Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 90 of 90

Sai na tara yanzu zata haifa,babban É—an gidan captain Khalil wato ibrahim wanda yanzu ya ke da shekara ishirin da huÉ—u shine ke son iman,don ya dage sosai shi khairat ya keso,kuma alhmdh yarone me hankali yana da nutsuwa kuma yana da aikin yi.don yanzu har mahaifinsa ya samo masa aiki a babban asibiti lilitan mata wato ghanychology.

Ina zaune naji jiniyar mota ta tsaya,irfan da ke min tausa ya riƙe hannuna muka tashi,Arman na hango da mahaifinsa.wanda mahaifin nasa yaje ya ɗakkosa a makarantar sojoji da ke kaduna. Shi daman tun tasowarsa ya keson aikin mahaifinsa wato soja.

Da sauri yazo ya zo ya rungomeni yana murnar ganina.ina ta murnar ganin ɗana,Yaya Bilal wanda yaci wankan shadda kamar wanda be fara manyanta ba.don haryanzu shekararsa arba'in da baƙwai.don haka har yanzu kamar saurayi na ke ganin abina,don gaskiya jikin yaya Bilal me kyau ne,kullum sai inga kamar ana ƙara masa kyau.

HaÉ—amu ya yi dukkanmu ya rungumemu,mu duka iman ce kawai bata nan tana skull cikin farin ciki na kalli iyalina ina jin wani irin mugun daÉ—i har cikin rai na.

Adaren ranar na haihu É—a namiji me kama da yaya Bilal,bayan anyi suna ina zaune ina shafa mai ya shigo,ya ajjemin wata takadda kan cinyata.na kallesa cikin tsoro.amman na daure na buÉ—e.da sauri na tashi na rungumesa.ya biyamina hajji harda umra nida yarana baki É—aya.daman kuma su Mamana da baba Abdullahi suma zasuje.

Na rungumesa na ce"Allah na gode maka daka bani miji nagari abin son kowacce mace.na gode mijina Allah ya albarkaci dukiyarka.ya albarkaci yaranmu dana al'ummar musulmi baki É—aya."

Bai bari na ƙarasa ba ya yi kan faffaɗan gadonmu me kyau.muna dariya cikin nishaɗi.
*Alhamdulillahi*

Hmmmm laifin daɗi ƙarewa anan na kawo ƙarshen wannan littafi nawa,me suna ABIN CIKIN ƘWAI.gaskiya ni kai na dana rubuta littafin naji daƊinsa sosai,saboda wasu darussa dani kai na dana Ƙaru,don labarin na gaske.

Fatana Allah ubangiji yasa mu amfana da abinda ke cikinsa,abinda na rubuta dai dai Allah ya bamu ladan baki ÆŠaya,akasin haka kuma Allah ya yafe mana baki ÆŠaya.

HaƘiƘa babu abinda zan ce wa ubangiji sai godiya,saboda yadda kuka nunamin soyayya da Ƙauna Allah yabar zmnci amin.

dafatan zaku biyoni asabon littafi na,wanda har sai yafi abin cikin Ƙwai haƊuwa,don shi labarin ba na mutum Ɗaya bane,labarin xai zamo kamar drama don zai zamo akan mutum uku ne,waƊanda suka sha gwagwarmayar rayuwa.

SUNAN LITTAFIN👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*MICIJIN SARI KA NOƘE*

DUK WANDA YASAN KARIN MAGANA YASAN ABINDA LITTAFIN YA KE MAGANA AKAI.KU DAI KU BIYONI DON JIN YADDA ZATA KAYA.

*KU KASANCE DA GAWURTATTU BIYAR INSHA ALLAH SUN SHIRYA TSAF DON DAWO MUKU DA SABBIN LITTAFINSU,AMMAN SAI MUN HUTA NAN DA ÆŠAN WANI LOKACI.

*TAKU HAR KULLUM*
*ummu maher(miss green)*

don Allah duk wanda ya karanta littafin nan yaji daÉ—insa,ya yimin addu'ah akan Allah yacikamin burina.

Ilove u too all.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.