Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 14 of 90

Ɗago kansa ya yi sannan ya ce"kai kaka ni fa idan damuna zaki yo sai in fita?kawai daga shigowarta sai ta haɗamu".?ganin irin mirmisisin da ya yi da idanuwa bata ƙara ce masa komai ba suka cigaba da hirarsu kaka na ɗarsa wani abu azuciyarta.

Ina fitowa na samu wani ɗan lungu na fashe da kuka mai ƙarfin gaske,na yi mai i'sa ta sannan na juya xan tafi sai muka ci karo da yaya Aliyu da Yaya Mukhtar.da mamaki suke kallona sannan suka haɗa bakinsu wajen ce wa"a'ah little sis me kuma ya sameki haka?me ya faru agidan?".saurin goge fuska ta na yi to me zance musu?ce musu zanyi inason yaya Bilal shi kuma yana wulaƙanta ni ko me?no ai abin da kunya.

Ganin bance komai ba suka sakani agaba wai sai na gaya musu abinda ya faru?bakina yana rawa na ce"kukan rabuwa ta na ke yi da Rashida".na faɗi hakan cikin shagwaɓa.dariya sukayi dukansu musamman yaya Aliyu ya ce"to ikon Allah kukan kuma tun yanzu?ai haƙuri zakuyo dukanku don ku daman rayuwar mace ƙanƙanuwa ce daga gidan iyayenta sai gidan miji,don haka ki share hawayenki kinji?"da to na bisu sannan na wuce.

Yaya Mukhtar ya ce"bro ni fa na samu mata agidannan Tun khairat bata kai haka ba na ke matuƙar sonta har yanzu,amman na rasa ta inda zan faɗa mata".?dariya yaya Aliyu ya yi sannan ya ce"bro me gaskiya kada ka yi sakaci kamar yadda na yi akan Rashida ka gabatar mata da kanka ka ga kawai sai a haɗa bikinmu asha biki".ya faɗi hakan yana kallon mukhtar wanda shima shi ya ke kalla.
***

Har na isa sashenmu jikina duk a sanyaye ya ke,ban kula da mutanen da ke farlon ba na yi wuce wa ta sai kuwa naji anty Hamdala ƴar Mama wato uwargidan su maman mu wacce take aure a Abuja ta ce"ikon Allah ita kuma wannan ƴat baƙar yaushe ta fara raina mutane har haka?".mata ce"hmm Hamdala ta gaisheki tana ganin kakarta da uwarta sun ɗaure mata gaba agidannan sai wanda taso ta gani da mutunci a gidannan sannan take gani da gashi,ai kinga gwara mutum ya kama kansa kafin kuma a koma dukanka".cikin jin kunyar maman nawwara wato antyna Hamdala na ce"mmn nawwara ina yini?wallahi ban kula da zuwan ki bane amman don Allah ki yi haƙuri".na kama kunnuwa na alamar ban haƙuri,sai kuwa ta ce"ai ke dai kam Khairat kin shiga ukunki da iya haɗa munafunci yanzu da ki ka saka za'ayi wa su Nadiya auren dole me ye ribarki?baki da wata riba sai ta munafunci da iya haɗi,to wallahi ni dai kada ki yadda gulmarki tazo kaina don ba Hajiya kaka ba ko Hajiya wacece agabanta zanyi maganinki ehe don ni ba kunyar wata tsohuwa na ke ji ba,idan su Baba ita ta haifesu to mu ba'ita ce ta haifemu ba".

Sosai na yi mamakin abinda Anty Hamdala ta faɗa na rasa me yasa iyayensu suka koya musu rashin sanin darajar mutane,Daman Hajiya kaka sun saba yi mata rashin kunyarsu da fitsararsu abin yana yimin ciwo don duk zagin da Hajiya kaka ke yi wa mahaifiyata bai saka ko kaɗan na raina ta ba,shiyasa sam bata bari a cuce ni ko kaɗan sai dai idan bata wajen don takan faɗa ce wa wai ni banyo mai sunan na ta ba,don ni ba mutum ce mai faɗa ba,sai ka yi min abu ban taɓa nuna maka ka yi min ba sai dai inyi kuka in share hawayena ko mama ba ta sanin komai idan ba ni ce na gaya mata ba.
Ban sake ce wa komai ba na wuce ɗaki raina babu daɗi,a rasa me yasa ƴan uwana suka tsaneni haka?ko don suna ganin son da Baba ke nuna min ne oho?ko kuma fifita ni ɗin da kaka ke yi ne?don ita Hajiya kaka babu ruwanta ko agaban waye sai ta nuna min ƙaunar nan daga Allah take.

Mama ta sameni aɗakina lokacin na fito wanka na gaisheta ta ce"yauwa Khairat ɗazu yayanki Aliyu yazo ya ce gobe zakije gidansa Khadija babu lafiya ga shi kuma zaiyi tafiya kinga sai ku zauna a atare".?to na ce mata amman ba don raina yazo ba don sam bana son zuwa gidan babban yayan nawa wanda shine babba awajen mama shine ɗan farin ta,abinda yasa bana son zuwa saboda Khadija aƙwaita da shegen son jiki sannan ba tada jan dangin mijinta ajiki,duk da itama ƴar uwarmu ce don auren dangi a ka yi musu Babanta baba faruku Ƙanine awajen babanmu kuma uwa ɗaya uba ɗaya suke.
Babu yadda na iya washe gari da wuri na haɗa kayana bayan na gama gyara ɗakina harda babban farlonmu duk sai da na gyara sannan na nufi kitchen inda mama take aiki,na samu Nadiya tana cin ayaba sai zubar da ɓawon take,mama kuwa ko kallon ɓangaren Nadiyan bata yi ba,tana ta aikinta na rasa mama wata iriyar macece sam babu ruwanta da wani faɗace faɗa ce rayuwarta so simple ce,babu yadda za ayi inyi wa mahaifiyarsu Nadiya haka don mama bata taɓa bani ƙofar raina wani cikinsu ba,nima ko kallon Nadiyan banyi ba don nasan neman jaraba take na wuce wajen mama,da fara'a na ce"mama aƙwai abinda za'a ƙarasa miki ne?"ɗan murmushi ta yi sannan ta ce"a'ah na gama komai ɗauki abincin Kaka ki kai mata anjima kuma Boy zai zo ya ɗaukeki"?in dai kaji mama ta ce boy to yaya Aliyu take nufi ɗan farin mama don tana matuƙar ji masa kunya don ko hira sosai basu cika yi ba.

Tsaki naji Nadiya ta yi sannan ta fita,nasan sarai dani da mahaifiyata take amman bance komai ba na girgiza kaina na wuce.
Ina zuwa sashen Hajiya kaka na same ta tana kallon labaran safe a tv ɗinta,da fara'a ta amshi basket ɗin kayan karya kumallon na ta sannan ta ce"ABIN CIKIN ƘWAI Lafiya naga kin rame haka ko wanine ya taƁaki yanzu in saƁa masa".

Girgiza mata kaina na yi kafin in bata amsa naji sallamar Yaya Bilal,a take naji gabana ya yi wani mugun faÆŠuwa don tsabar tsoronshi da na ke ji,hajiya kaka ta kalleni ta daka min harara don tasan abinda na ke wa tsoron.

hajiya kaka ta ce"ke kuma me ye kika wani firgita kamar kinga wani namijin zaki"?.É—an dai dai ta nutsuwa ta na yi sannan na ce"babu komai kaka bari inje mama za ta aike ni ne".

Hajiya kaka ta ce"hmm kyaji dashi dai da kin gansa sai ki kama wani rarraba idanuwa kamar mujiya yo sojan har wani abu ne da zaki dinga tsoronsa haka?Ni fa kakanku nasha yi masa kuka akan ya kaini barrek ÆŠinsu don a tafi filin daga dani saboda rashin tsorona,yo me aka yi aka yi wani soja".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.