Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 11 of 90

a ranar muka koma gida dukanmu,ni dai jikina haryanzu bai daina ciwo ba,alokacin da muka shigo cikin gidan na hango Hajiya kaka suj fito ita da Hajiya Inna ƙawarta kuma aminiyarta da alama ma unguwa zasu je.

Muna fitowa daga cikij motar kowa da guntun ciwonsa ajikinsa Rashida ce kawai babu ciwo,da sauri naga Hajiya kaka ta yi gefe tana salati kamar ta ga abin tsoro.

Bata iya magana ba har muka ƙaraso kowannenmu yana tangaɗi kamar zai faɗi,Hajiya kaka ta ce"ikon Allah sai kallo wannan wani irin dukane haka duk jikinku ya toye kamar an ƙona ku?ni dai yau naga abinda ya isheni". ta ɗora hannunta aka xa ta saka kuka Hajiya Inna ta ce"haba Hajiyata mu fasa tafiyarnan kawai yau dai gidannan ba lafiya ba"?.da sauri Hajiya kaka ta ce"yo ina kuwa lafiya jikokina duk an farfasa musu jikkunansu wallahi idan ma malamanne sukayi musu dukan ƙatti to wallahi aikinsu ya ƙare a nigeria,Allah da a ƙasar umanne da tuni sai dai wasu da tuni sunsha harbi".ita dai Hajiya Inna jan hannun aminiyarta ta tayi don tasan halinta yanzu sai ta tsaya tayi ta sunbatu kuma ba tare da ta tambayi ba'asi ba ta ɗorawa wani laifi.

Kai tsaye ɓangaren Hajiya kaka mukayi dukkanmu bayan mun zauna sai ga ta kamar an jeho ta ta ce"to wallahi Allah bazamu yarda da fasawa jikokina jiki ba,an gaya musu tsintosu mukayi ko kuwa?to wallahi ahir ɗinsu".dukkansu sunkuyar da kansu sukayi musamman ma waɗanda suka san sunyi laifin su Nadiya kenan,duk bakunansu a kumbure wasu kuma idanuwansu.

"Ikon Allah ku kuma me ye na wani sunkuyar da kai kamar munafukai?".babu wanda ya amsa mata acikinsu Yaya Bilal daya gama harzuƙa musamman kalaman kaka ya ce"loook Hajiya kaka ba abinda ki ke tunani bane?waɗannan yaran ni da kaina na yi musu wannan dukan"?.da sauri Hajiya kakanta juyo tana kallon Bilal kamar dai yaune ta fara ganinsa.
Fashewa ta yi da kuka ta ce"to wallahi Allah Ya isansu mugu mai jinin fulani,mai Ƙirar samu dawa kawai wato abin ma mugunta ne ko?ai gashi ka daki waƊannan amman baka daki waccen Ƴar jakar ubarba mai Ƙira irin ta ka".ta nuna Rashida ita kuwa ta murguƊa mata baki".kaka ta harzuƘa za ta Ƙara magana Baba na ya dakatar da kaka wajen ce wa"umma waƊannan yaran sun zubar mana da mutuncinmu a gari,waƊannan yaran da ki ke ganinsu Ƴan neman mata ne".

Hajiya kaka bata fuskanci abinda baba ya faƊa ba ta ce"a'ah malik to idan basuyi abota da mata ba to daku zasuyi?"Ganin kaka bata fuskanci abinda suke nufi ba yaya Bilal ya daka musu tsawa ya ce"i'm talking to u ku faɗa mata abinda kukayi ko kuma yanzu in ƙara yi muku wata sabuwar tafkar".ana cikin hakan iyayensu mata suka shigo su dukansu saboda an gaya musu abinda ke faruwa.

Suka zazzauna kowaccensu ji take kamar ta haÉ—iye zuciya ta mutu saboda an daki Æ´ar ta,kuma zuwansu ya yi dai dai da fara bada labarin tun kaisu makaranta har zuwa iyanzu da sukayi abinda sukayi.

Sosai iyayensu suka fara salati masu kuka na yi masu zagin ƴaƴansu suma sunayi,amman mama kishiyar mama da sauri cikin kuka ta ce"wallahi wannan ƙarya akewa su Nadiya idan hakanne me yasa su waɗance munafukan ba'a dakesu ba aka fake da dukan waɗannan tunda sune marasa galihu".wata uwar harara baba na ya bita dashi sannan ya ce"wallahi idan kika ƙara magana awajennan to abakin aurenki".yana faɗin hakan ya juyawarsa kamar ba shine ya yi maganar ba.

Sosai abin ya ƙular da mama ta cigaba da kukanta wai yanzu akan wannan shaiɗaniyar yarinyar aka kuburawa ƴarta idanu har haka.

Jagwab kaka ta zauna kamar zaman Æ´an bori ta ce"yau na shiga É—aka ban fito ba,me zan gani haka acikin jikokina aka samu waÉ—annan masu halin mutanen annnabi luÉ—u?ya Allah idan mafarki na ke Allah yasa in farka."

"kaka wannan maganar fa ta zama dole ayi meeting akanta,insha Allah yanxu kowa zai tashi ya je ya huta gobe za'ayi meeting insha Allah".cewar Baba Abdullahi mahaifin yaya Bilal.

Kaka ta ce"Allah sarki ABIN CIKIN ƘWAI,so sukayi su lalata miki rayuwarki amman Allah ya fisu Allah kuma ba azzalumin bawansa bane,ni duk da haka ma sai na kaiki asibiti inji ko sun taɓa miki rayuwarki masu rayuwar dabbobi kawai".tana faɗar hakan ta ja hannuna muka shiga ƙuryarta kunya duk ta isheni wai za ta saka a dubanu gasu Baba duk a wajen.

dukkansu suka tashi jikinsu duk a sanyaye Hajiya Inna ta shigo ta kalleni ta ce"oh sannu ƴar nan Allah yabi miki haƙƙinki,Allah kuma ya shiryar dasu gaskiya,don wannan sam ba halin ƴan mutunci bane,wannan halin ƴan akuya ne."

caraf kaka ta amshe tana ƙwalla ta ce"ni fa abin nan ya bani mamaki wallahi yo me ye abin so ajikin mace da mace idan ba rashin mutunci ba?ni fa anya ma kuwa waɗannan yaran basu shaye shaye?na ga abin na su ya zarce hankali sun kama ƴar uwarsu sun ciccijeta haka kamar ƴaƴan mayu?Allah badon jikokina bane wallahi da sai igiya ta yi saura don bazan yarda ba,idan ita waccar sokuwar inyamurar uwar ta ki ta yi shiru to ni wallahi ba zan yarda ba don ni ba sallamammiya ba ce".

haƙuri Hajiya kaka ta fara ba ta ta ce"ki yi haƙuri waɗannan yaran addu'a zamuyi ta yi musu Allah ya shiryesu,kuma daman inason in gaya miki kada ki yadda ƴaƴanki su mayar da yarannan makaranta don ƙara lalacewa zasuyi,kuma sannan su fito da miji ayi musu aure ko hankalin kowa ya huta".

da sauri kaka ta ce"kai Inna gaskiya ƙwaƙwakwarki tana ja wallahi,ke daman tun muna yara kina da ja,su Hansai basuyi asarar kuɗin tara ba".dariya Hajiya Inna ta yi sannan ta ce"to ai kinga gwara ayi musu auren kowa ya huta,ko kuma ma idan sukace muku basu da mazajen auren ga ƴan uwansu maza nan sun cika gida taf sai a harhaɗasu kawai kowa ya huta."

Sosai kaka ta yi murna da shawarar ƙawatarta Hajiya Inna,suka cigaba da tsara abubuwansu ni kuma na fito waje don tafiya sashenmu ƙafata ta yi tsami sosai jan ƙafar kawai na ke,ƙamshin turaren yaya Bilal naji naji wani irin mugun shauƙi har cikin raina ban ankara ba na ji an bangajeni an wuce na buɗe idanuwa da ƙer,Yaya Bilal ya wuce ko kallon inda na ke baiyi ba ballanta na ma in saka ran zaiyi min magana,wasu zafafan hawaye ne suka fara ƙwaranyo min,son maso wani ƙoshin wahala tun ina ƙarama ta na ke dakon son yaya Bilal har girma na amman shi ko ajikinsa idan ya ganni ma yadda kasan yaga kashi haka ya ke nunawa.

Allah ya yiwa yaya Bilal halitta mai ƙyau da tsari kaf ƴan gidanmu babu wanda ya kai koda ƙwatansa a komai,ga ilimi,addini,ƙyau,kuɗi,nasaba.duk ta haɗa waɗannan abubuwan duk jikokun gidanmu farare ne yawancinsu amman ni ba fara ba ce,amman kuma baza'a kirani da baƙa cen ba,ina da ƙira mai ƙyau kuma ina da ƙyau dai dai gwargwado,ina da ilimi,tarbiyya,nasaba,da sauransu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.