Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 76 of 90
murmushi na yi sannan na ce"kada Ka damu nima duk wannan bidi'ar bata gabana albarkar auren shi na keso".sosai na burgesa amman fa muna cikin zancen naji alert Ɗin kuƊi awayata na ce"habibee naga ka turomin kuƊi me zanyi dasu haka"?.murmushi ya yi sannan ya ce"ki yi wani abin dasu,amarya ta me sirrin kyau".ya faƊi hakan yana murmushi,bai bani damar Ƙara magana ba ya yi shigewarsa cikin mota ya yi gaba.
Sosai na keson shahid,ba don kuÆŠinsa ko kyau ba,a'ah sai don tsare mutuncinsa,sam bai taÆa koda taÆa hannuna da sunan wasa ba,balle kuma wata maganar banza,muna mutunta kanmu mu duka,anan na ke jan hankalin Ƴan mata da zawarawa adinga riƘe mutunci da kyau,saboda ke mace duk abinda ki ka yi bai Æoyuwa namiji kuwa ko zai yi sau ÆŠari ba'a Ganewa,kuma a musulunce ma hakan sam ba shida kyau kuma ma ba tarbiyya bace.kuma matuƘar ki ka sadaukar da mutuncinki ga wani to fa wannan mijin koda tare ku ka yi lalatar bazai taÆa ganin darajarki ba,balle kuma akaiga zancen mutuntawa,don shi aure anfison ayisa da ganin mutuncin juna.
da kai na na ware kuƊi masu yawa aka sakewa hajiya kaka sabbin kayan Ɗaki aka yi mata sabon fenti,mama na itama aka sake yi mata furnitures duk da basu daƊe ba,sannan mama ta faƊawa babana duk kuƊin da shahid ya ke bani,baiyi mamaki ba ko kaƊan don yaron yasan tarihinsa tun farko har zuwa yanzu,mahaifiyarsa da mahaifinsa suna da kuƊi sosai kuƊi kuma masu mugun yawa,shi da kansa shahid a iya nigeria ma yana da company's sunfi ashirin,ga kuma na Ƙasashen waje,uwa uba kuma likita ne me zaman kansa me kuma lasisin kowacce Ƙasa,likitan zuciya ne shi,mahaifiyarshi kuma unguwar xoma ce.kuma ba Ƙaramin kuƊi suke samu ba.
ranar daya rage saura Ƙwana biyu gidanmu ya cika Æam kamar auren budurwa,son hatta ankon biki,sai da shahid ya turomin kuÆŠi wai abawa kowa,wai su haka suke yi naƘi amsa sai gashi ya lallaÆa yaje wajen hajiya kaka,itama da farko taƘi amsa amman da taga ransa ya Æaci sai ta amsa,ai kuwa kowa sai daya samu ankon biki,ranar Ne kuma amminsa tazo gidanmu mata mai mutunci da sanin darajar mutane,ta ÆŠakko wata mata wai za ta yimin gyaran jiki na larabawa.
daga ganin matar ma balarabiya ce wataƘil ÆŠakkota aka yi,,harda Ƙanwarta tazo ita ammin,duk suna da mutunci sosai naƘi fitowa wai ina jin kunyarsu ta ce"a'ah khairat mufa bama jin wannan kunyar gwarama tun yanzu ki saba don shahid ba shida kunya wallahi".murmushi kawai na yi ai kuwa aranar aka fara yimin gyaran jikin,wowo hmm wai ko tsagar gida ma hanani fita matar ta yi sai dai ina ÆŠaki ina shan a/c,Mutanen gidanmu suka dinga zuwa ganin ammin shahid,shima tun daga ranar ammin ta hanashi xuwa saboda gudun saÆawa Allah don taga yadda Ƙirar khairat ÆŠin take,ba kowani namiji ne xai iya kallonta ya kyale ba,duk da ta yarda da ÆŠanta mutum ne me kana kansa sosai,da tsantsae tsoron Allah,,shiyasa a kullum take godewa Allah da kyautar da ya yi mata na samun ÆŠa kamar shahid,daman kuma ba yawan yara akeso ba albarkarsu ake nema.
kullum muna maƘale awaya ni da shahid ana zuba soyayya na lura su larabawa mayun soyayya ne,kamar laila majnun.
Baba na ya saka aka kirawo masa Bilal ya ce"Bilal kasan me yasa nasa ka aka kirawomin kai?".girgiza kawai ya yi,idanuwansa sunyi ciki duk ya rame abin tausayi ya ce"ina son ka yarda da Ƙaddara me kyau ko mara kyau,ka cire komai aranka kamar ma ba'ayi ba,kai Ɗinnan dai yayan khairat ne kuma uban ƳaƳanta har huƊu,to kaga aƘwau akaƘa me Ƙarfi a tsakaninku,don haka yanzu ma na kiraka ne don ka zamo waliyyin khairat,don ance babban wa uba koda ace yanzu mu faƊi mu mutu kai ne babansu su duka".
sosai wata zufa ta shiga tsattsafo masa,ya goge ta cikin dauriya da Ƙarfin hali ya ce"ba bu komai baba na gode da bani shawara da ka yi."baba yaji daƊi sosai suka cigaba da hirarsu amman can cikin zuciyarsa yana jin wani abu yana yi masa yawo sosai,ranar dai Bilal kusan Ƙwanan zaune ya yi,saboda tsananin tashin hankali,gobe khairat Ɗinsa xa ta Ɗaura aure?da wani ba shi ba?za ta tafi gidan wani?yanzu shikkenan sun rabu har abadan?tuni ya dinga kuka kamar ba shi ba,tabbas yanzu yaga illar rashin yin bincike kafin Ɗaukar mataki,kuma yanzu yaga illar yin saki har uku,da Ɗaya ya yi mata ko biyu da yanzu suna nan zamansu gwanin sha'awa.
Anan nake jan hankalin maza akan mu kula mu daina yanke hukunci cikin fushi,an sani kuma an yarda ita rayuwar aure tana zuwa da Ƙalubale daban daban kuma sai anyi haƘuri sannan ake samun abinda ake so,don haka mu kasance masu haƘuri ako ina kuma aduk halin da muka tsinci kanmu.
to nima anawa Æangaren hakan ta kasance amman tsaÆanin tunaninmu ba ÆŠaya bane da Bilal ni da Shahid ci ke muke da zumuÆŠi da son kasancewa da juna,na tuna gobe iyanzu ina rungume jikin mijina abin alfaharina,ina matuƘar son shahid son da bai ko na yaya Bilal ba,don sai yanzu na gane ashe lokacin ban san ma wani so ba,sai yanzu nasan so don shahid ya shayar dani madarar soyayya.
******
Washe gari na chaÆa adona cikin wata doguwar riga wadda shahid ya kawomin me shegen kyau,kalar skye blue ta tasha kwalliya har ya gaji,kowa sai bina da kallo ya ke kamar wata acikin zarah,gidanmu ya cika Æam,Ƴan huÆŠu ma sunsha Ƙwalliya sosai da skye blue ÆŠin shadda aka dinga yi mana hotuna dasu,don tun sassafe ya aiko da wani me hoto wanda ya Ƙware yasan kuma aikinsa,kuma baƘar fata ne amman ya iya hoto sosai yasan kuma aikinsa,don duk wanda aka yiwa hoton sai ya yi murna saboda hotunan suna fita tarwal sosai.
iyaye na guda 12 duk anyi mana hotuna dasu gwanin sha'awa ga Ƴan huƊu agaba suma sunyi kyau.
Ɗaki na ya cika da Ƙawaye sosai,Mukaji shigowar angwaye bayan an Ɗaura aure,da sauri nadiya ta ce"khairat tashi ki leƘa kiga angonki sai jin kunya ya ke".
Ai banji kunyar ba kuwa na tashi ta saman bene ina hangosa,don daman baba na ya bamu mukulli muka haye saman,babu hayaniya babu komai...... .âœðŸ¿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯â€â™€ï¸ðŸ‘ŽðŸ‘‡ðŸ‘‡*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.