ce"khairat don Allah ki fita a É—akin nan ina ce wa kece kika tayar masa da ciwon nasa ko?tsabar rashin tausayi da kuma imani haka ki ka rufe idonki ki ka ce kin tsanesa.amman shine yanzu zaki wani dawo nan?maza ki tashi ki fita cen bama nemanki".
Sosai na fashe da kuka har da majina na ce"haƙiƙa hajiya kaka ban yi wa kaina adalci ba.na cuci kaina da nunawa yaya Bilal tsana har haka.ko da me ya yimin bai cancanci inyi masa haka ba.don Allah ina neman yafiyarku ku yafe min".na faɗi hakan ina kuka sosai.
Likita yana shigowa ya bada umarnin kowa ya fita zai duba Yaya Bilal,haka aka yi kuwa kowa ya fita sai ni kaÉ—ai.har hajiya kaka ta fita sai kuma ta dawo ta ce"to ke uwar Æ´an marasa jin magana komawa kika yi kika zauna kamar mijinki"?.jin hajiya kaka ta faÉ—i hakan tuni na tashi gabana yana faÉ—uwa tunowa da shahid.don nasan duk wannan abinda na yi yasan komai,na tashi na fita ina kallon yaya Bilal.
Ina fitowa na fara bin bango ina tafiya ina cije leɓe,duk jikina ya yi mugun yin tsami,ga haihuwar dana yi wacce ta bani wahala sosai.
Da sauri shahid ya taso ganin ina shirin faÉ—uwa,kome ya tuna sai ya yi sauri ya yu baya zuciyarsa sam babu daÉ—i ko kaÉ—an.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.