Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 45 of 90

Ta faÉ—i hakan tana mana wani kallon banza,Maryam ta ce"hmm idan kunsan wata baku san wata ba".sai ta danna wayarta ta kira hajiya kaka tana shaida mata abinda ya faru.

Kai tsaye Hajiya kaka ta shiga ɓangarensu Bilal.ta yi sa'a kuwa Baba Abdullahi yana nan suna hira da matarsa.hajiya Ruƙayya na ganinta ta gimtse fuskarta don tasan ba alheri ya kawo hajiya kaka ba.

Hajiya kaka ta nisa ta ce"Ruƙayya zo ki dake ni ba murtuke fuska ya kamata ki yi ba?uwar rashin ɗa'a.yanzu gashinan kin koyawa ɗanki Bilal ya wulaƙanta ƴan gidansu,saboda shima yanzu ya yi gida ko?to wallahi ko awata uwa duniya ya ke ki kirasa ki faɗa masa wallahi ya yi maza yabar maryam ta shiga gidan nan idan ba haka ba.masifar akanki zata ƙare,yo idan ma ba rainin hankali ba tayaya za'ace a hana ƴan uwan mutum shiga gidan ɗan uwansa?a ina aka taɓa yin hakan?ko ke ƴan uwanki sun taɓa zuwa nan aka hanasu shigowa?to wallahi ahir ɗinki daga ke har ɗan naki mara kunya".

sunkuyar da kai hajiya Ruƙayya ta yi,Baba Abdullahi ransa yakai ƙololuwar tashi,ya nisa ya ce"Ruƙayya yaushe Bilal ɗin ya yi tafiya?ashe shi yanzu idan zaiyi tafiya haka kawai ya ke yinta?saboda ya zama babba ko?babu saka albarkar iyaye?."

"wallahi nima bansan ya yi tafiya ba?amman ka yi haƙuri".

Number Bilal ɗin ya kira,ya ɗaga yana tsaka da aiki bayan sun gaisa ne ya rufesa da faɗa sosai,ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba,Bilal ya yi shiru kawai yana jin faɗan mahaifinsa,ya basa haƙuri ya kashe wayar ya kira obinna ya bada umarnin maryam ta shiga.

Maryam na shiga ta kalli jidda ta ce"to uwar mata yanzu ma ai sai ki hanani shiga?uwar iyayi mai son raba kan Æ´an uwa".

Ta faɗi hakan tana hararar jidda ɗin.jidda ta yi ƴar dariya ta harɗe hannayenta a ƙirji tana wa maryam ɗin kallon rainin hankali ta ce"hmm kin bani dariya wallahi,ai ta banzar tunda ita dai wacce take cikin gidan ba tada wannan matsayin da zata bada doka da order aji,don haka ni baku burgeni ba".

Ta faɗi hakan tana nuna halin ko in kula,har maryam ta yi gaba sai kuma ta dawo ta ce"hmm jidda ma ki ke kowa?to idan ban mayar miki ba kice ni ba jikar hajiya kaka bace?kema da ki ke wani fiffigewa wai ke gaki star awajen miji ko?to wallahi kiji tsoron Allah don duk matar da ta saka ido ana wulaƙanta ƴa mace tana jin daɗi to wallahi wataran itama sai an wulaƙantata wataran itama,don haka ki guji ɓacin rana".

Dariya sosai Jidda ta yi ta ce"oho dai tsabar rashin zuciya ya ce baya so amman sai da aka liƙa masa."ta faɗi hakan tana tin tsirewa dariyar muguntar ta faɗamin magana.

Har na yi gaba sai kuma na dawo,na kalleta idanuwa na suka cika ɓam,da hawaye ban yarda sun zubomin ba na wuce sashe na.na barsu ita da maryam suna ɗauki ba daɗi.

Sosai maganar da jidda ta faɗamin take bin dukkan gaɓɓan jikina,na ƙwanta akan ɗaya daga kujerun farlona na saki kuka mai ƙarfi,tabbas na cancanci Jidda ta yi min gori,yau ƙwanana huɗu amman ko albarkacin haƙƙina da ke kansa ai ya kamata ya saukemin,amman madadin rashin hakan gashinan matarsa na wulaƙanta ni.
"Haba Khairat yanzu don wannan banzar ta faɗa miko magana shine ki ke kuka?ai kuwa matuƙar zaki dinga yi mata kuka to kuwa ta samu lagon ƙuntata miki agidan aurenki,ki zama jajirtacciya agidanki,nasan kina da dauriya amman ki ƙara daurewa kinji".ta faɗi hakan tana sharemin hawaye na.

Nan dai muka shiga hira take cemin gobe za'a kawomin gara ba'a gama haÉ—awa bane,na ce mata babu komai.

Ta ce"yanzu ma daga asibiti na ke naje dubo Rashida,kinsan tun bayan bikinku ba tada lafiya".ta faÉ—i hakan cikin damuwa.
Nima cikin damuwar na ce"innalillahi ashe haryanzu jikinne?shiyasa dana buga mata waya naji shiru?tun shekaran jiya na ke kira amman switch up".na faÉ—i hakan cikin damuwa.

Maryam ta ce"ke dai bari ɓari ta yi wallahi ciki wata huɗu".da sauri na saki salati tsabar tausayi kamar zanyi kuka,na ce"yanzu ya jikin na ta?".maryam ta ce"ai da sauƙi ma yanzu don wallahi ranar da tayi ɓarin da mukaje baki ga ba abin tausayi,ko magana bata iyawa sai dai idanu,don ta zubar da jini sosai ai yanzu da sauƙi".

Tuni jikina ya hau tsuma na idanuwa na suka kawo ruwa,don komai idan aka saka Rashida aciki mai mahimmaci ne,tun muna ƙanana idan ɗayanmu ba shida lafiya to zaka samemu cikin wani hali.

Maryam ce ta dinga rarrashina,amman duk da haka ban daina kukan ba,tunanin halin da Rashida take ciki shine yafi tsayamin,na ce"insha Allah zanje in duba ta fatanmu dai Allah ya bata lafiya me É—orewa,na faÉ—i hakan muryata na rawa.
***

Har washe gari jikina duk babu daɗi,na kira wayar yaya Aliyu mijin Rashida yafi sau 5 amman bai ɗaga kiran ba,ƙarshe dai na haƙura.

Na fito daga wanka kenan na jiyo ƙarar tsayuwar mota,jikina yana rawa na leƙo na hango Yaya Bilal yana fitowa daga cikin motar,kayan da ya sanya sunyi matuƙar amsarsa,kyaunsa ya ƙara fitowa sosai,hawaye masu zafi suka fara ambaliya acikin idaniyata na saka hannuna na goge,ban gama ida abinda na ke ba na hango Jidda ta fito daga sashenta taci uban riga da wando english wears ya yi matuƙar kamata,ta rungume Yaya Bilal shima ya rungumeta sosai,kamar wani zai ƙwace ta,tuni wani abu ya tsayamin azuciyata kamar wani mashi ko kuma guduma,tsananin kishi na yakai ƙarshe da sauri na saki labulen,ya yinda shi kuma ya ɗauki jidda kamar ƴar tsana suka yi ɓangaren Bilal ɗin.

Na ƙwanta akan gado na hau aukin kuka,wanda ayanzu ya zamarmin kamar wani abinci,ina da komai a store ɗina,don tun kafin a kawo min gara ya ajjewa kowaccenmu abinci,fridge ma cike ya ke da abubuwa na more rayuwa,ni dai mijine ya zamarmin wahala don tunda muka yi aure ban ƙara sakashi a ido na ba sai yau.

Ina cikin wannan yanayin naji ana buga ƙofar ɓangare na,jiki na duk babu ƙwari nazo na buɗe,wanda na gani atsaye ne yasa ni waro idanuwa na waje.. .✍🏿

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.