Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 42 of 90

Banɗaki na shiga na yi wanka na fito Hajiya kaka ta ce"buɗe cikin sif zakiga wata atamfa super ɗakko ta ki saka, jiya na amso miki ita,amman banda mero saboda ita na barta ta saka kayan lefanta saboda ita babu rashin mutunci aciki,amman Ruƙayya ji bi lefan da ta haɗo miki duk aƙwatin bai cika ba,ai wallahi baza ko saka ko ɗaya ba,ana gama bukin zan mayar mata tsiyarta,don itace matsiyaciya don ni dai ban gada ba,ɗinki kala goma na yi miki ki yi ta sakawa kina fita,kuɗi na ware sosai na bawa Rashida ta yi komai,sai da aka ɗinka sannan ta kawo min,yarinyar arziƙi wacce bata yo mugun hali irin na uwar taba.
Ni dai ina jin hajiya kaka bance komai ba,na shirya cikin atamfata blue da kuma ratsin brown ɗinkin riga da zanine amman ɗinkin ya yi ƙyau sosai,musanman ma dana saka kayan na yi ƙwalliyata simple na ɗaura ɗan ƙwali na akan ƙwantaccen gashina wanda yasha saloon sai tashin ƙamshi ya ke.

Rashida ta shigo tana dariyar tsokana ta ce"to Alƙawarin Allah ya cika an ɗaura auren Rahama da kuma Bilal".

Wani irin faɗuwar gaba naji,yanzu shikkenan an ɗaura aure na da Yaya Bilal?yanzu shikkenan na zama matarsa?mun zama abu ɗaya?tuni hawaye suka fara ƙwaranyo min kamar an buɗe bakin fanfo. . .✍🏿

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:21] Miss Green🍀: 45. . . . 46

Rashida ce ta share min hawayen ta juyo da fuska ta tana kallona sosai ta ce"Khairat wannan kukan da ki ke ya yi yawa,don Allah ki daina kinji"?.Ta faÉ—i hakan tana kallon cikin idanuwa na,a hankali na ce"to na daina sis Don Allah ki yafemin kinji".

Dariya ta yi sannan ta ce"a haba matar yaya ai bata laifi,yanzu dai tashi mu fita waje ana ta hotuna bakyanan,waccen rasai ɗin matar yayanki mero tana cen gindin camera ana ɗaukar hoto,abin dariya Yaya Salim yaƙi fitowa yana cen wajen abokansa,wai kunya ya keji kada araina sa don ya auri mero".

ta faÉ—i hakan tana jan hannuna,murmushi kawai na yi mukazo muka wuce ta kusa dasu Hajiya Kaka ta ce"yauwa Rashida fita da ita,don ni na gaji da zaman ta aÉ—akin nan".

"Cikin shagwaɓa na ce"au yanzu Hajiya kaka har kin gaji dani ko"?.murmushi ta yi sannsn ta ce"haba Me sunana yaya za'ayi in gaji dake?ai hakan ma bazai yiwu ba".

Hotuna sosai aka yi mana,mamana da Æ´an uwanta duk sunzo an É—aukemu hotuna,da yaya Salim da Yaya Aliyu da autanmu maher duk an É—aukemu hoto gwanin sha'awa.
Duk abinda muke yi a idon su Hajiya Iklima,ta ciji laɓenta har sai da taga jini ya fito,Anty kishiyarta ta zaro idanuwa waje ta ce"ikon Allah Iklima jini fa na ke gani abakinki"?.ta faɗi hakan da mamaki.

"Hmm Za kiga abinda ma yafi jini abakina,matuƙar ina ganin matar nan da ƴaƴanta sai inji kamar zan mutu saboda baƙin ciki,a duk duniya babu halittar dana tsana irin Zulaiha da kuma ƴaƴanta musamman waccen baƙar ƴartata,na tsanesu tsana mafi muni arayuwata".

"Ai ba ke kaɗai ki ka tsanesu ba,nima na tsanesu wallahi,duk wani iyaye na Zulaiha yanzu ai ya zama tarihi,wai ita wadda miji keso ta dinga wani iyawa,yanzu ina iyawartata take?kinga kuwa ai ko yanzu ɗan koli yaci riba wallahi".Anty ta faɗi hakan tana hararar mama wacce ma bata san wainar da ake toyawa ba,da Rana aka kira masu kiɗan ƙwarya sosai suka ƙware wajen sana'arsu,aka sakamu a tsakiya nida mero,ai tuni amarya mero ta ware ta zage tana ta muskuta mazaunai kamar ba amarya ba,ina ta taɓa ta wai kada ta yi amman ina rawar take ta yi,ko ajikinta.

Hajiya kaka sai liƙi take ta mana,musamnan ma ni,atarihi babu wani bikinda Hajiya kaka ta taɓa kashe kuɗi irin bikina,ta kashe kuɗi ba na wasa ba,har tausayi ta bani.

Ana cikin wannan kiÉ—anne na zagaye a hankali na fita na koma É—akin Hajiya kaka na dinga cin kukana idanuwa na sukayi jawur kamar gauta.

A hankali mama ta ƙaraso inda na ke,ta ɗago fuskata sosai ta sharemin hawaye na sannan ta ce"khairat aƙwai abubuwa da yawa da ya kamata in faɗa miki amatsayi na,na mahaifiyarki duk wata uwa tagari tana yi wa ƴarta da nasiha da tabi mijinta,ta yi masa biyayya,yi na yi bari na bari sannan aƙwai wasu abubuwan da ya kamata in faɗa miki na farko shine,kada ki sake mijinki yaji wari ko wani bashi ajikinki,ki kasance mai tsarkake jikinki ki zamo kullum cikin tsafta,yin hakan zai ƙara kusanta ki da mijinki sannan tsafta na ɗaya daga cikin ginshiƙin aure,matuƙar mace ƙazama ce to za kiga babu inda auren ya ke kaiwa,kullum cikin faɗace2 da kai ƙara,abu na biyu kuma shine ki kasance mai kula masa da dukiyarsa wala yana nan wala baya nan,ke dai ki zamo mai saka idanu akan kula da dukiyarsa,sannan ki rintse idaniyarki akan kuɗinsa,duk yawan kuɗin da zai ajje kada ki ɗaukar masa,khairat nasan halinki nasan baki taɓa yin hakan ba amman ki kiyaye hakan.ladabi da kuma biyayya indai ya baki umarni ko menene ki yi,indai har bai take addini ba to ina mai jan hankalinki ki yi sa,iya girki nasan ke gwana ce akan hakan amman yanzu tunda miji zaki yiwa to tabbas ya kamata ki ƙara ƙwazo sosai ta yadda zaki yi fice aduniyar girki.

Khairat idan har na ce zan zaunar dake inyi ta yi miki magana akan aure to tabbas zamu ƙwana ban gama ba,sai dai ince Allah ubangiji ya baku xaman lafiya me ɗorewa.
Tana faÉ—ar hakan ta rungume ni tana kuka sosai,nima kukan na ke a haka Rashida ta shigo ta samemu,itama ta taya mu kukan,babu mai rarrashin wani.

Mama ta ce"khairat wannan envelope da kika bani wanda wannan bawan Allahn ya baki,jiya na buɗesa naga kuɗi ne aciki har dubu ɗari,to shine na wuce kasuwa na siyo miki wasu abubuwan,banso na yi amfani dashi ba amman Aliyu ya tabbatar min da mutumin arziƙine,sannan yau daya zo ɗaurin aure ya baki ƙyautar mota guda,amman mahaifinki ce wa yayi ba za'a amsa ba,amayar masa amman motar tana gidan Aliyu,za'a siyar a siya miki wani abin mai amfani."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.