Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 48 of 90
****
Ƙarar wayar jidda ne ya karaɗe wajen,tana sama kan bene tana wanka,Bilal na kusa da wayar ya shiga kiranta da honey!honey!!amman jidda bata ma san yana yi ba,ya ɗaga wayar don ya bada uzurin mai wayar shiru yaji anyi don haka ya ajje wayar ya cigaba da aikinsa cikin system ɗinsa.
Tana sakkowa Bilal ke faɗa mata an kira ta,ai da gudu ta ƙaraso wajen tana ce wa"wa. .wa. .waye?".
KafaÉ—a Bilal ya É—aga alamar shima bai san waye ba?.ta duba number gabanta ya bada wani irin rass rass,ta daure ta tashi tana wayan cewa ta ce"au bari in hau sama na manta nan wajen sam babu network,shiyasa idan zanyi waya ta nake hawa sama".ta faÉ—i hakan tana yin gaba zuciyarta fal tsoro amman ta godewa Allah da Bilal É—in bai gai ne waye ba.
Tana hawa saman ta shiga É—akinta ta kulle harda saka key,sannan ta samu bakin gadonta ta zauna,ta kira number hannunta na rawa.
"Barkanki da dare mrs Bilal Admiral B".
Gaban jidda ne ya faɗi sannan ta ce"ranka ya daɗe Oga dafatan kana lafiya?wallahi ɗazu wayar na bari a ƙasa na shiga wanka ashe Bilal ya ɗauki wayar?".ta faɗi hakan tana jin bugawar zuciyarta na ƙara ƙaruwa.
Sosai Alhaji Damas ke dariya sannan ya ce"Banyi magana ba mrs Bilal,idan da na yi magana yau nasan gidanku Boom wuta zata tashi kinga mutum ya yi asarar dukkanin wannan aikin dana sakaki,to kinga yaya kuma zan ɓata aiki na,i zuwa yanzu kin samu wani rahoto ne?".
ya jeho mata wannan tambayar?jikinta na rawa ta ce"eh ranka shi daɗe yanzu haka na samu ka jiraye zuwa na gobe insha Allah,zan masa ƙaryar zuwa gida daga nan dai inzo".
Dariya sosai ya yi irin dariyar basawa,sosai jidda take jin tsoron dariyar Alhaji Damas,tana cikin wannan halin ne taji yana ce wa"yauwa kinji ina dariya ko?ba komai na kewa dariya ba sai yadda kika mayar da ƙwaƙwalwar kamar wata babyn roba,duk da basirarsa da kuma fikirarsa,shiyasa akace mace tafi shaiɗan iya annamimanci."
shiru jidda ta yi don ita lamarin Alhaji Damas yabar bata mamaki,don mutumin yasan kan rashin tausayi da kuma rashin sanin darajar É—an adam.
Suna gama wayar ta kashe wayar baki ɗaya,don haryanzu bata dawo nutsuwarta ba,anya kuwa ta yiwa Bilal adalci arayuwa?mutumin da ya taimaketa ya tsamota daga ƙangin rayuwar da take ciki?amman shine duk ta manta wannan kyakkyawan halarcin,yana sonta so na haƙiƙa,ta haɗa masa ƙarya amman kuma bai nuna mata komai ba,koda afuska ne kuwa. saboda Tsananin sonta da ya ke.
Wata zuciyar ta ce mata,haba jidda Yanzu akan ɗan wannan abinda ya yi miki ne har ki ke wani tunanin har wani halacci ya yi,Alhaji Damas daga haɗuwarku ta farko ya baki gida mau shegen kyau da kuma tsada.ya bata shi halak malak,sannan duk zuwan da zata yi da kuɗaɗe take zuwa dami guda,tuni account ɗinta ya zama popular saboda muguwar cikar da ya yi da kuɗaɗe,ko shi Bilal ɗin da yake wani ƙafafar ya taimaka mata tasan sarai Account ɗinsa babu rabin kuɗinta,koda aƙwai ma waɗannan ƴan gidan nasu ba bar masa shi zasuyi ba,saboda yadda ya ke taimakonsu sosai.
****
"mero!mero!!mero!!! Salim ne ya taƙar ƙare yana ta ƙwala mata kira,da sauri ta fito daga cikin ɗakinta da radionta akunne wacce Hajiya kaka ta saka ta siyo mata,wai ita baza ta iya zama ita kaɗai ba,ita kuma Hajiya kaka da taya ɓera ɓarna ta siyo ɗin,don ita da mero yadda kasan remote da tv haka suke.ita Hajiya kaka tv ita kuma Mero remote,don sai yadda mero ta yi da kaka ha suke zamansu,don ita hajiya kaka aƙwaita da ɗaurewa jikokinta gaba.
Tana zuwa ta tsaya tana kallonsa shima yana kallonta,ta wani ture baki gaba tare da turo ɗaurin ɗan ƙwalinta ma gaba na rashin kunya.
Sai kuwa ta ce"haba Yaya Salim nifa shiri na keji kazo ka tsaida ni,yanzu gashi nan har sun wuce ni".ta faÉ—i hakan kamar xa tayi kuka.
Kallon banza ya yi mata sannan ya ce"ah lallai mero rashin kunyarki ta ƙara bunƙasa sosai,yau satinki uku agidan nan amman kullum idan na dawo sai dai inje in siyo abinci?a matsayi na na mijinki? Me ki ke nufi da hakan?,ko kina nufin kullum sai na dawo da uwar gajiya ta sannan inje inyo miki take away ki buɗe wannan ƙaton tunbinki,ki cinye ke gaki uwarcin tsiya,take away ɗaya baya isarki saboda haɗamarki,amman idan wajen girkine sai ki maƙale hannu ki ƙwanta ke gaki uwar san jiki ko?to ki buɗe kunnuwanki sosai kiji,wallahi daga yau na daina siyo abinci,ga kayan abinci nan a store komai aƙwai ki duba abinda ki ke da buƙatar dafawa ki dafa amman wallahi ni na daina siyo wani abinci kinji ko?".
Yana faɗar hakan har ya yi nisa sai yaji mero na ce wa"oho dai ai naga ni ban iya girkin ba?idan kace inje wani hito in ɗakko kayan girki ni ta ina na sansu ma?ni koko kawai na iya damawa,don shi kaɗai hansai ta koyamin,kuma ni wannan ƙaton abin girkin na madafa wallahi ni dai ban iya kunnasa ba,kawai wataran inje ya babbake ni".
abin dariya abin takaici,wai bata iya girki ba?to a gaba zai sakata yana kallo idan bata iya girkin ba?wata shawara ce ta faɗo masa aransa don haka kawai ya fita daga gidan ba tare daya ƙara magana ba.
***
"Lafiyarki khairat bakya zuwa skull,É—azu wannan malamin naku ya kirani wai bakya zuwa,me yake faruwa ne agidan naku?"
Kasa ce wa yaya Aliyu komai na yi,don bana son tona asirin halin da na ke ciki.... .âœðŸ¿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯â€â™€ï¸ðŸ‘ŽðŸ‘‡ðŸ‘‡*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_*Miss green ce*_🤙ðŸ¿
[23/09, 16:23] Miss GreenðŸ€: *_🪺ABIN CIKIN ƘWAI🪺_*
📃LITTAFI NA 2
UMMU MAHER(MISS GREENðŸ€)
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
Matso kiji👂ðŸ»
Kada ki kasance mai yawan yiwa mijinki musu wallahi yin hakan yana dakushe ki a wajen mijinki don haka a kiyaye,ba da faÆŠa ko fushi miji ya ke saka ya soki ba,A'ah da rarrashi da kissa ake mallake miji.
-------------------------
53. . .54
. . ."haba khairat da ke fa nake magana kinyi shiru?".Yaya Aliyu ya faÉ—i hakan cikin fushi don shima baya son rainin hankali.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.