Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 29 of 90

Asanyaye mahaifiyata ta tashi da addu'ah a bakinta,mahaifiya ta macece mai yadda da ƙaddara ta kallesu kamar babu wani abinda ya dame ta ta ce"Iklima &mariya ku kasance masu faɗin alkhairi akan ƴaƴan wasu,sai kiga kuma naku ƴaƴan sunyi albarka amman ba zagin ƴaƴan wasu ba,matsalar khairat ni ta shafa ba wani ba,kuma mutuwar aure ba ku aka saki ba ni aka saka don haka wannan ba matsalarku ba ce,ku fita daga ɗakin nan".
ta faÉ—i hakan cikin É—aga murya".
Dukkansu sun tsorata da canjin yana yin Zulaiha,donbata taɓa yi musu koda musu bane,amman yau ita ce har da ɗaga musu harshe".

"hmm zulaiha kina borin kunya ne dai kawai saboda asirinku ya tonu ke da gantalalliyar Æ´arki Æ´ar daÉ—i maza,to kodai baki ce mu fita ba yanzu zamu fita daga wannan É—akin shaiÉ—aniyar Æ´ar ta ki don haka mu mun fita kada ma garin tsayawa wata masifar ta shafi namu Æ´aÆ´an don ku ba alkhairi bane acikin al'umma.
Da sauri suka fita don sunga yadda mode É—in mama ya canja sosai kada silar tsayawarsu ta yi musu wani abin.

Kulle ƙofar gam mama na ta yi sannan ta matso inda na ke,numfashi na yana fita da ƙer ta kalleni fuskarta sam babu annuri ta ce"khairat kin bani mamaki kuma kin bani kunya,haƙiƙa ban taɓa zaton haka daga gare ki ba,yaushe ki ka lalace?yaushe ki ka zubar da tarbiyyar dana baki?haƙiƙa khairat na ji matuƙar kunyar kaina da kuma mutanen da suka yarda da ke ɗari bisa ɗari".
ta juya min baya ta ce"khairat ki faɗa min wanda ya yi miki ciki har ki ka yi ɓari?idan har ki ka ƙi faɗamin to Allah ya i'sa tsakanina da ke,kuma na cire ki daga cikin ƴaƴa na".sai ta juyo tana fuskanta na.

Tausayin khairat ya cika zuciyar zulaiha,uwa da É—a kenan amman a fuskarta rashin imani tsantsana ta nuna wa Æ´ar ta don ta faÉ—a mata gaskiyar abinda ya faru.

Bakina yana rawa na ce"haƙiƙa mama wannan rana har tafi ranar mutuwa ta zafi,bantaɓa tunanin ko da a mafarki zan tsinci wannan rayuwar ba,ban sani ba ban san kuma me ya faru dani ba?ni dai na tashi na ji ni a baƙon yana yi,ban taɓa zama na minti goma dana miji awaje ɗaya ba,mama kin sani koda saurayin ma na yi to ya zamar min dole in faɗa miki,don ban saba ɓoye miki komai ba,tun yarinta na har zuwa yanzu,wallahi mama ban taɓs kusantar wani ɗa najimi ba?me zan gaya miki yanzu ki tabbatar da hakan?".

da sauri mama ta juyo ta ce"khairat tashi in duba ki"?.

duk da halin da na ke ciki sai da na shiga ɗimuwa sosai akan hakan,duk da mahaifiya ta ce amman da tsananin kunya,tunda dai yanzu ni ba ƙaramar yarinya ba ce".

tsawa ta bugamin da ƙarfi,da sauri na tashi daman rigar bacci ce ajikina na ciresa baki ɗaya.

Kallona sosai take da mamaki,babu wata hanya ko kaɗan daya nuna khairat ta taɓa kusantar ɗa namiji,grady a matsayin budurwa taje cikakkiya.

Shiru mama Ta yi ta kasa ce wa komai,ta tafi tunanin wani abu daya shuɗe,tabbas jiya taga hajiya iklima na barbaɗa abu a ƙofar ɗakin khairat amman bata san kome ye ba,da sauri ta fita waje kai tsaye ɗakin hajiya iklima ta shiga,zuciyarta har wani bugawa take,lallai hajiya iklima ta taɓo ruwan dafa kanta,don yau za ta nuna mata ko da yaya kurna tafi magarya daɗi.

Sosai ta tsorata da ganin zulaiha,tos wani ɗan ƙwalba da ta ɗakko ya fashe,tsoro sosai ya fito daga idanuwan hajiya iklima.

Bakinta na rawa ta ce"zu. .zu. .zulaiha ms ki ka shigomin ɗaki"?.bata i'da gamawa ba zulaiha ta shaƙo wuyanta sosai har dai da ta kaita bango tana kakkarin aman wahala,cikin ɓacin rai da baƙin ciki zulaiha ta ce"kina tunanin Allah zai barki da abinda ki ka yiwa jinina?yarinya bata ji ba,bata gani ba kin ɗora mata lalurar dole?to wallahi sai na kashe ki na kashe banza".

Amira ce da ta shigo ɗakin yanzu taji abinda ke faruwa ta sheƙa da gudu tana kiran mutane,sosai ɗakin ya cika da mutane kun san gidan yawa ɗuuu kowa ya shigo.wanda bai san abinda ya faru bama yanzu ya sani,hajiya kaka ma ta shigo don tana cen tana kukan abinda ya faru,mero ma ganin kakan tana kuka ita ma sai ta hau kukan sai yanzu ne da suka jiyo ihu suka firfito har mero.

Da ƙer aka cire hannun mama daga wuyan hajiya iklima ta haɗa wata uwar zufa sosai,kamar wadda ta yi babban yaƙi,hannunta na kan wuyanta tana murzawa ta samu waje ta zauna a bakin gadonta,tana tarin wahala.

Sosai hankalin kowa ya tashi da jin duk abubuwan da suka faru,wasun su sun yadda wasu kuma basu yadda ba,hajiya kaka tana kuka ta ce"kai gaskiya zulaiha inyamurai sunyi asara da suka haifo ki a matsayin Æ´arsu,yanzu kuma bayan hanyar da ki ka saka Æ´arki shine ki ka biyo kishiyarki har É—aki zaki kashe ta?ah to wallahi ba agidan nan za'ayi kisan kai ba,zo ki fita cen garinku na Æ´an obwa musho,kije cen ki yi,idan kinga da ma-ma ki shiga boko haram ko kuma Æ´ar kidnapping amman mu ba'a nan ba".

Tana faɗar haka taja ƙeyar mama har ɗakinta tana tsaye ta ɗibi kayanta ta fito,sai dai me?sai ga yaya Aliyu ya shigo kallon mama sosai ya yi,sannan ya kalli hajiya kaka wacce fici-ficin idanuwanta suka kuma komawa ciki sosai,alamar rashin mutunci take ji ko kallon Aliyu ɗin ma bata yi ba.

"Mama lafiya me ya faru?ya na ganki da aƙwati kuma?"

Duk alokaci ɗaya ya jerowa mahaifiyar tasa tambayar,mama ta kallesa cikin tausayinsu sannan ta ce"Aliyu yau zamana agidanku ya ƙare,zan tafi da kewarku amman ga ƙanwarku nan,i'ta kaɗai ce mace acikinku don Allah ku kulamin da i'ta kamar ina nan?ga ƙaninku da ke makarantar ƙwana shima ku kulamin dashi don Allah".

Kasa gane maganar mahaifiyar tasa ya yi,kansa ya yi masa nauyi sosai harshensa ya kasa furta komau har maman ta fita baki É—aya daga cikin gidan,da sauri yabi mahaifiyar tasa,gudu ya ke sosai a motar sai dai yana zuwa titi yaga ta hau mota,da sauri yabi motar hankalinsa duk a tashe.

A babbar tasha aka ajje ta,tana fitowa taga Aliyu ya biyota,ta gyara zaman mayafinta sannan ta ce"Aliyu yanzu sai da ka biyoni?da ka zauna kusa da ƙanwarka ka lallashe ta,don a yanzu tana buƙatar mai taimakonta akusa da ita,wanda zai share mata hawayenta bayan rashinta.

"Mama wai me ya faru da khairat É—in?wani abu ne ya faru da i'ta?".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.