Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 7 of 90

"to me Hajiya tunda dai bakasan inda motocin suke ba shikkenan ba sai ka gaya min kai ɗan hajiya bane,tunda ni dai ba ƴar hajiyar ba ce to shikkenan,bari inje in hau motar haya in tafi abuna ni dai yau babu me hanani zuwa ƙwatarwa jika ta ƴanci duk baƙin cikin mutum ma sai dai ya yi don ya yi ta banzar.

Tana fitowa waje ta dinga tsare adaidaita amman suna ƙin tsayawa,cen ta hango Bilal yana ɗaga mata hannu cikin motarsa ya yi gaba abinsa.
"Kai amman yau muguntar fulanin bauchi ta tashi ai Bilal kasha a maman ruƘayya uwarka dole ka Ɗagomin hannu a mota,yau zanga wanda ya Ɗaure maka gindi a gidan,cikin gidan ta koma tana ta banbaminta ta wuce saahen Mahaifiyar Bilal tana zuwa kuwa ta sameta a farlo tana cike wasu takaddu,da sauri ta ajje aikin da ta ke Rashida da Nusaiba suna tayata aikin da sauri suka kalli kakar ta su don sunsan aƙwai abinda ya kawota.

"Yanzu Ruƙƙaya ke ce kika bawa ɗanki Bilal damar wulaƙantani a idon duniya ko?ki ka sakashi ya ƙwashe motocin gidan ya ɓoyesu don kada inje in karɓarwa jikata ƴancin ta ko?".

"haba Umma ta yaya zance ya aikata hakan?wallahi ban san komai a game da hakan ba,don Allah ki yi haƙuri idan ya dawo zan samesa muyi maganar".

"ikon Allah ki ma samesa kuyi maganar ba ma ki hukuntasa akan ɓata min ɗin da ya yi ba ko Ruƙayya?tunda shi Bilal ɗin shine ya haifeki ba ke ce ki ka haifesa ba ko? to shikkenan idan shi Abdullahi ɗin ya dawo ya yi masa faɗan tunda ke tsoronsa ki ke ji?".

tana faɗar hakan ta yi tahowarta,Rashida ta ce"ni fa daman nasan ba alkhairi ya kawo wannan tsohuwar ɓangarenmu ba?ke dai umma kada ki yi magana don wallahi idan ki ka ce wa yaya Bilal hajiya kaka tazo nan kin san zuwa zaiyi suyi ta ɗauki babu daɗi don haka kawai ki saka musu idanu,idan ba haka ba wa ke shiga tsakanin kaka da Yaya Bilal?.

shiru dai Hajiya Ruƙayya ta yi kanta na yi mata ciwo ta ce"Nusaiba ɗakkomin paracetamol insha kaina ciwo ya ke".da sauri nusaiba ta ɗakko mata a wani ƙaramin kid tasha sannan ta haɗa kayan ta koma ɗaki.

Nusaiba na ganin mahaifiyar ta su ta tashi ta ce"Anty Rashida gaskiya kaka ba ta ƙyautawa wallahi kawai daga abu ya haɗota da Yaya Bilal sai ta ƙare akan Mama ai bai kamata ba wallahi,ki ga fa abinda ta kewa mamansu Khairat kulli yaumin sai ta goranta mata wai ita tuba ce?ai bai kamata ba tunda har ta musulunta."

"hmm ke dai bari nusy wallahi matar nan ta tsayamin a ƙahon zuciya jira kawai na ke wataran ta taɓoni tasan ta taɓoni don abinda ta kewa iyayenmu ya isheni wallahi".

"hmm Anty Rashida gwara dai abi a sannu mu rabu lafiya tunda ta kusa sheƙawa ma kowa ta huta wallahi da jarabar mafaɗaciyar tsohuwa,ai Yaya Bilal ɗin shine dai dai ita kaf gidannan,yanzu ba ta ce wai za ta faɗawa Baba ba wallahi muna nan da ke baza ta faɗa masa ba,don ni nasan irin son da takewa Yaya Bilal,suna cikin hirar ya shigo don haka suka tsuke bakinsu suna yi mai sannu da zuwa,yasha mur ya ce"ina Mama take?".da sauri nusaiba ta ce"tana ɗakinta yanzu ta shiga don kanta na ciwo".
Shigewa ɗakin mahaifiyar ta sa ya yi ya barsu anan,Nusaiba ta ce"Anty wai me yasa Yaya Bilal ya fimu ƙyau ne?shiyasa magana ma sai ya ga dama ya ke mana mu dai sai fari kamar zabaya amman kuma ya fimu ƙyau."

"Ke ni dai rabani da maganar wannan bawan Allah kinfi kowa sanin kunnensa yanzu ya iya dawowa ya ɓata mana rai don haka ni dai ki bar maganar".

hajiya kaka ranar har kuka ta yi wai Soja ya hanata fita a gidan don yasan shi soja ne,duk wanda ya shigo ɓangarenta sai ta faɗa masa ai soja ya wulaƙanta ta.

An sallomoni daga asibiti na yi garau dani kamar ba ni ba,Baba kuma ya kafa musu tsauraran sharuÉ—a akaina don haka kowacce ta kama mutuncinta arabu lafiya.
Sanda aka sallamo ni Yaya Bilal ya koma da daddare na nufi sashensu ina zuwa na tarara da Abba da Hajiya na gaishesu na wayance na shige wajen Rashida har ta fara bacci na tasheta tana mitar waye ya tashe ta sai ta ganni ta ce"gaskiya Khairat ba ki da mutunci kinsan yau yini na yi aiki sai da wannan É—an wahalar ya tafi sannan muka huta".

mamaki ne sosai kam fuskata na ce"waye kuma É—an wahala Rashida?".banza ta yi min ta shiga banÉ—aki ta fito tare da É—auro alwala ta kalleni sannan ta ce"wa ye kuwa daya wuce yaya Bilal?".harararta na yi sannan na ce"gaskiya Rashida wallahi baki da kunya yanzu yayan namu shine É—an wahala?ni zuwa ma na yi in gansa inji sanyin a zuciyata ashe kuma ya tafi".?

sheƙeƙe ta yi tana kallona sannan ta ce"lallai khairat wai ke haryanzu yaya yana ranki baki ciresa ba?gaskiya idan har zan baki shawara ki haƙura da yaya don wallahi aƙwai matsala babba idan har ki ka ce zaki so yaya,saboda idan ma baki sani ba yau ki sani yaya ya wuce duk yadda ki ke tunanin mata da yawa suna kawo kansu waɗanda suka amsa sunansu mata masu ji da kuɗi da mulki amman wallahi ko kallo basu ishesa ba,wai shi har yanzu bai ga macen da ta ƙwanta masa ba,don haka ina mai baki shawara khairat ki yi haƙuri ki ciresa daga zuciyarki,ga maza masu mulki masu komai suna sonki ammanke kin dage sai yaya gaskiya ki yi haƙuri ki zaɓi ɗaya a cikinsu musha biki".

wasu hawaye ne masu zafi suka zubomin,nasa bayan hannuna na sharesu sannan na tashi zan tafi duk jikina a saɓile,janyo hannuna Rashida ta yi sannan ta ce"yi haƙuri khairat wallahi ban san abin zai ɓata miki haka rai haka ba ƴar uwata,insha Allah daga yanzu bazan ƙara faɗa miki haka ba,zan taya ki da addu'ar Allah ubangiji ya baki Yaya Bilal".tana faɗar hakan ta rungumeni tana kukan tausayina i'tama.
****

Kamar yadda kuka sani part 12 ne agidanmu kuma duk ƴaƴan Hajiya Kaka ne su da ta haifa da mijinta,Baba Abdullahi shine na farko sai Bananmu Abdulmalik,Baba Tijjani,Baba Kamalu,Baba Sagir,Baba Bashir,Baba Ali,Baba Auwalu,Baba Ƙasim,Anty Zulaiha,Baba usman,Anty Aisha.

Waɗannan sune Ƴaƴan Hajiya Kaka,Abdullahi yana da yara biyar ya aurar da biyu mata saura mata biyu namiji ɗaya
Yaya Bilal,Babanmu kuma yana da Yara 8,Tijjani 9,kamalu 6,Sagir 5,Bashir 10,Ali 4,Auwala 9,ƙasim 6.Zulaihat 7,Usman 2,Aisha uku.

Waɗannan sune jikokin kaka waɗanda adadinsu ya kai 74,dukkansu mazan a gidan suke da ya ke gidane mai yalwa sosai kuma daman tun kafin mahaifinsu ya rasu ya riga daya ta nadar musu waɗannsn filayen kowa da nasa,matan kuma sun ce sun barwa yayyinsu,amman duk da haka sai da suka basu kuɗi masu yawa saboda suna tausayin ƴan uwansu saboda tun suna ƙanana an koya musu tausayin ƙannensu saboda haka tunda suka taso da son junansu suka tashi shiyasa babu wani talaka acikinsu don dukkansu duk wanda ya ke samu zai janyo ɗan uwansa a kusa dashi sosai,kuma kaf ɗinsu mutum biyu ne masu kuɗin,Malik da kuma Abdullahi amman duk sai da suka ja ƴan uwansu a jiki duk abinda suka samu na ƴan uwansu ne.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.