Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel
Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt
Chapter 50 of 90
Sauke numfashi na yi ina ganin kamar baxan iya wannan abubuwan duk da ta faɗomin ba,na kalle ta na ce"ni wallahi mmn junior kunya na keji,idan na gansa sai inji kamar ƙasa ta tsage na shige ciki,wallahi ina jin nauyinsa".
Kallo na sosai ta yi cikin nutsuwa ta ce"hmm ai kuwa khairat ba zaki taɓa fita daga cikin wannan matsalar ba,ki cire duk wani nauyi da jin kunyarsa.ki nuna masa kema macece,sannan idan ya shigo hannunki ki nuna masa jan aji sosai irin namu na mata,kada ki sakar masa kanki kamar wata jaka,don Allah khairat ki nutsu ki karɓi mijinki a hannu,wannan zaman da kike me aikin gidan nan ma ta fiki matsayi,don haka ki daure daga shi har jidda ɗin ki nuna musu baki damu dasu ba,sannan ki yi duk yadda za ki yi ki karɓe mijinki chas a hannunki,sannan wannan sirrin na ki ina so ya tsaya daga ni sai ke,don bana son kowa yaji".
Murmushi sosai na yi cikin dakiyar zuciya na ce"insha Allah anty zanyi yadda ki ke so".murmushi ta yi muka cigaba da girkin namu.
Muka zuba a babban faranti muka fara cinsa cikin nutsuwa har muka gama,na koma kitchen na wanke kayan tas.na dawo muka hau hira,ta ce"khairat gobe zan aiko ƙanwata ta kawo miki wani turare,ki daure ki yi amfani dashi don Allah kada ki bani kunya."
ÆŠaga mata kai na yi ina jin daÉ—in haÉ—uwa da ita,don ba don ita ba da ban san yaya zanyi ba,don yadda na ke tsoron yaya Bilal ko Babana bana tsoronsa haka.
Halisa tana komawa gida ta shiga haɗa abubuwan da zata aikowa da Khairat,har wasu shegun ƙananun kaya waɗanda ra siya ƙwanan nan wanda bata yi amfani dasu ba,har kayan bacci duk da tasan khairat ɗin na dasu,ta haɗa su duka ta aika gidansu akira mata ƙanwarta Xeenatu.
Turaren kuma oder É—insa ta bayar aka kawo mata,don daga saudia ake kawo turaren,halartaccen turare ne wanda ake shafawa ajiki musamman don jan hankalin mijinki".
Mai suna miskil Zawaaj,turare ne mai matuƙar sanyin ƙamshi da jan hankali.
****
ai kuwa ina dawowa daga makaranta na tarar har Xeenatu tazo,bayan mungaisa ne take sanarmin ita ce wadda Halisa ta aiko,murmushi na yi mata muka ƙara gaisawa sosai,an ciko min wata ƙatuwar bakko wai duk kayan ne aciki,idan ban gane ba in kirata awaya.
Naji daɗi sosai tun Xeenatu na nan na fara gabatar da wasu abubuwan,ni da kaina sai da abin ya yi min cif sai naji jikina duk asake kamar nasha wani abu da zai ƙara min wani armashi ajiki na.
Na saka wasu ɗamammun riga da wando,wanda ni da kaina sai dana ji kunyar yin hakan,dirina ya fito ɗas ɗas kamar wata ƴar bebi,hmm tuni na ɗauko turaren da ta aikomin na bulbulasa yadda ya kamata,tuni jikina ya kama ƙamshi sosai,na saka after dress akai,saboda zan raka zeenatu na yi kyau sosai,na samu wani plat ɗin takalmi na wanda ya yi min kyau,na rako ta muna hira.
Dai dai nan hancin motar Yaya Bilal ya danno na yi gefe ina wata irin tafiya ina rangaji tare da girgiza jikina kamar wata macijiya,ko kallon saahensa banyi ba na fara taunar cinguim ɗin bakina yana bada ƙara ƙararas ƙararas,ina hangosa naga yana yimin wani kallon cikin ƙasa,sai da ya cire glass ɗinsa yana wani yimin kallon ƙasa ƙasa.
Tuni na yi gaba nazo dai dai inda ya faka motarsa na wuce ko kallonsa banyi ba,Har na raka Zeeenatu na dawo na wuce har ta kusa dashi ina girgiza mazaunai na wuce,zuciyata sai bugawa take sai dai wani É“angaren na zuciyar tawa yana bani Æ™warin guiwa..... .âœðŸ¿
07068606171
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯â€â™€ï¸ðŸ‘ŽðŸ‘‡ðŸ‘‡*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_*Miss green ce*_🤙ðŸ¿
[23/09, 16:23] Miss GreenðŸ€: *57. . . . . .58*
Da sauri ta ɗaga hannayenta za ta mare ni,na riƙe hannunta da ƙarfu har sai da ta yi kuka,sannan na yasar da ita awajen na cigaba da motsa jiki na,duk yana kallon abinda ya faru,ya taso ya kalleni ransa aɓace ya fara magana"ke baki da hankali ne zaki jefar da ita?".
kallonsa na yi sosai sannan Na ce"ikon Allah yanzu kai baka ji kunya ba?kazo wai zaka shigarwa matarka faÉ—a?ita baka ga abinda ta yi ba?wato ni gani mara galihu sai ta mareni ta takani yadda take so ko?to wallahi ahir É—inku daka kai har ita,don ba Æ´ar aiki aka kawo muku ko baiwa ba".
Ganin yadda na yi mai ne yasa yaja hannun jidda suka yi sashenta,ta zube kan tiles tana ce wa"Allah ya isa na wannan muguwar yarinyar mai kama da basamudiya ta yi min targaÉ—e".
Da sauri Bilal ya ce"ke kada ki ƙara ce mata basamudiya,don ƙanwata ce kinga kuwa zubina tayo".da sauri Jidda ta tashi cikin fushi ta ce"hmm ai wallahi tallahi wannan matakin daka ɗauka agidan nan ba zai maka kyau ba?ai naga ce wa kayi ko kallonta ba zaka yi ba,ashe duk ƙaryar bogi ce.har da yimin alƙawari gashinan tun ba'a kai ko'ina ba ko'ina ba kayi fatali da alƙawarin daka ɗaukarmin".
Kallon banza ya yi mata sannan ya ce"Jidda kada fa ki faɗamin zancen banza,wannan yarinyar itama matata ce kamar yadda ki ke,kuma inaso ki saka aranki daga yau zan koma wajen matata,in neme yafiyarta akan duk abinda na yi mata,haba ai na shiga haƙƙinta ma,ni narasa me ya shiga kaina yasa na yi fatali da ita na manta da ita sam,to zaluncin nawa bai kai nan ba,ke bakya tunanin in mutu in tashi da shanyayyen gefe?ke murna zaki yi ko?".
"Hhhh ai wallahi Bilal baka isa kace yau zaka koma wajen wannan Æ´ar iskar yarinyar ba?ai ba haka muka yi da kai ba?Bilal yau ka nuna min ce war namiji baÉ—an goyo bane".ta faÉ—i hakan tana jan kwalar rigarsa.
Fincike fici ficin hannayenta ya yi tayi gaba tayi baya kamar za ra faɗi,tana hawaye ta ce"Allah ya isa tsakanina da kai Bilal wallahi sai Allah ya sakamin,ƙara fincoka ta ya yi kamar kayan wanki sannan ya ce"ki shiga hankalinki jidda sam ni ban zama lusari har haka ba,da xaki mayar dani sa'anki duk maganar da tazo bakinki ki faɗamin ita,ita khairat ɗin da ki ke zagi bata fiki ba?,ki duba sosai ki gani."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.