Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 33 of 90

Mahaifiyar mama i'ta ke rarrashin mamanmu su yaya Salim É—in ma kuka suke sosai,sun kasa rarrashin mama don basu san ma me zasu ce mata ba,don suma neman masu rarrashin suke.

Tsakar dare na fara É—an motsa É—an ya tsana yaya Salim da ke gefena ya É—aga fuskarsa da sauri don bai san sanda bacci ma ya É—aukesa ba,mama da ke kan sallaya ta tashi da sauri sukayo kaina su duka,kakarmu,yaya Aliyu,mama,yaya Salim,maher.dukkansu suka rufu akaina suna yimin sannu.

Murna da farin ciki suka cika zuƙatan waɗannan family,hawaye na fitows daga fuska ta na ce"mama na".da sauri ta amsa tana shafa fuskata i'tama kuma tana hawayen.

Na fara samun sauƙi sosai don ƙwanana uku suka sallameni,ita ma anty khadija an sallame ta muka wuce gida baki ɗaya,sai dai tun a asibitin sai da yaya Aliyu da khadija suka hau sama suka faɗo,don muraran ta nuna bata son mu koma gidanta,yaya Aliyu ya ce ai kuwa bata isa ba sai dai ita tabar gidan don duk duniya bashi da kamar mahaifiyarsa da kuma ƙannansa musamnan khairat wacce take mace.

****

"Oga mun gano yarinyar da wannan ɗan matsiyaciyar ya ke so,mu kashe ta ne ko kuma mu barta?".ce war ɗaya daga cikin yaran Alhaji Damas,baƙi ƙirin dashi kamar zunubi.

Sassanyan lemo Alhaji Damas yasha sannan ya ce"ni bana taɓa yin abuna ba tare da ba yi wa mutum mai kankat ba,ba zaku kashe ta amman zaku yi mata ƙanin mutuwa ta yadda zai san ce wa ni dashi ba ɗaya bane,ta yaro ƙyau take ba ta ƙarko."ya faɗi hakan yana miƙewa tsaye yaran nasa suka bishi abaya.yana saƙa mummunar ƙuduri akan Jidda wacce ta kasance budurwa ga Bilal.

Zama na da mahaifiyata yasa yanzu na É—an fara sakin jikina,ga shi ko da wasa bata bari na in zauna ni kaÉ—ai saboda abinda likita ya ce kada a barni ni kaÉ—ai saboda b.p É—ina ya hau sosai,kuma duk ta silar tunanin.

Ranar suna Yaya Aliyu ya ce baza ayi suna ba,saboda yasan abinda hakan zai kawo,barka ma kawai da ƴan gidansu sukazo sai da akaso ayi faɗa,wai mama tazo ta zauna gidan ɗanta wai ta ƙwaso tsohuwarta inyamura sun taho tare.

Wannan magana ta tsayawa mama sosai,a take mutuwar aurenta ta dawo mata sabuwa fil,hawaye masu zafi suka zubo mata,lallai su mama iklima sun cuce amman babu komai kansu suka cuta don har awajen Allah ta fisu tunda dai ita bata taɓa cutar dasu ba.

****

Hajiya Inna ta kalli ƙawarta hajiya kaka ta ce"yanzu Ramatu haka zamu yi ta zama kina tare da wannan ciwon da aka rasa gane kansa,kullum abu ƙara gaba ya ke ni wallahi gani na ke ma kamar a mafarki".ta faɗi hakan cikin damuwa.

Mero da ke gefen Hajiya kaka tana É—an yi mata tausa,itama duk shirmenta yanzi ta ajjesa a gefe tunda hajiya kaka ba lafiya.

Alokacin su Baba Abdullahi suka shigo,Baba Bashir,Baba auwalu Baba ƙasim, suka zauna suna gaishe da hajiya inna ta amsa itama tana musu ya mai jiki,suka amsa mata da sauƙi sannan hajiya inna ta ce"a'ah lafiya na ganku ku dukanku kunsha manyan kaya haka?".

Baba Auwalu ne ya ce"ai shi yaya Abdullahi ba tare muka fita dashi ba,yanzu dai shigowa ne dai muka haÉ—u dashi to shine ya ce daman zaizo duba umma ne,amman mu mun kai kuÉ—in Bilal ne har da saka ranarsa."

"Ikon Allah to Allah ya sanya alkhairi".
Suka amsa da amin suna kallon mahaifiyar tasu wacce ke kallansu itama har zuciyarta tana jin daÉ—in ganin kan Æ´aÆ´anta a haÉ—e.

Bakinta ya fara motsi alamar tana son yin magana,mero ce ta lura da hakan ta ce"la kaka nason yin magana".ta faÉ—i hakan da farin ciki don ta damu da ciwon hajiya kaka.

A hankali Baba Ƙasim ya saka kunnensa dai-dai bakin Hajiya kaka,jin abinda take faɗa ne yasa ya kalli ƴan uwansa da sauri.

Kuyi haƙuri gobe da safe zakuji update me yawa.

*Miss green ce*

35🟩36

. . . .kallon mamaki suke ta bin É—an uwansu dashi sannan Baba Abdullahi,ya ce"lafiya naga duk hankalinka ya tashi?me ya faru me ta faÉ—a maka?".ya faÉ—i hakan yana kallon É—an uwansa.

Wata uwar zufa ya sharɓe sannan ya ce"ta ce wai ko da ta mutu a cika mata burinta na auran Bilal da kuma khairat".ya faɗi hakan yana sunkuyar da kansa.

Murmushi Baba Abdullaho ya yi sannan ya ce"babu komai ai mu bamu i'sa mu tsallake duk wani abu da tace ayi ba,fatan mu dai Allah ubangiji ya tashi kafaÉ—arta".ya faÉ—i hakan cikin damuwa sosai don da za'a dawo da ciwon jikinsa da ya fi kowa jin daÉ—in hakan,don mahaifi yafi gaban wasa.

Baba ƙasim ya ce"ammam kana ganin yaya wannan haɗin ya yi kuwa?kana ganin gashi shi hae mun riga da mun kai masa kuɗi,gashi kuma ta yi maganar khairat?kuma ga abinda ya faru da rayuwae yarinyar?".

murmushi Baba Abdullahi ya yi sannan ya ce"hmm Ƙasim kenan?me ye amfanin gida bai ƙoshi ba akaiwa dawa?ai ko aure ne dashi ba rana aka saka mai ba sai ya aure ta,tunda ba shi ke da kanshi ba mu muka haifesa,kuma zancen abinda ya faru da khairat ni ban yarda ce wa hakan ya faru ba,sannan ko da ma ya faru ɗin dole ne sai ya zauna da ita tunda dau ita ƴar uwarsa ce,idan har bai rufa mata asiri ba waye zai rufa mata?"ina tambayarka ƙasim".?shiru baba ƙasim ya yi don yaga yayan nasu ya ɗau zafi shiyasa ya yi shiru ya sakawa abin albarka kawai,tunda dau bashi da ta cewa don su duk abinda yayansu ya yanke shi suke yi basu taɓa saɓa masa bisa umarninsa ba,yadda kasan mahaifinsu don kunsan ance babban ya uba.
Hajiya inna ta ce"hmm ni wallahi wannan haɗin har zuciyata daɗinsa naji,tun da dai wannan yarinyar ai ƴar uwarsa ce,ai wannan haɗi ya yi daɗi wallahi".ta faɗi hakan zuciyarta fes,don ko yanzu Hajiya kaka ta nunawa matan ƴaƴanta darasi akan sharrin da suke ƙullawa khairat,don haka tasan zuciyoyinsu kamar zasu fashe za ta yi,kowaccs mata agidan so take Bilal ya ce yana son ƴaƴansu amman shi ya yi kunnrn uwar shegu harkokinsa kawai ya ke.

To wannan maganar sosai ta hargitsa ƙwanyar ƴan gidanmu,musamman ma waɗanda daman ba so na suke ba,daga ni har mahaifiyata su mama iklima dukkansu jikinsu ya yi sanyi,wato ita wannan yarinyar duk muguntar da suka yi mata,ƙarshe sai dai ta zamo mata alkhairi,inji masu iya magana suka ce hassada ga mai tabo taki ce.

Daga ni har mahaifiyata babu wanda yasan wannan maganar,saboda tunda mama tazo ko hirar Æ´an gidanmu ba ballan tana ma har muji komai.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.