Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 36 of 90

Na ce"wai ni Rashida ya naga kin ƙara wani fari ne da cika idanuwa?".Dariya ta yi sannan ta ce"hmm ai nan da 7 month zaku zo suna".

Rungume ta na yi ina dariya na ce"ah ki ce mun kusa zama manya?".

Ta ce"ni kuwa ya naga ko É—an gyaran amare baki fara ba?ai wallahi Khairat baki da mutunci ace zaki auri yaya na amman sai a duniya na ke ji"?.

Kallonta na yi ƙuri na kasa ce wa komai,mamako da kuma ruɗu suka cika ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwata,na ce"hmm wai Rashida me yasa ki ka fiye wasa ne?Ta yaya za'a ce za'ayi biki na amman baki sani ba?"a'i kema kin san ba zai taɓa yiwu ba".na faɗi hakan ina kallonta.
Sosai mamaki ya game ƙwaƙwalwar Rashida ta ce"wai kina nufin baki san za'ayi aurenki nan da sati biyu masu zuwa ba?".Ta faɗi hakan tana kallona.

Da sauri na tashi tsaye na ce"haba Rashida kada ki sanya zuciyata ta buga da waÉ—annan kalaman na ki maras tushe?Don Allah ki faÉ—amin abinda ke faruwa"?.

ÆŠan huras da numfashi ta yi sannan ta ce"hmm khairat nasan za kifi kowa farin ciki dajin wanda zaki aura,Yaya Bilak shine wanda zaki aura,har an kai kuÉ—i da komai tun wata uku da suka wuce".sosai na waro idanuwa duka waje na ce"Wai Rashida kin tabbatar abinda ki ke faÉ—amin gaskiya ne kuwa"?.Kallon banza ta yi min sannan ta ce"ai kin san na saba yi miki haka"?.

Rasa tudun da fawa na yi na ce"lallai Rashida ni mai sa'ace kiga duk tsayin shekarun dana yi da dakon bawan Allahn nan azuciyata ashe nan kusa zan aureshi".na faɗi hakan ina rungume da filo a ƙirjina,Rashida ta ce"ah to kinga mune manyan ƙawaye kuma ƙannan miji ba?".Ta faɗi hakan tana kai min dukan tsokana.

Sai dai tun yanzu na fara tunanin wani irin zama zamuyi da Yaya Bilal?Yadda ya tsaneni kamar mutuwarsa?lallai aƙwai babbar matsala a wannan rikitattan zaman na mu.

Ranar dai na yi yinin jin daɗi,Rashida ta ce"baki tambayeni mutuniyarki Nadiya ba"?.murmushi na yi sannan na ce"hmm Rashida ni fa yanzu gwara inyi nesa dasu don zama dasu ba alkhairi ne arayuwa ba,kina ganin dai halin dana fa ɗa saboda su,ni tunani na ma kada Yaya Bilal ya zargeni akan hakan kinga bazai taɓa ganina da mutunci ba".?Na faɗi hakan kamar zanyi kuka.

Cikin tausayina Rashida ta da fa kafaÉ—a ta sannan ta ce"Khairat kada ki yi wannan tunanin,ba kowani tunani É—an adam ya ke sakawa a zuciyarsa ba,saboda kada wataran ya rasa tunanin mw zai yi,don shima tunanin da na shi lokacin,kuma yana da kyau ki kyautata kyakkyawan zato a karan kanki,kada ki yadda da duk abinda mutane zasu faÉ—a akanki,ke dai tunda kin yadda da kanki shikkenan,sauran ki barwa Allah zai miki sakayya da gaggawa."

Goge hawayen fuska ta na yi sannan ce"Hmm Rashida wannan ƙazafin da aka yimin ya kasa gogewa acikin zuciyata,sunyi min illar da bazan taɓa warkewa ba,sun cutar min rayuwata,sun wargazamin farin cikina,ina rayuwa da mahaifiyata da ƴan uwana cikin aminci da kuma ƙaunar juna,amman yau duk ina wannan Rashida?Ya tafi har abada bazai dawo ba".Na faɗi hakan ƙwalla na fitowa daga cikin idanuwa na.
Sosai Rashida ke bani baki sannan ta ce"kibar komai ba komai ba,insha Allah muna nan zaune zakiga sakamakonsu,insha'Allah khairat ba zaki taɓa taɓewa ba,komai ya yi farko yana da ƙarshi,yanzu bikinku tare za'a haɗa dana yayyin ki biyu".

Tuni na fito da idanuwa na waje na ce"ikon Allah da kuma su waye?".Dariya Rashida ta yi sannan ta ce"hmm buɗe dai kunnenki sosai kiji,Yaya Salim da Mero,Yaya Aliyu da Maryam".har dafe ƙirjina na yi sannan na ce"oh ni wannan aure aƙwai rikici to shi Yaya Salim daman yana son mero ne?".Dariya Rashida ta yi sannan ta ce"ina a'i wannan duk haɗin tsohuwa Hajiya kaka ne".

sosai na ke dariya sannan na ce"caɓɓi lallai Yaya Salim har kuka sai ya yi,saboda shi arayuwarsa yana son mace ƴar boko,to yaya kenan?tunda i'ta dai mero ko aji ɗaya bata taɓa shiga na boko ba".

Nan dai muka cigaba da hirarmu har ta rakoni waje,ta ce"khairat amman na yi mamaki da bro Aliyu bai gaya miki zancen aurensa ba"?.Dariya na yi sannan na ce Hmm wata ƙila baya son asani ne?kin san halin matarsa,ni fa wallahi ya ƙara ɗin ma saboda Anty khadina sai a hankali wallahi,ni ɗinma ɗaga mata ƙafa kawai na ke saboda matsayinta na matar yaya na,saboda san bata iya magana ba".

Rashida ta buÉ—e baki za ta yi magana sai ga Yaya Aliyu mijinta da Nadiya ta wani hakimce agaban mota.sosai na yi mamakin ganin hakan na kalli Rashida na ce"ikon Allah sai kallo su kuma yaushe suka zama masoya har haka?".

dariya Rashida ta yi sannan ta ce"haba Khairat kamar baki san Mama iklima bane?sun neme sa ne kuma yanzu gashi sun samu,ni dai Allah na saka agabana kullum goshi na yana ƙasa ina roƙar Allah ya fiddani daga zaluncinsu ya bani haƙurin jure duk wani cin kashinta,da i'ta da Yaya Aliyun".

suna ƙaraso wa muka gaisa da Yaya Aliyu ya amsa da fara'arsa muna cikin gaisawa Nadiya ta ce"honey zo mu tafi jiri na keji bana son tsayawa".A'i da sauri naga Yaya Aliyu ya bita suka yi saman bene.

Har suka hau ban daina kallonsu ba na juyo na ce"Rashida Alkah ya baki haƙurin jure komai, ya ƙwato miki mijinki a hannunki".

Muka yi sallama akan za tazo waje na awannan satin,abin mamaki ina fitowa daga gidansu Rashida naga wannan motar a ƙofar gidan,na buga wani uban tsaki kusan awata huɗu amman suna zaman jiran gawon shanu.

Hanyar titi na yi ko waiwayonsu banyi ba,har na tsayae da keke napep kawai sai naga wannan mutumin ya fito yaje wajen me keken ya nuna masa wani kati,ai da gudu mutumin ya tafi,ni kuwa haushi duk ya kama ni,na gallawa mutumin harara wani a mummurÉ—e dashi,na ce"wai don Allah bawan Allah sata na yi muku kome?kun dameni sai bina kuke?".

Murtuke fuska ya yi sannan ya buɗe baki zai yi magana,aka buɗe murfin motar,sosai na buɗe idanuwa na ina kallon wanda ya fito daga cikin motar ƴar pos ɗin dake hannuna ta faɗi a ƙasa.

*Miss green ce*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.