Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 41 of 90

"Inye au daman kai Bilal sakarai ne?tun daga yanzu mace ta fara juya ka?yadda uwarka ke juya ubanka?ah lallai su Ruƙayya za'a ɗauki darasi anan,kana wulaƙanta ƴar uwarka saboda wannan yaloluwar yarinyar wacce ko ƙugun arziƙi ba tada shi,aba kamar muciya an ɗaura mata zani,shine ka ke wani rawar ƙafa da rawar kai,kai ga me mata ko?to wallahi ka sake ka cuci jika ta Allah ya isa".

Tana faɗar hakan ta dawo inda na ke ta janyo hannuwana fuuuuu,sai gani gaban Yaya Bilal,na tsaya da ƙer ƙafufuwa suna ta rawa saboda tsoro da fargaba.

"Yauwa tsaya nan!".
Hajiya kaka ke faɗar hakan ta ce"yauwa kema tsaya adinga yaƙe bakin dake tunda tallan makilin suke,ana wani hoto ana yaƙe haƙora kamar wasu masu tallan makilin".ta faɗi hakan tana harararsu.

Abinda kaka bata sani ba,ashe duk ana jinta acikin lasifiƙa don kusa da lasifiƙar take,haushi sosai Bilal yaji akan wannan cin fuskar da kakarsa ta yi masa,don kakar tashi ta ƙara jin haushi sai ya riƙe hannuwan Jidda ƙam kamar wani zai ƙwace masa ita.

Sai kuwa kaka ta ce"Hmm ai kin ɓur inji tusa,ai idan baka mayar da ita ciki ba,kai baɗan Ruƙayya da Abdullahi bane,shasha mara sanin ya kamata,ke kuma kina nan kamar wata ƴar tsana da wani jememmen jikinki".

sosai aka saki dariya awajen,Hajiya Ruƙayya abinda surukar tayi ya tsaya mata sosai,kaɗan ya rage ta yi kuka tsabar takaici,wata ƴar uwar Hajiya Ruƙayya ta ce.

"Wai ni Anty har yanzu wannan masifaffiyar tsohuwar bata daina rashin mutuncin nan ba?kawai ki saka yara agaba,don ba'ason jikarki,to uban waye yasa ta nace sai ta aureshi?ai yanzu gashinan agaban mutane ya wulaƙanta ta ai ni ya yi min dai dai daya wulaƙanta ƴar banza".

Ita dai Hajiya Ruƙayya kasa magana ta yi saboda tsabar ɓacin rai,ji take kamar ta kama Hajiya kaka ta yi ta dukanta,saboda yau Hajiya kaka ta kai ta ƙarshe.
Jidda taji zuciyarta kamar zata fito saboda haushin tsohuwar take ji,amman ta yi alƙawarin sai ta koya mata hankali sosai.

Ko da akazo wajen yanka cake,sosai akayi drama don da Bilal ya bawa Jidda ta basa,sai ya kasa juyowa ya bawa Khairat sai dai abinda ya bawa kowa mamaki da sha'awa bai wuce yadda Khairat ta yanko cake ɗin ta saka a bakinta ba,sai da ta bawa kowa tausayi awajen,abinda kuma ya ƙara bawa kowa mamaki bai wuce yadda khairat ta juyo da Bilal ba,ta saka masa cake ɗin abakinsa.

Ya samu kansa amai haɗiyesa,yana kallonta da mamaki da kuma ƙarfin hali irin na ta,Jidda kuwa ta cika ta yi ɓam,saboda haushi tana ta hararar Khairat.

Ran Hajiya kaka ya yi fes da abinda ya faru,hajiya kaka ta kira mai hoto ta ce ya yi mata ita kaɗai da jikarta,haka kuwa akayi mai hoto yazo ya ɗandasa musu hotuna masu matuƙar ƙyau,ta janyo hannun Bilal ta saka ana khairat suka kalli junansu unexpected mai hoto kuwa ya ɗauka ƙes.ƙes.
Sannan aka yi musu da hajiya kaka ma.

Anci ansha amaren sai hidimarsu suke,gwanin sha'awa,nima yanzu na saki jikina gani ga su Rashida ga Maryam ma,ƙannen Anty khadija ko mutum ɗaya bai zo ba,saboda suna taya ƴar uwarsu kishi.
Sai ƙarfe tara aka tashi goma sha ɗaya aka tashi daga dinner ɗin,muka koma gida duk a matuƙar gajiye,mun fito daga cikin wajen kawai idanuwa na suka kaimin kan Jidda da Yaya Bilal,tana rungume a ƙirjinsa har suka shiga cikin motar mai ƙyau.

Na kafesu da idanuwa na,zuciyata sam babu daÉ—i sai yanzu na gane ce wa ka auri wanda ya ke sonka ma wani abune arayuwa,rai na duk babu daÉ—i muka tafi gida.

Kowa ya yi bacci sai munshari suke,na wurwucesu duk sun baje akan kafet ɗin,suna ta bacci wasu akan gado wasu kuma a ƙasa,na wuce banɗakin na ɗauro alwala sannan nazo na tada Sallah na yi raka'a huɗu,sannan na ɗaga hannaye na sama ina roƙar ubangiji ya kawo min sauƙi acikin lamarin aure na,ya cusawa yaya Bilal sona wanda har yafi ƙarfin son da na ke masa.

Na shafa addu'ar ina kuka,Rashida da ke kusa dani ta kalleni ita ma hawayen take muka shafa addu'ar tare.
****

Washe gari da wuri su Rashida suka fara shirinsu,ni kuwa sai bacci na ke mai cike da son Yaya Bilal,wai gamu da wasu fararen yara aƙasan wata bishiya mai kyau muna lilo gwanin sha'awa.

Rashida ta ce"ikon Allah sai kallo mu duk mun tashi mun shirya amman ke da ki ke matsayin amarya sai baccin asara ki ke?ta faɗi hakan tana tashi na,miƙa na yi sannan na tashi ina salati.

Kai tsaye banÉ—aki na shiga na shiga na yi wanka tare da brush,don na yi sallah tun asuba tare da yin azkhar É—ina na safiya,wanda kuma wannan tarbiyyar gidanmu ce,duk wani yaro ko babba da asuba ya ke salla tare da karatin qur'ani da kuma azkhar.

ÆŠaya daga cikin kayan da Hajiya kaka ta bayar aÉ—inkamin na É—akko shadda ce fara sol,wacce ta gaji da aiki ga shi tasha tsone work,É—inkin doguwar riga,ni da mero ta bayar aka yimana,amman ita mero nata kalar ash ce shaddar.

Munyi kyau sosaj sai ɗaukar ido muke,na fito daga ɓangarenmu sai sheƙi na ke,lalle na ya yi kyau sosai a hanya muka haɗu dasu Salimat da Iman,duk suna da cikinsu har ya fito ma,Salimat ce ta yi dauriyar ce wa"oh su khairat amarya?babu magana ne?".

Banyi niyyar yi musu magana ba,na gaishesu iman tana wani cin magani ta wuce gaba tana ce wa"hmm Allah dai yasa cikin ya fita kada akaiwa wani gidansa".ta faÉ—i hakan tana hararata.

Sosai naji zuciyata ta yi wani irin zafi,na wuce ina goge ƙwalla acikin idanuwa na,kai tsaye na wuce sashen Hajiya kaka.

Ɓangarenta acike sosai na wuce cen cikin ƙuryar ɗakinta ina gaida mutanen da ke wajen,ɗakinta babu kowa aciki ashare a goge sai tashin ƙamshin turaren wuta ya ke,daman Hajiya kaka aƙwaita da tsaftace waje.

Na baje akan gadonta tare da cire golden ɗin mayafina,na cire awarwarona da ɗan kumne na cire kayans nabar iya under ɗin dake jikina,na hango kayan lefena akan sif ɗin hajiya kaka saiti tara cif,wanda daƙer yaya Bilal ya yi lefan wai shi bashi da kuɗi,alhali ko ƙwanan nan an ƙara masa matsayi kawai dai bai so na ne shiyasa zai ce hakan,jidda kuwa abakin mutane naji ana cewa dozin biyu ya yi mata.

Na rintse idaniya ta ina kiran sunan Allah,a haka wani bacci mai nauyi ya É—aukeni,sai da naji Hajiya kaka na tashi na tana ce wa"ikon Allah wannan amarya da lalaci ki ke,ga mero cen ta shige cikin gida ana ta hotuna da ita,ita da ma yaushe tazo gidan?amman ke da kika rayu agidan kina nan kina wani baccin asara.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.