Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 61 of 90

•5)- Shan madara kofi daya kafin a kwanta bacci a kullum yana taimakawa fata sosai.

•6)- A kasance ana shafa man kadanya a jiki bayan anyi wanka da daddare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gabadaya da man kadanya domin samun fata mai laushi mai sheki.

 

7)- A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sannan a shafa a fuska ko fata na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan dumi.

8)- Lemun tsami da sukari na taimakawa wajen fitar da fatar dake da gautsi a jiki sannan yana sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matsa ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon mintuna uku sannan a wanke

9)- Ayi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo. Kada a maka duka a jiki yawan amfani da ababe dayawa a fata yana haifar da kuraje a fata.

*By*
*dr mata ummu maher(miss green)*
*don neman ƙarin bayani*
07068606171

*MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

Instagram links👇

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/

Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

MISS
GREEN CE
[23/09, 16:29] Miss Green🍀: *🏮ABIN CIKIN ƘWAI🏮*

littafi na 3

*by✍🏿*
Ummu maher(miss green)🍀

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

*Sirrinki👂🏻🌈*

Ƴar uwa ki kasance mai yawan yiwa mijinki da ƴaƴanki addu'ah da al'ummar musulmi baki ɗaya,don ita addu'ah makamar mumuni ce.
------------------------------

73. . . . . .74

. . . ."Hajiya zuciyata ciwo take min agame da abinda Khairat ta yi min,hajiya sai yanzu na tabbatar da abinda ki ke faÉ—amin a game da khairat,hajiya ki yafe min don Allah."ya faÉ—i hakan yana fashe wa da kuka sosai.

Hajiya Ruƙayya ta ce"Bilal kenan tunda har ta yi agidan ubanta agidanka ne baza ta yi ba?ai shiyasa na faɗa maka wannan yarinyar ba macen aure ba ce,amman saboda kai yaro ne shiyasa wannan kakar taka ta cuce ka,insha Allah sai Allah ya saka maka."ta faɗi hakan tana share mishi hawayen fuskarsa.

******

a hankali na farka na buÉ—e idanuwa na waÉ—anda suka yimin girma sosai,na fashe da kuka tuno abinda ya faru da sauri Rashida ta matso inda na ke,ta rungumeni itama tana kukan Yaya Aliyu yana tsaye yana kallonmu shima yana goge hawayen fuskarsa,na kallesu su duka ahmad ma yana wajen commisioner of police na ce"nasan bakunanku cike suke da tambaya ta ba'asin abinda ya faru?amman ni da Kai na zan faÆŠa muku duk abinda ya faru".

Su Dukansu suka zubomin idanuwa suna kallona,na share hawayen fuska ta na basu labarin duk abinda ya faru,dukkansu salati suka saka yaya Aliyu ya ce"tabbas Bilal zaiyi nadamar wannan Abinda ya yi miki khairat,ki yi haƘuri Ƙaddararki kenan".kuka na fashe dashi na ce"wallahi yaya Aliyu ayanzu na tsani Bilal tsana mafi muni arayuwata,koda ma ace bai sake ni ba toni tabbas xan saki kaina kuma babu tantama jidda ce ta haƊamin wannan sharrin,na barta da Allah shine zai sakamin".sai na fashe da wani irin matsanancin kuka me cin rai.

Rashida ta rungumeni tana kuka ta xe"ki daina kuka khairat insha Allah sai Allah ya saka miki."Ta faƊi hakan tana kuka,ahmad ya kalleni sosai tausayina duk ya cika zuciyarsa ya ce"Khairat nima dai haƘurin zan baki saboda duk wanda ya sanki yasan halinki don haka inason ki share hawayenki,insha Allah nan ba da daɗewa ba gaskiya za tayi halinta,don shi ramin ƙarya ƙurarre ne,ita kuma ƙarya fure take bata ƴaƴa".

Sosai suka dinga ƙwantarmin da hankali har naji zuciyata ta ɗan samu salama,sai da aka yimin ɗori a hannuna don na samu gocewar ƙashi.ban san yaya aka yiba yanzu so ya koma ƙi nidai na tsinci kaina da mugun ƙin yaya Bilal,ni gani nake duk abinda aka ce masa na yi ai shi me yin bincike ne ba kawai ya hau kai ya xauna ba.don haka insha Allsh zan nuna masa khairat ɗin daya sani adacen baya to ayanxu ba ita bace.zanyi kuma duk yadda zanyi wajen gano duk wanda ya yimin wannsn sharrin.

Yaya Aliyu yana ɓaremin ayaba ya ce"khairat tun acen baya munyi kuskure sanda abin nan ya faru kafin ki yi aure,har na barki ki ka zauna agidana ba tare da kin zauna agidanmu ba,saboda tsoron wani abu da zai biyo baya,kinga sai aga kamar bamu da gaskiya ne amman yanzu insha Allah gidanmu zaki je,don gidan ubanki ne,duk wanda zai yi miki gori ya yi miki,nidai na baki goyon bayan duk wanda ya yi miki kada ki barshi kema ki rama kinji"?.

ÆŠaga kaina na yi sannan na ce"gaskiya ne Yaya Aliyu awannan karon na saka tsoro araina da tunanin abinda mutane zasu iya faÉ—a akai na amman yanzu kome za suyi sai dai suyi amman agidan ubana zan zauna,babu kuma wani tsoron da zanyi tunda dai nasan abinda ake zargina akanshi sam ban aika tashi ba" .

Ahmad yana jinmu sai kuwa ya ce"khairat su mutane daman idan kace zakaji tsoron su to sunfi son hakan,gwara ka dage ka amshi Æ´ancinka wanda ka rasa awajensu.ki nuna musu cewa kefa yanzu an daina cutarki ki bari,za kiga kowa yana jin tsoron haÉ—a hanya da ke."

Sosai naji daɗin shawarar daya bani,Rashida ma ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce"haka ne khairat duk abinda suka gaya miki,amman gaskiya Yaya Bilal bai kyautawa kansa ba,amman ni nasan aƙwai ranar nadama".murmushi kawai na yi sai naji zuciyata duk ta wanke.

Na ce"insha Allah zanyi ta bincike har sai na gano duk wanda ya shiryamin wannan ƙulalliyar".murmushi Ahmad ya yi sannan ya ce"khairat kenan ki barsu da Allag yafi ki rama da kanki don ramawar zai zamo kamar kin raina hukuncin Allah ne,abinda na keso da ke shine ki nutsu sosai ki dage da addu'ah babu dare babu rana,wallahi khairat na baki wasu ƴan ƙwanaki ƙalilan sai kin bani labarin abinda zai faru,don haka ki manta da wannan abin."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.