Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 77 of 90

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:30] Miss Green🍀: *🏮ABIN CIKIN ƘWAI🏮*

littafi na 3

*by✍🏿*
Ummu maher(miss green)🍀

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

*Sirrinki👂🏻🌈*

*Ciwon basir*

abubuwa da yawa suna kawo basir kamar haka👇🏻👇🏻

*Yawan cin maiƙo*
*yawan cin yaji*
*shan lemon ƙwalba*
(abu me gas)
*shan zaƙi*
(chocolate)

abubuwan da ya kamata mai ciwon basir yaci👇🏻👇🏻

*Lemon ɓawo*
(fruit)
*abinci mai ganya*
(latas,cabbage d srnsu).

basir yana lalata mace sosai don haka ki kiyaye cin abinda zai kawo miki basir.
---------------------------

89. . . . . . 90

. . . . . . .ina ganin ya taho inda muke da sauri na matso inda Shahid ya ke,ina murmushi sosai abin ya bawa Bilal haushi ya daki gaban motarsa da hannunsa saboda tsabar takaici ya shiga motar ya wucesu fuuu,aka buÉ—e masa gate É—in ya shige,yana jin wani irin bugawar zuciya kamar zata fito waje.

Ko kallon ƙurarsa banyi ba Shahid ya ce"Hayatee dafatan kina lafiya"?.murmushi na yi na ce"lafiya klau dafatan kaima haka"?.na lura yaji daɗi sosai da yadda na karɓesa ya kira amminsa awaya muka gaisa.bai cemin in shiga cikin motarsa ba nima banyi ƙoƙarin shiga motar tasa ba don daman shiga motar saurayi bata cikin aƙida ta,kuma a musulunce ba dai dai bane yin hakan rashin tarbiyya ne.

Sosai muka yi hira harda dariya zuciyata ta nutsu dashi sosai.kuma ya cemin sunyi magana da Babanmu zai aiko gidanmu a saka rana nan da wata biyu masu zuwa,na yi murmushi na ce"kai gaskiya wata biyu ya yi kaÉ—an".murmushi ya yi shima sannam ya ce"awaje na baiyi kaÉ—an ba Hayatee ni da zai yiwu ma yanzu a É—aura mana aure kawai,da nafi kowa more aure".

Dariya maganarsa ta bani na ce"haba sai kace wata ƴar tsana"?.haka dai muka cigaba da hirarmu gwanin sha'awa.kamar haɗin baki sai ga Yaya Mukhtar shima yazo wuce wa,ko kallonsa banyi ba,tunda idan na gaishesa baya amsawa.shahid da saurinsa ya matso ya miƙa masa hannu don suyi musabaha.amman sai yaya mukhtar ya kauce ya yi shigewarsa gida alamar yana mugun jin haushinshi.

Aƙwai abinda shahid ya yi daya ƙara sakawa naji ina matuƙar mugun sonshi,saboda yadda ya nuna ko ajikinsa bai damu ba,ya dawo muka cigaba da hirarmu ta masoya.

******

Hajiya kaka na shafa addu'ah Bilal ya shigo ransa amugun ɓace,Hajiya kaka ta ce"a'ah wai kai lafiyarka kuwa Bilalu?ka ke ta wani cika kana batsewa ko dai kai da wanine?".kamar yana jira sai kuwa ya fara magana cikin mugum fushi ya ce"wai kaka waye ya bawa wannan yarinyar damar tsayawa da wani awaje ne?gashi nan ta ɗakko mama wani kamar ƙwara,wai da sunan zance?to wallahi ni bazan yarda da wannan shashancin ba."

Ya faɗi hakan cikin matsanancin fushi,da sauri kaka ta kallesa kallon baka isa ba sannan ta ce"kai kaga Bilalu binan hanyar ɓangarenku,baza kazo ka ce zaka yimin ihu a kunne ba,ko ubanka Audu bai isa yazo yana yimin ihu akai ba,balle kai karan kaɗa miya.to wai ce maka aka yi khairat baza ta yi aure ba ko me?ko kuwa so ka ke ta koma maka?ku cigaba da xaman dadiro?".da sauri Bilal ya kalleta ya ce"Hajiya kaka zaman dadiro kuma?saboda me zaki ce zaman dadiro zamuyi alhali ita matata ce".

Ya faɗi hakan cikin zare idanu,jamar hauka sabon kamu,sai kuwa haiya kaka ta ce"inye ikon Allah sai kallo,Allah inajin Bilalu ka zare wallahi,ina karatun addininka ya tafi?ko kuwa lokacin da ka yi sakin mahaukaci ne kai?to bari kaji tun kafin in zagi uwarka Ruƙayya ka fitarmin daga sashe na kafin in yi maka ihu."sosai abin ya bawa Bilal mamaki ya ce"ok haka ki ka ce ko?ni ne mahaukacin ko?shikkenan babu komai indai khairat ce taje kome za tayi ta yi na daina ko kallonta".

Ya faɗi hakan yana fita daga ɓangaren Hajiya kaka,Da sauri ta ce"yauwa tafi nono fari ai jeka ka yiwa uwarka Rakiya wannan haukar don ni nafi ƙarfin haukar ka,haukar banza haukar wofi kawai,ka saki matarka saki har uku irin na jahilai sannan yanzu ni kazo ka ce zaka ƙare akaina?a'ah ba zai yiwu ba,banci nanin ba nanin baza ta cini ba."ta faɗi hakan tana kunna ƴar radionta.

Da ƙer muka rabu da Shahid,don na lura Shahid ɗan soyayya ne na ajin ƙarshe.ya bani wata kyakkyawar waya me mugun kyau da tsada na amsa na yi masa godiya.

Ina shigowa gida na yiwa mama bayanin komai sosai ta yi murna da jin hakan,Baba yana dawowa ya saka aka kirani kaina a ƙasa ya ce"khairat na yi bincike akan yaron nan balaraben nan,kuma na gano yaron arziƙi ne har mahaifinsa wanda Allah ya yiwa rasuwa,kuma gobe zasu zo a saka ranar aure da komai".murmushi kawai na yi kaina yana a ƙasa na tashi na tafi da sauri saboda kunyar baba dana ke ji.

Haryanzu su twins basu dawo ɓangarenmu ba,nima ban damu ba don da kansu yaran ke zuwa waje na su cika nima da surutu don haka na ke kaɗa kansu su tafi baki ɗaya ma,wannan abin ba ƙaramin tsayawa Bilal arai ya yi ba,ya shirya kayansa ya koma wajen aiki ransa duk babu daɗi don gani ya ke kome ya yiwa khairat bai cancanci ta tsanesa har haka ba.

Ƴan huɗu kuka sosai suke da tafiyar mahaifinsu,suka saka Kakarsu agaba Hajiya Ruƙayya wai su sai sun dawo banu yadda ta iya haka nan ta dawomin dasu,ai kuwa wataran har paracetamol na ke sha saboda fitinarsu,wataran idan na fita zance bina suke Shahid kuwa ya biye musu suyi ta yi masa shirme,har sai na gaji na korasu gida sannan suke haƙura.ai kuwa shahid yana yi musu hidima sosai,kuɗi kuwa kullum cikin turomin su ya ke,inyi ta fushi saboda kuɗin sunyi yawa,idan na yi magana shima haushin ya ke ji sosai don haka sai na daina yin maganar.

Rashida fa ta dage wai tana fushi dani akan abubuwan da na ke yiwa yayanta,ni har mamaki suke bani daga ita har yayan nata da duk wani meson na koma gidanshi,don gani na ke kamar ilimin addini bai ishesu ba,don duk wanda ya yi ilimi bazai ce na koma gidan Bilal ba.

*********

sosai mutanen gidanmu suka tisa gulmata agaba,wai zan auri É—an yankan kai,don irin kuÉ—in da aka kawo na aure na ya girgixa kunnuwansu sosai,ya bada sadaki miliyan biyar,ai kuwa duk hankalinsu ya tashi don gani suke kamar shahid bai da hankali,don idan da yana da hankalu bazaiyi haka ba.

Hmm maganar gulma kuwa yanzu ta ƙaru alokacin da aka fara.shigowa da lefe na cikin gidanmu,aƙwatina suka ƙi ƙarewa sau shigowa dasu ake,ƴan uwa da sukazo ƙarɓar lefe sai da suka gaji da ƙirgawa,Aƙwati dozin huɗu haka aka kawo min,Hajiya kaka sai buɗa take tana yada magana a fakaice tana ce wa"ho ho ina gwanin wani ga naka,lallai yau ake harkar arziƙi agidan nan,Ba lefi aƙwati shida ba alokacin ma wai tana budurwa kenan?aka kawo mata wannan lefan kamar ƴar tsana,yanzu kuwa gashi Allah ya fidda ta,ni atarihi ma ban taɓa ganin yarinyar da aka kawowa lefe har haka ba".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.