Complete Hausa Novels

Abin Cikin Wai Complete Hausa Novel

Reading file: ABIN_CIKIN_WAI_COMPLETE_HAUSA_NOVEL.txt

Chapter 26 of 90

Maryam dai ta kasa ce wa komai,a wani ɓangaren na zuciyarta son yaya Aliyu ne tsan-tsa acikinsa,tsoronta ɗaya anty khadija don ita sam a atsarinta ba zata so ta auri namiji mai mata ba.

Nan dai mukaci gaba da hirarmu akan saukarmu da kuma bikinsu Rashida,anan ne Rashida ke yi mana albishir da Babansu ya nemo mana admission a makaranta,ni ɓangaren law sai kuma Rashida, nadiya,Iman, khalisat,Bara'atu sai kuma maryam aminiyarmu duk harkar lafiya ne amman kowa da nasa ɓangaren.

Ni daman tunda na taso ina masifar son karatun lawyer don ina tausayawa talakawa musamman idan suka shigar da ƙara aka yi biris da abin ko kuma a cuce su,ko kuma fyaɗe da akewa ƙananan yara wanda ayanzu ya zama ruwan dare sai dai Allah ya kawo mana mafita.

Soyayyar A.D da jidda sai daɗa haɓaka take,wani mugun son Bilal ne ya ke damun jidda ko bacci zata yi idan ta rufe idanuwanta shi take gani,ta rasa wani irin love take masa.uwa uba ga irin taimakon da ya ke mata ba kaɗan bane,yanzu haka ya bada kuɗi a ruguje gidansu a sake musu wani,daga haɗuwarta dashi zuwa yanzu ya kashe mata kuɗi yafi a ƙirga,ko a mafarki ita jidda bata taɓa tunanin za ta auri miji irin Bilal ba,haƙiƙa tafi kowacce mace sa'a.ga wani irin mugun kishinsa da ke cin zuciyarsa sai take ji kamar duk ranar da ta ganshi da wata mace za ta iya yin komai akanshi.

****

Ina shiga sashen Hajiya kaka na tarar Mero ta tsaya tana wani muzurai,Hajiya kaka na tsaye da É—an madoki hannunta,tana bin mero ita kuwa mero sai gwaliya take wa hajiya kaka tana dariya tana mata gwalo tana rufe ido.

Sosai abin ya bani dariya,sai kuwa hajiya kaka ta ƙara biyo mero ji ka ke timm,kaka ta faɗi a tsugunne ta kasance a ƙasa hajiya kaka ta saki kuka ta ce"shegiyar yarinya aljana wallahi na ɗauki masifa tun ba'aje ko ina ba".

ta faɗi hakan tana fashewa da kuka,sosai na tausayawa hajiya kaka na matso na ɗagata sai kuwa mero ta ce"ai wallahi don baki san yadda na taɓa kada megari bane shiyasa,har rawar banjo na sakasu da na saka musu karara ajikinsu,ni fa wallahi ba'a taɓani in ƙyale".ta faɗi hakan tana yi wa hajiya kaka dariya.

Abin takaici abin baƙin ciki yarinya ƙarama na caskare hajiya kaka amman ta kasa magana,ina ƴar dariya ta na ce"to wai kaka me ma ya haɗaki da wannan basa mudiyar yarinyar?ai sai taji miki ciwo wallahi".

Da sauri kaka ta ce"ai wannan shaiɗaniyar yarinya ce ta ƙarshe,wai fa daga na ce ta ɓatamin tap ɗina shikkenan take wannan rashin mutuncin".muna cikin maganar yaya Salim ya shigo fuskarnan a murtuke yasha ɗanyar shaddarsa skye blue ya yi ƙyau sosai don shi daman da Babanmu ya ke kama sosai kamar an tsaga kara.

Sai kuwa ya ce"a'a Hajiya kaka waye kuma ya taɓa mana ke?".kukan ta cigaba da yi ta faɗa masa duk abinda mero ta yi mata.cikin ɓacin rai ya ce"ke ma kaka ai kinga matsalarki ko wace shara sai ki kama ki ɗakko mana i'ta,ai gashinan yanzu kin ɗebo ruwan dafa kanki".

Sai kuwa yaji mero ta ce"caɓɓi ai wallahi ko yanzu idan ta yi min wallahi sai na rama,tsohuwa masifaffiya kawai. . .tun kafin ta ƙarasa maganar yaya salim ya ƙwarfeta ta faɗi ƙasa ta hau kuka wai ya bugeta a cikinta,ƙara haurinta ya yi sai kuwa ta tashi zumbur za ta arta ana kare ya cafkota sai kuwa ta rungumesa taba ce wa"don Allah kaji ƙaina ka ƙyaleni wallahi ƙafafunka da guduma aka yi su".

wani irin shork yaji tunda ga kansa har ƴan yatsunsa da sauri ya saketa yana nuna ta da yatsansa ya ce"to oya! ɗauki bocket kije ki ɗabo ruwa a tap ɗinmu ki cika mata komai ko kuma inyi miki tsinannan duka wawiya ƴar ƙauye kawai.

Sosai ta zabura ta É—auki bocket É—in ta fita tana mita,inno da ke cikin É—aki tana yi wa Æ´ar ta addu'ar Allah ya shirya mata mero.tunda mero ta taso bata huta da magana ba ita ce ta shiga gonar wane,ta tsokani wane.

Ni na nuna mata yadda ake É—iban ruwan a tap sannan na wuce sashen maman arman.

Tare da maman arman muka fito sashen Hajiya kaka,sai dai fa muna zuwa naga mero tana kallon kaka tana murguÉ—a baki,kaka kuwa tana tsaye idanuwanta sun cika,na ce"a'ah hajiya kaka bata gama É—iban ruwan bane?".

Kaka ta ce"hmm taya ni baƙin ciki khairat yarinyar nan hawan jini take so ta sakani,yanzu fa tunda ki ka fita babh abinda na gani na alamar an zuba ruwa."

sai kuwa mero ta ce"anty khairat don Allah zo muje in nuna miki inda na zuba ruwan"binta na yi kamar raƙumi da akala sai me a masai ta zama take ta zuba ruwan".

sai kuwa mero ta fashe da kuka ta ce"wallahi anty tun ɗazu na ke ta zubawa ya ƙi cika"?sai kuwa ta fashe da kuka.

Dariya ce ta kamani har da riƙe ciki,lallai na yadda da abinda kaka ta faɗa ƙauyanci da gidadanci sun cika ƙwaƙwalwar mero.

*hmmm muje zuwa Fans ba a fara komai ba yanzu salon wasan zai fara Kudai kawai Karku gaji da comment sharhi tare da sharing akwai daddadar tafiya nan gaba*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*miss green ce👉🏿*

[23/09, 16:19] Miss Green🍀: *_🥚ABIN CIKIN ƘWAI..!🥚_*

NA💋
*_Ummu maher(miss green🍀)_*

GAWURTATTU BIYAR✨✨

27🟨28

. . . .duk wanda ya ke wajen sai da mero ta bashi dariya,har ita kanta hajiya kakar wacce aka yi wa laifin,tsabar Ƙauyanci mutum ya yi ta zuba ruwa acikin shadda kuma ya ce wai ta ƙi cika?.
babu yadda na iya dole ni dai na nunawa mero komai,Ta kalleni tana dariya ta ce"la anty ashe mahaya ce ban sani ba?sai kuwa ta fashe da kuka".rarrashin mero na dinga yi hajiya kaka ta ce"ai da kin rabu da ita sai inga duka na za ta yi kome da ta wani Ƙwalalomin manyan idaniyanta wanda inno ta shafa mata,amman ni dai Ɗan uwana sale ba haka ya ke ba".
tana faƊar hakan ta koma Ɗakinta tana mita,naja hannun mero muka wuce sashenmu,a farlo na tarar dasu nadiya suka wani kalleni sheƘeƘe sannan iman ta ce"he!this girl ina zakije mana da wannan mahaukaciyar yarinyar"?.ta faƊi hakan tana mana wani kallon banza.
na buÆŠe baki zanyi magana sai kuwa mero ta yi caraf ta ce"ah tsaya waye Mahaukacin?".
Da sauri nadiya ta matso kusa da mero ta ce"ke!ke!!kece mahaukaciyar ko dukanmi zaki yi?ƴar Ƙauyen banza kawai".
"A'ah gyara zancenki ai Ɗan Ƙauye shine jahili me zagin mutane amman fa ni ba ni bace,idan kina neman mahaukaciya ki hau saman bene zaki same ta".
Sai kuwa nadiya ta kalli saman benen,kuma mahaifiyarta na saman kamar mero tasan tana sama ÆŠin.
Wani banzan mari nadiya ta bawa mero amman sai dai me?tun kafin ta sauke hannunta itama meron ta rama jika ke tas tas maruka har biyu.
Da sauri na riƘe hannun mero ina janta gefe sai kuwa mero ta ce"anty wallahi ki daina ja na don wallahi yau sai na fasawa wannan farar kamar Ƙwai baki".
da Ƙer naja ta gefe tana Ta faman kumfar baki.
ranar sosai aka yi rigima agidan momi iklima ta dage wai sai ta ramawa nadiya mari hajiya kaka ta ce taje idan ta isa ta dake ta,ai kuwa ta shige Ɗaki ba tare da ta Ƙara magana ba,don tasan halin hajiya kaka kaƊan daga aikinta ta ciwa mutum mutumci,musamman idan ta rufe waƊannan fici-ficin idanuwanta,sai ta wanke mutum tsaf.
Sosai muke shirin yin sauka ni da rashida muke abinmu su nadiya ma nasu suke,don yanzu tsakanin rashida da nadiya abin ya Ɓaci,don ita nadiya kallon kishiya takewa rashida,ita kuwa rashidar ko kallon inuwar Nadiyar bata yi,don ta ce rashida bata isa ta yi kishi da ita ba,don bata kai wannan matsayin ba.
sosai hajiya kaka ke ihu duk hankalinmu ya tashi,sai dai me!?muna zuwa muka tarar da ita ta saka kuÆŠinta agaba wanda suka kekkece kamar an ÆŠakkosu a bakin kura.
mamaki sosai kowa ya ke ga kuÆŠi da yawa amman kaÆŠanne ba'a keta su ba.
Nice na yi Ƙarfin halin zuwa wajenta na ce"hajiya kaka me ya faru da kuƊinki haka?".
Kukan ta cigaba da yi sannan ta ce"khairat ranar da kiga ina Ƙirga kuƊinnan?"
sai kuwa na Ɗaga kai alamar na gane,ta ce"to tsautsayi ina Ɗakkosu A ƙarƙashin gado shine naga duk Ɓeraye sun cinye min".
kowa guntse dariyarsa ya yi,sai kuwa mero ta ce"ah kiji min tsohuwa da wayo?yanzu ai gashinan kinyi biyu babu".?
madoki hajiya kaka ta ÆŠakko tana ce wa wallahi sai in dake ki in daki kuÆŠina wallahi".
Da gudu ta yi gefe ta cigaba da dariyarta.
yaya mukhatar wanda shigowarsa kenan ya ce"to yanzi kinga sai aje asaka kuÆŠin abola ko?".
da sauri ta juyo ta ce"to ai ba haƊejawa ne suka bani kuƊin ba?Da dangin uwarkane suka bani yau da nasan sai sun garƘameni".
Jan bakinsa ya yi kawai ya yi shiru,Ƙarshe dai yaya mk da yaya Aliyu sunyi mata alƘawarin biyanta kuƊinta wanda ta ce dubu sittin ne,don muddin basu biya taba aƘwai matsala.
anan aka Ƙirga dubu shabiyar waɗanda su babu abinda ya shafesu,hajiya kaka sai tsinewa Ɓeraye take tana kuka.
Su nadiya sai dariya suke don daman haushinta suke ji.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.